Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 153

Chapter 153

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

kitchen. Tana cikin wanke kwanikan ya shigo kitchen ɗin, waiwayowa tai ta dubesa. Ya canja kayansa zuwa shadda fara tas da tai masa tsananin ƙyau, ga mayataccen ƙamshinsa mai cika hancin mai shaƙa da bashi nutsuwa. Ya ɗan janye idanunsa daga kanta yana kallon agogon hannunsa. “Bara na gaishe da su Mammah kina buƙatar wani abu ne?”. Duk da tayi mamakin jin zancen Mammah sai batace komaiba taɗan girgiza masa kanta. Takowa yay gabanta yana ɗago fuskarta suka kalli juna. “Baza'amin addu'a ba?.” ya faɗa a wani irin sanyin murya. Tana mamakin a yanda ya iya sarrafa yanayinsa a salo daban-daban, kuma duk cikin kame kansa babu wani rawan kai ko gaggawa tattare da shi. Idan badan ita da take ganin true color ɗinsa a tsakanin jiya zuwa yau ba babu wanda za'a faɗama haka yake ya yarda, dan ko'ita idan yay abu ya basar sai take ganin tamkar ba shine ya aikataba. Ya barta da kunya shiko ko'a jikinsa....... “ALLAH ya tsare ya dawo da kai lafiya Yayanmu”. Haɓarta ya saki da tura duka hannayensa a aljihunsa yana kallonta, “Har yanzu matsayin Yayan kawai gareni?”. Ya faɗa yana tsatstsare ta da idanunsa masu kaifi a gareta. Ɗan ɗago idanu tai ta kallesa, ya wani juya mata nasa manyan idanun yana ƙara tsuke fuska. “Yanzu ni waye a wajenki?” Ya faɗa cikin muryarnan tasa ta rashin sakewa. Mamaki tambayar tasa ta bata, da ɗan rawar murya da kunyarsa ta haifar mata tace, “Yayanmu!”. “Daga nan fa?”. Duk da ta fahimci abinda yake son jin sai ta noƙe dan itama ɗin dai gwanace a miskilancin. “Zaki magantune”. Ya faɗa yana sake kallon agogonsa da juyawa zai fita. Jitai duk babu daɗi, “Kayi haƙuri idan na ɓata maka rai Yayanmu”. “Ba haka matata ke bani haƙuri ba, dan haka sai ki shirya ta yanda nafi buƙata kafin na dawo”. Ya faɗa yana ficewa batare da ya waiwayota ba. Kallo ta bisa da shi zuciyarta na maimaito mata karatun hajiya Falmata daki-daki. Ganin tunanin bazai kaita ko inaba ta cigaba da aikinta cikin dauriya dan wani sabon zazzaɓi ke neman saukar mata, ga wajen itakam har yanzu zafi yake mata kaɗan-kaɗan. Duk da yanda take jin nata haka tai juriyar gyara gidan har sashensa, sauƙintama ba wani datti bane. Turaren wuta ta saka har General falo da ƴar barandar waje. Ta bi kuma da fresheners masu daɗi. Sosai nutsuwa ta ƙara saukar mata jin ko'ina ya ɗauka ƙamshi kamar yanda take buƙata. Daga haka ta taƙarƙara ta koma bedroom ta kwanta kozata samu barci ya ɗauketa kafin sallar la'asar. Tana kwanciya ana fara knocking, dole ta miƙe kamar zatai kuka. Hijjab ta saka sannan ta fito ta buɗe. Ganin su maman halima yasa fara'arta bayyana tana jera musu sannu da zuwa. Suma cike da kulawa suke amsa mata suna shiga da kayayyakin da sukazo dashi. Akwatinanta ne na lefe da tarkacen ƴan kayayyaki. Sai kayan gara da suka bata mamaki. Naziru daya kawosu ne yace ta buɗe ƙofar kitchen ta baya a saka tacan zaifi sauƙi. Dan yasan hanyar tunda da shi aka kawo furnitures ɗinta. Cike da girmamawa ta karɓa masa. Taje ta buɗe ƙofar shi da maigadi suka dinga jigilar shiga dasu su Sakina na tayasu da wanda zasu iya. Hardasu kayan cin-cin. Jitai ƙwalla ya cika mata ido najin daɗi da tausayin su baba. Iyaye dabanne, duk da sunsan babu abin AK ɗin ya rasa a rayuwarsa sunyi hoɓɓasa ɗin ganin sun cika mata darajarta akan abinda al'ada ta tanadar. Dan dai gara al'adace da ƙyautatawar iyaye ga miji bawai wajib bace kamar yanda samarin yanzu suke kallo, harma suke samun damar yarfa mace in ba'ai mataba saboda son zuciya. Sai da aka gama shiga da komai sannan ta kawo musu ruwa da lemo sukai zaman gaisawa. Sakina sai kalle-kalle take da jinjina wannan gida a ranta, duk da da ita aka kawo amarya yau dai tafi kallon komai yanda ya kamata dan shiyyasama ta nace sai tazo. Aiko sai gashi ƙiri-ƙiri tana nuna hassadanta a fili dan sai wani yamutse-yamutsen fuska take ita da uwarta dake ji kamar ta fidda Zinneerah ɗin ta kawo sakina ciki. Ita dai Zinneerah bama bi takansu taiba, dan akwai sauran ƴan ɗan musa da sukazo tare su uku sai maƙwaftansu mmn sadiq ɗin abokan arziƙinta suma su uku, sai ƴaƴan mmn halima da ita, da matar Naziru. Kasancewar su mmn halima tsaffin mata ya sasu fahimtar yanayin Zinneerah ɗin, sai mamaki ya kama irinsu mmn sakina da matar Naziru da ita kanta mmn Haliman dan sudai sunsan Zinneerah ba wannan ne aurenta na farko ba, tunda gata harda little. To amma yanayin nata yayi kama da na wadda namiji ya fara taɓawa. Sauran kam dai har ransu gani suke Zinneerah ta kawo mutuncinta, musamman ma ƴan dan musa da babu wanda yasan ƙaddarar data afku ga Zinneerah ɗin har yanzu. Duk da kuwa Inna Asabe ta saki maganganu da sukaje danya sai duk suka kallesu matsayin hassada kawai da sharrin baƙin kishinta da bai ɓoyuwa harga ƴaƴa. Sai da suka shiga ko ina suna mai yabawa da jera addu'oin fatan alkairi. ★★★ Koda Mahma ta koma gida bata yarda ta nunama su Mammah komaiba, hasalima dama basusan inda tajeba. Da sukace zasuzo gidan AK ɗin kuma cikin dabara ta hanasu akan su bari sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sai a maida Farah baki ɗaya dan ya kamata takoma ɗakin mijinta tunda ta samu sauƙi. Da farko Zakiyya ta tubure akan Farah bazata komaba har sai AK ya saki Zinneerah, zuwa lokacin Farahn ta haihu. Kallonta kawai Mahma tai tana gitgiza kai da sake yarda da zancen AK. Kamar zatai magana akan cikin Farah ɗin sai tai musu shiru kawai. Dan ita Farah ɗince da kanta tace zata koma gidanta saboda tunowa da zafafan gargaɗin AK. Ba aunty Zakiyya da Mammah ba hatta Mahma sai da tai mamakin furicin na Farah, amma sai batace komaiba tai murmushi kawai. Aunty Zakiyya kuwa wani shegen harara ta watsa mata da faɗin “Saiki koma ballagaza kawai mayyar miji”. Kaucewa dukan nata tayi tana kumbura baki, dan ita dai wlhy shawarar Adilah da sukai waya jiya da daddare zatabi, gara ta koma koma mi za'ayi ayisa acan. ★★★ Hajiya iya kuwa data koma duk da tana fushi da Uncle Ahmad har yanzu taƙi saurarensa dan ta dage sai ya ƙara aure ya ajiye matar a Nigeria koda zata barsa ya koma. Kokuma ya bar iyalansa anan. Wannan shine zaɓin data bashi kawai ta tsuke bakinta. Zaunar dasu tai shida Baffah da Mommy ta sanar musu komai daya faru. Baffah dai yasha mamaki wannan al'amari, Uncle Ahmad kuwa da dama gaba ɗaya hasashensa da nazarinsa ya tafi kacokan a wajen ne tunda Baffah ya bashi labarin abinda ya faru da tarihin Zinneerah sai baiji komai ba sai takaici da tausayin Zinneerah ɗin. Cikin zafinsa yace, “Aiko indai ta tabbata sune suka aikata yanda sukai wasa da rayuwar yarinyarnan suma tasu saita shiga garari wlhy, dan bazamu barsuba sai inda ƙarfinmu ya ƙare. Gatan da suka kalleta da tashinsa a farko har suka aikata mata wannan ta'asar zasu tabbatar da tunaninau gurɓatacce ne kuwa”. Ɗari bisa ɗari duk suka bashi goyon baya. Suna cikin tattauna yanda zasu ɓulloma

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182