Chapter 49
Chapter 49
hankali. Waɗan nan dai sune yanzu tare dake anan gida, zaki kuma kasance da kusan dukansu yanzu a gida insha ALLAH”. Fuskarta daɗan murmushi tace, “Nagode Baffah”. Murmushin shima yay mata yana jinjina kansa. Yayinda su Haneef suka haɗa baki wajen, “Welcome to Shira's family ƙanwarmu”. “Na gode Yayuna”. Ta faɗa ita cikin son aro jarumtar son sakewa da su. Dan taji daɗin yanda duk suka nuna jin daɗin kasancewarta a cikinsu. Ƴar gajeruwar nasiha Hajiya iya tai musu akan zuminci kafin su fara cin abincinsu a tsanake. Wajen yayi shiru bakajin ko ƙwaƙwƙwaran tarin wani saboda dokace a garesu ba'acin abinci ana magana musamman idan Hajiya Iya da Baffah na waje. Uwa uba kuma Babban Yaya mai gayya mai aiki dashi ko ƙara cokalinka ya cikayi sai kasha uwar harara. Koda duk suka kammala duk ficewa sukai, dan dukansu karatu sukeyi a mabanbanta makarantu jami'oi. Wasunsu na gab da kammalawa, wasu kuma yanzu suka fara musamman ƴammatan. Wasu kuma na tsakkiya. Sai su Bahijja dake secondary sun wuce Zinneerah da aji daya, dan suna ss2. Sai dai yau bazasujeba dan suna wani ɗan hutun kwana biyu a gida. Bayan wucewar kowa ita dasu Meenal ɗin ne suka gyara dining ɗin. Hajiya Iya kuma ta nufi ɗaki gabatar da sallarta ta walha tana bar musu saƙon raka Zinneerah wajen iyayensu ta gaishesu. Suna kuwa kammala gyara wajen suka jata. Meenal ce taja birki lokacin da suke gab da kaiwa tsakkiyar ƙaton harabar gidan nasu. “Kunga ku tsaya a fara da nunama sister kowanne sashe first”. “To uwar tsari”. Cewar Jamal da shaƙiyanci. Hararsa Meenal tayi sai dai batace komaiba. Bahijja tace, “Da gaskiyar sister ai, a fara da waje”. “Naji karku cinyeni da baki malamai. Sister Zinneerah nan inda muka fito shine sashen Granny nasan kin sani ai?”. Jamal ya faɗa idonsa a kanta. Batare da jiran amsarta ba ya cigaba. “Wannan na kusa da shi shine sashen Daddy Ahmad ne. Sai dai basa nan suna ƙasar Turkey lokaci-lokaci suke zuwa. Yaransa biyar shima. Yah Ibrahim, Yah Sadiq, Yah Hafeez. Aunty Zuhrah. Sai Aneesa dan bazance mata Aunty ba, kwana tara kawai ta bani a duniya kamar wannan yarinyar”. Ya nuna Meenal. “Shashasha ai dai na girmekan ko?”. “Oho a banza dai tunda kammu ɗaya”. Ya bata amsa yana mata gwalo. Dariya abin nasu keba Zinneerah. Dan haka yanzuma tai murmushi mai faɗi. “Yauwa sai nan kuma Sashen Gwaggo Bilkisu ne idan tazo nan take sauka itama. Tana Lagos da yaranta huɗu itama, kada lissafin yay miki yawa zakisan sunayensu suma nan gaba. Sai nan shine sashen su Yah Saifudden. Nan kuma sashen baƙine. Wannan da zamu shiga shine sashenmu, iyalan Baffah kenan”. Murmushi Zinneerah tai cike da gamsuwa dajin birgewar tsarin nasu. Batare da tayi maganaba suka nufi sashen Baffah ɗin da yafi na kowa girma a gidan kasancewar yafi kowa yawan iyalai. Sun fara shiga katafaren falo da yaji kayan more rayuwa da ƙawa, wanda har suka fice daga cikinsa Zinneerah bata gama kammala kallon daular dake shimfiɗe a cikinsaba. Basu tsaya anan ba suka isa falo na biyu wanda shima ƙatone na gaske harma zai iya ɗara na farko kayan alatu. A tunaninta an gama kenan, sai taga sun shigo wani falon a hannunsu na dama, sai dai shikam madaidaicine bakai na baya girmaba amma ya fisu tsaruwa. Hamshaƙiyar mace ƙyaƙyƙyawa dake zaune da waya a kunne ta ɗago tana kallonsu. Fuskarta a sake take sai dai ba murmushi takeba. Zama su Bahijja sukai a kujera suna faɗin, “Barka da safiya Momie”. Kasancewar waya take bata amsa musu ba. Tadai ɗaga musu hannu kawai idonta akan Zinneerah data kai zaune ƙasa zuciyarta na harbawa da ganin kamanin matar da Khalipha sosai. Bayan ta kammala ta ajiye wayar tana faɗin, “Masha ALLAH ɗiyata sai yanzu muke ganinki?”. “Kuyi haƙuri Momie”. Zinneerah ta faɗa kamar yanda taji su Meenal na kiranta. Cikin ƴar dariya tace, “A'a aiba laifi kikaiba ƴata. muna miki maraba da shigowa cikinmu”. Gaba ɗaya kan Zinneerah a kulle yake. Tadai daure ta amsa mata da godiya tana gaisheta cikin girmamawa. Hakan yasaka Hajiya Nafisa jin daɗi har ranta dajin ƙaunar Zinneerah. Sun ɗanja lokaci a sashen Hajiya Nafisa da suke kira Momie nata mata ƴan tambayiyi jefi-jefi da janta da hira. Hajiya Nafisa itace Baffah ya aura bayan rabuwarsa da Hindatu. Itace mahaifiyar Khadija da a yanzu haka tayi aure itada ƴar uwarta Hafsat. Sai Khalifa, Saifudden, da auta Bahijja. Sunɗan jima Kafin su miƙe su fito dan itama wajen aiki zata fita. Daga nan sai sashen Hajiya Halima mahaifiyar su Meenal. Wadda suke kira Ummi. Itace ta haifi Mas'ood, Moos'ab, Ni'ima, Meenal auta. Itama ɗin dai ta tarbesu da kulawa da sakewa. Dan tamafi Momie fara'a gata da barkwanci. Yanda Zinneerah ta lura su Jamal sunfi sakewa sosai anan. Nanma sun jima sosai kafin su fito zuwa sashen Hajiya Ai'sha amaryar Baffan da suke kira da suna Ammi. Itace mahaifiyar su Haneef Safiyya, Abidah Jamal auta. Mahaifiyar su Jamal ba mace bace mai yawan fara'a. Amma tanada son mutane itama. Dan ta tarbi Zinneerah ɗin da kulawa sosai, harma takai hirarsu tafiyin tsaho anan fiye da kowanne sashe. Basu fitoba sai da akai kiran sallar zuhur suka koma sashen Hajiya Iya data gaji da zuba idon dawowar tasu ma. ★★★ Lallai da gaske Shira's Family yayma Zinneerah daɗi. A cikin kwanaki huɗu kacal sai gashi ta saki jikinta da kowa, musamman ma su Bahijja dake ɗorata a hanya waɗanda bata da aminai sama dasu a gidan. Zata iya cewa shine gidan zama na farko data shigo bata fuskanci ƙiyayyar waniba a zahiri. Dan inma akwai masu ƙin nata sun danne a zukatansu basu taɓa nuna mataba. Daɗin zama cikinsu ya matar da ita batun kwana biyu da akace zatayi ta koma. Abinda kawai ta kasa sakewa da shi shine kwana ɗakin da aka bata matsayin nata. Komai take a cikinsa a ɗararene. Gashi su Meenal basa shiga ɗakin sam. Ko zuwa sukai tana ciki sunfi yarda su jirata a falo harta fito.. A randa ta cika kwana na biyar suka koma makaranta. Ranar duk sai taji kuma babu daɗi. Amma janta a jiki da Hajiya iya keyi yay matuƙar ɗebe mata kewar su Little da ke damunta a rai tun zuwanta gidan. Tamkar kuma Hajiya iya ta shiga ranta sai gashima ta kira mata Mama a waya suka gaisa. sai dai su Sadiq duk sun wuce makaranta. Gwarancin Little dake wasa kawai take jiyowa. Tanason tambayar lafiyarsa tanajin kunyar maman Sadiq. Dan haka tai shiru tunda dai ALLAH yasa ta jisa ɗin. Zinneerah na zuba ido taji ance ta shirya ta koma gida kodan karatunta sai taji tsit. A ranada ta cika kwanaki tara a gidanma Baffah yasa ta shirya Yah Saifudden ya kaita makarantar su Meenal da sunan sabuwar ɗaliba. Hakan ya bata mamaki dan babu wanda yay mata bayanin za'a canja mata makarantane. Garama Hajiya iya ta mata nasiha akan ta dage sosai karta bari su maidata baya. Tafi son karatunta da nasu Bahijja ya tafi dai-dai. Zinneerah ba ƙoƙarine da itaba. Sai dai tanada naci akan abinda takeso. wannan ne ya taimaka mata matuƙa wajen amsa interview da akai mata duk da dai karatun da tayi a gidan Abba ya matuƙar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182