Chapter 6
Chapter 6
ɗakin. Kuka kam Zinneerah ta shashi matuƙa. Ga ciwon da cikinta kanyi lokaci zuwa lokaci. Dawowar Sa'a gidan da kayan ɗanwake ta samu tsagaitawar kukan saboda lallashinta da Sa'a ta zauna yi. Ganin yanda Sa'a ta nuna matuƙar damuwarta yasata shanye sauran kukan nata dan ba yaune farauba a gareta ga halin Inna matar ubanta. WASHE GARI. Da safe kamar yanda ta saba kafin tayi tafiya tanayin sallar asubahi ta fito tsakar gida ta hau shara. Duk da sanyin dake busawa na sanyin safiya haka taima tsakar gidan ƙwal da shara, ta gyara turken dabbobin Inna ta zuba musu sabon abincinsu. Sannan tazo ta fara haɗa wuta. Cikin dauriya take komai, dan wani irin zazzaɓine ke ratsa dukkan ɓargon jikinta a hankali. Haka ta cigaba da daurewa harta kammala dukkan ayyukanta wajibabbu a gidan. Babu wanda ya fito a mutanen gidan sai can gyallowar rana. Sa'a ce ta fara fitowa tana mata sannu, sai ga Tinene ta fito itama tana mika da hamma dan sai yanzu zatai sallar asuba. Can sai ga baba ya shigo gidan, da alama tunda ya fita salla masallaci bai shigoba sai yanzun. Dukawa sukai har ƙasa ita da Sa'a suna gaishesa. Ya amsa idanunsa aka Zinneerah da ya kwana da damuwarta a cikin ransa. Murya ƙasa-ƙada dan kar Inna taji yace, “Zinneerah yaya jikin naki?”. “Da sauƙi Baba”. Ta amsa kanta a ƙasa. Kafin ya ƙara cewa wani abu Inna ta fito wuff. Da sauri yabar wajen saboda wani shegen kallo mai kama da harara data watso masa. Taja tsaki tana duban Zinneerah dake durƙushe har yanzu. “Ki tashi ki ɗebo mani ruwan rahi dan randunan gidanga duk babu ruwa. Kuma na rahin yamma nakeso dan ruwansa yahi garɗi da haske”. “To inna. Ina kwana?”. A takaice ta amsa mata tana karasowa wajen murhun inda wutar da Zinneerah ta haɗa ta kama sosai. Fuskar Sa'a babu walwala tace, “Inna dakin barta sai anjima rana ta ƙara dagawa sama, kinga akwai sanyi garin sosai”. “To uwata, yanda kikace ai haka zanyi”. Inna ta faɗa a hasale.. Shiru Sa'a tayi, dan tasan gatse Inna tai mata. Zinneerah dama bata tsayaba, tuni ta ɗauki botikin fenti da hijjab ta nufi ƙofar fita cike da dauriya. Hakan ba sabon abu bane a gareta, shiyyasa fita ɗibar ruwan a yanzu bai dametaba. Kawai yanda takejin jikinta babu daɗine matsalarta. Amma haka ta nausa kanta hanyar jeji domin ɗebo ruwa. Harta isa babban rafinsu da su kansu basusan iyakar inda ya tsayaba bata haɗu dako kare ba. Ta ajiye botikin a gaban rijiyar da aka gina a tsakkiyar yashi wadda bawani zurfine da itaba. Hasalima a gabanta ake duƙawa asa kwano a kwarfo ruwan dake kwance. Bismillah ta ambata tana saka kwanon cikin ruwan, sai da ta kwashe na ciki tas ta watsar waje sannan ta jira ya sake taruwa ta diba a botikin nata. Bayan ta cikashi taf ta miƙe da ƙyar ta ɗora bisa kanta. Koda tai sallama Sa'a ce kawai dake wankin baki da gawayi ta amsa mata. Inna ko dake bakin murhu tana yanka tuwon dare daya rage tana jefawa a ruwan data saka a wuta ko kallonta bataiba. Hakama Tinene dake gefen Innar tana shan koko. Sai da ta wanke duk randunan gidan guda huɗu sannan ta juye ruwan ta Sake komawa. Haka ta dinga kai kawo tsakanin gida da rafi ɗibar ruwa. Tun bata haɗuwa da kowa har mutane suka fara fitowa. harma da irinta masu zuwa sakkon ɗibar ruwan na rafi. Duk wanda ta haɗu dashi gaisuwar mutunci ce tsakaninsu. Har ALLAH yasa ta kammala gaba ɗaya. Zuwa yanzu Inna ce kawai a gidan, Baba ya fice wajen sana'arsa. Sa'a da Tinene kuwa sun ɗauki tallar gyaɗa da Riɗi da itama tasan tata tallan na jiranta ne. Sai da ta gama ɗauraye ƙafafunta da sukai futu-futu da ƙura tazo inda Inna ke tankaɗen garin ɗan-wakenta. “Inna na gama ɗibar ruwan”. Yanda tai maganar murya na rawa yasa Innar kallonta. Duk da yanayinta ya nuna bata jin daɗi hakan baisa Inna tambayarta ba. Sai ma sake tsuke fuska tayi da faɗin, “Zauna inason magana dake”. Babu musu Zinneerah ta zauna duk da ranta fal tsoro. Ƙare haɗe fuska Inna tai tana dubanta da ƙyau. A tsawace tace, “Miya maidoki garinga?”. Sosai gaban Zinneerah ya ƙara tsananta faɗuwa. Murya na rawa tace, “Inna sune suka koroni. Sunce basa buƙatar baƙauya irina. Kuma saida suka shinhiɗa mani uban bugu da aibantani kahin su bani jikka biyu da rabi su sani a mota....” “Munahika, halan wata tsiyar kika ƙulla masu acan? Saboda kina buƙulu da abunda zan samu na hassahi daga kuɗin aikin naki?”. “Wlhy Inna ba haka bane. Matar gidance bata sona dai na rantse”. “Ruhwa mani baki dan bantan ubanki. Ai hajji Lanti zatazo ne, zanji gaskiyar zance a gareta. Wa billahillazi naji saɓanin abinda kika hiɗi yanzu ina halakaki na halaka banza wohi babu mai sanin yanda akai. Ƴar banza, kinhi son mu zanna ga ƙugunki ga nawa a gida. Sabidda kina kishi dani tunda uwarki bata gida? To mu zanna ga hili ga mai doki ai. Dan uban mutum yayi idan yana iyawa dani ko. Tashi ɓacemin a ido kahin naita tsinarki har se zaman Danya ya gagari ubanki ma bake kaɗai ba”. Mikewa Zinneerah tai tana shartar hawaye. Duk da cin zarafi ga inna ba yaune farauba a gareta. Sai na yau ɗin yay mata zafi ainun. Karon farko taji tana kwaɗayin son sanin inda mahaifiyarta ke rayuwa a yanzu. Ɗakin kwanansu ta shige, ta faɗa akan yamusashshiyar katifar da Yaya Sa'a da Tinene ke kwana. Dan ita bisa tabarmar karauni take kwana kamar yanda Inna take buƙata. Dauɗaɗɗun kayan dake gefe ta jawo ta shiga rufawa a jikinta saboda sanyi da takeji. Sosau ta ringa rawar sanyi tana sambatun zazzaɓi. Har tsahon lokaci babu wanda ya shigo ɗakin. ba kuma ta ƙarajin motsin Inna ba. A haka barci yay gaba da ita mai nauyi. “Zinni!! Zinni!!. Wai dan buhun ubanki baki jina inata kware baki?”. A firgice ta tashi zaune jin irin kiran da Inna ke ƙwalla mata tamkar ana yaƙi. Ta amsa a kasalance tana ƙoƙari janye kayan data nausama kanta gefe dan ta samu damar mikewa. Fitowar tata yay dai-dai da shigowar Yaya Gajeje gidan da sallama. Inna ta sake tsuke fuska tana kallonta. sai kuma ta ɗauke kai ta maida ga Zinneerah dake fitowa tana rawar sanyi da yamutse fuska alamar bata da lafiya. “Oh sannu ƴar gata! Ina nan tsaye ke kina can kina jan nashari a ɗaki? To kizo ki haɗa mani wutar ɗan wake kar rana tayi..” Da sauri Yaya Gajeje tai saurin tare numfashin Inna, “Haba Inna, wane haɗa wutar ɗanwake kuma kike magana haka? Diba kiga yanda take rawar ɗari da alama bata da lahiya”. “Mtsoww!!” Inna taja tsaki. Kafin ta cigaba da magana a hasale. “To ina ruwana da ciwon nata. A yanzu ma wagga duniya waye ke da lahiyar. Gajeje ki hita idanuna, karki kaini maƙurar randa zan maki bankaɗa wallahi”. Murmushi Gajeje tai tana kaiwa zaune. Cikin kwantar da murya tace, “To inna idanma kin mani bankaɗa ai kin isane tunda kece kika haiheni. Ni dai kin sanni ban ganin gaskiya na riheta ai. Amma dai kiyi haƙuri ni bara na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182