Chapter 1
Chapter 1
*_Typing📲_* *_MAKAUNIYAR ƘADDARA😭_* *_Bilyn Abdukk ce🤙🏻_* *_Da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai. Ya UBANGIJIN al'arshi ka bani ikon rubuta abin zai amfani al'ummar MANZON ALLAH. Ka tsare harshena da alƙalamina rubuta abinda zai cutar da ni da duk wanda zai karanta littafin nan. Ka bani ikon rubuta abinda zai amfaneni duniya da lahira ni da masu karatun._* *_Ina mai farin cikin sake dawowa a wannan karon tare da ƴan uwana, yanda muka fara lafiya ALLAH ya sa mu gama lafiya, UBANGIJI ya bamu kariya yay riƙo da hannayenmu baki ɗaya._* *_Ya rabbi ka gafartama Mahaifina da sauran al'umma da suka rigamu gidan gaskiya. Idan tamu tazo ALLAH yasa mucika da imani. ALLAH ka wajabta mana tsoranka da soyayyar MANZON ALLAH😭🙏🏻._* _Zafafa Next level_ *Page 1* ..............“Inada tabbacin wannan itace tashar da zaki iya samun motar duk wani gari da kike buƙatar zuwa”. Mai napep ya faɗa dai-dai yana samun wajen fakin, da ɗan karkato kansa yana duban yarinyar dake a baya zaune. Batace da shi komaiba. Sai ƙoƙarin kwance haɓar zaninta da takeyi jikinta na rawa. Ta miƙa masa ɗari biyar ɗin dake a ƙudundune saboda uban ƙullin da tasha a cikin zani. Baki ya buɗe kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan fisgi ƙudundunanniyar ɗari biyar ɗin daga hannunta yana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa. A yanzu ɗinma batace da shi komaiba, sai hawayen dake famar zarya daga idanunta zuwa kumatu. Tsohuwar ɗari biyu guda biyu da naira talatin a sama ya miƙa mata fuska a tsuke. “Nagode”. Ta faɗa a karo na farko tana amsar kuɗin. Batare da ta jira amsarsaba ta fito daga Napep ɗin tana kalle-kalle da ƙoƙarin sake maida kuɗin daya bata a haɓar zani ta ƙulle kamar ɗari biyar ɗin ɗazun. A kallo ɗaya zaka iya fahimtar ƙarancin shekarunta. Dan kuwa bazata wuce shekaru sha huɗu ba. A tsarin halitta batai kama da mai taɓin hankaliba, amma a yanayi zaka iya kiranta da mai ƙarancin hankalin. Duk da kuwa babu wani datti ko makamancin hakan a kaf illahirin jikinta. Ƙara kai hannu tayi ta share hawayenta a karo na babu adadi, cikin rauni da alamun tsoron dake tattare da ita ta furta, “ALLAH gani gareka. Da kai na dogara, a gareka kuma nake buƙatar taimak......” “Ƙanwata ina zakije?”. Karaɗin wani kwandasta ya katseta batare da takai ƙarshen addu'arta ba. Kallonsa tai da jajayen idanunta dake a kumbure saboda kuka tace, “Danya”. “Danya? Ƙanwata sai kinyi ƙarin bayani, dan nikam bamma taɓajin sunan wannan garin ba”. Shiru tai alamar nazari, ‘Gaskiyar kwandasta ɗin nan. Danya dai garinsu motama bata shiga sosai. To amma idan bata mantaba lokacin da zasu taho da Hajji Lanti bayan sun fito daga Danya a mashin, a Gozarki suka kwana, washe gari kuma daga Gozarki sukazo kusada, anan suka sami motar Katsina’. “Wai kodai bakisan ina kika dosa bane ƴammata?”. Kwandasta ɗin nan ya sake katseta. Da sauri tace, “Kusada zanje”. “......Kusa da kano, nesa da birnin katsina” kwandasta ya faɗa cike da barkwanci. ita dai batace da shi uffanba, sai ma faman waige-waige da takeyi, har yanzu akwai tsoron ko wani zai iya biyo bayanta tattare da ita. “Kinga ga motar da zaki hau can ta kaiki Gidan mutum ɗaya. Inada tabbacin daga can zaki samu motar kusada ƴar ƙyaƙyƙyawa”. “Nagode sosai” ta faɗa tana ɗan risinawa. Daga haka tai gaba da sassafa batare data sake bi takansa ba. Tana isowa motar daya nuna mata ko jiran ba'asi bata tsaya yiba saboda jin kwandasta ɗin motar nata faman faɗin, “Charanci, kankia, Gidan mutum ɗaya, Tsanyawa, Bichi, har kano. Can baya ta shige inda wata mata ke zaune ita da yaranta biyu da bazasu wuce sa'annintaba. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya dasa hannu ta gyara ɗan labulen jikin gilashin yanda take fatan ko su Hajiya biyota sukayi bama zasu iya ganinta ba. Duk da hakan kuma roƙon ALLAH take a ranta ALLAH yasa motar ta cika da wuri su tafi. Addu'ar tata kuwa ta amsu. Dan ko cikin ƙanƙanin lokaci motar ta cika. Ita dai tana duƙunƙune cikin hijjab har kanta. Ko wanda ya shigo ya zauna a gefenta bata kallaba sanda ya shigo. Ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jin motar ta ɗaga alamar zasu bar cikin tashar. Sunyi tafiya mai ɗan tsayi data tabbatar sunbar cikin birnin katsina ta tsinkayi maganar kwandasta na ambaton kowa ya bada kuɗin mota. Ciro kanta tai daga hijjab ɗin bayan ta kunto kuɗin data ɗaure a haɓar zaninta na canjin mai napep. Jin matarnan mai ƴaƴa na tambayar “Nawane gidan mutum ɗaya” ya sata tsaida hankalinta tana jiran amsar kwandasta ɗin itama. “Ɗari huɗu ne kuɗinki hajiya”. Ya bata amsa yana amsar kuɗin na kusa da shi. Matar tace, “Haba ɗana adai duba. Wlhy jiya a ɗari uku-uku mukazo. Yaran nanma ɗari bibbiyu na biya musu”. “Ai jiya kikace hajiya. Jiya kuma ba yau bace. Dan haka kuɗinki keda yaranki dubu da ɗari biyu ne”. Zatai magana wani dake can gaba yay saurin amshewa. “A'a fa gaskiya ɗari uku ne, ni kaina ɗazun nan da safe nazo a haka”. A take rigima ta kaure tsakanin kwandasta da matarnan da mutumin da yay maganar da safe yazo a ɗari uku. Da ƙyar dai aka tsaya akan ɗari uku da hamsin. Ita dai yarinyarnan dama bata tanka ba. Ta miƙa masa ɗari huɗun da mai napep ya bata canji. “Ƙanwata ina zakije?”. A taƙaice tace, “Gidan mutum ɗaya”. Canjin hamsin ya miƙo mata. Batare datace komaiba ta amsa ta maida a haɓar zaninta. Sai dai bata koma cikin hijjabinba tabi ayarin masu kallon hanya. Kasancewar motar mai lafiya ce bayan sallar la'asar kaɗan suka iso gidan mutum ɗaya. Danma sun ɗanyi tsaye-tsaye a hanya na sauke mutane. A gidan mutum ɗayarma dai a rikicen take. Dan ba taɓa yin tafiya irin haka ba sai wannan karon. Sanda zasu tafi kuwa hajji Lanti ce tai musu komai. Da ƙyar ta samu ta tambayi wani yaro mai saida biredi inda zata sami motar kusada. Shine ya nuna mata. Tai masa godiya. Ta iske ƙananun motoci kusan huɗu dake jere a kan hanyar da yaron yace mata itace hanyar kusada. Lokacin da suka tafi su tun daga cikin kusada suka shigo motar katsina. “Ƴammata kusada ne?”. Wani tsamurmurin saurayi ya faɗa yana nufota. Saurin ɗaga masa kanta tayi alamar eh. Cike da jin daɗi yace, “Yauwa taho muje, dama mutum ɗaya muke nema”. Har cikin ranta taji daɗin hakan. Ya nuna mata jar motar data gama fita hayyacinta. “Yauwa shiga nan. Bayin ALLAH a matsa mata mu kama hanya ko”. Cike da mita fasinjojin suka shiga muskutawa dan sama mata waje. badan wajen zai wadacetaba ta shiga ta zauna. Sai dai kasancewar ta mai ƙaramin jiki yasa bata takuraba matuƙa. Sai dai waɗanda ta tarar a ciki sunata faman mita sukam an takura musu. Direban ya cika haɗama da son kuɗi. Yanda direba bai tanka musuba itama bata tanka ba. Sai dai acan ƙasan ranta daɗi takeji zata koma gida taga Babanta da su Yaya Tinene, duk da su ba son ganinta sukeba. Tsabar rashin isashshiyar lafiyar motar basu iso ba sai gab da magriba, dan sun kwashe kusan awa ɗaya da rabi a hanya. Ga tsaye-tsaye da suka dingayi ana sauke wasu da ɗauka a ƙananun ƙauyika
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182