Chapter 132
Chapter 132
Mahma ce tace, “Kamar dai biyar ko”. “Biyar fa?”. Dr Mahmud ya ambata mamaki ƙarara a fuskarsa. Ɗan duban Farah ɗin dake riƙe jikin Mammah tana kuka da wani ɗan fisge-fisge yayi ya ɗauke kansa. Batare da yace komaiba yay mata allurar kawai ransa fal wasiwasi. Yana gama mata allurar ko mintuna biyar ba'a ƙullaba barci ya ƙara ɗaukarsa. Kallon AK Mahma tayi da cewa, “Taimaka ka kai mana ita mota Abdul-Mutallab, ku kuma kumuje shima ya samu ya huta”. Babu shiri Mammah tace, “Addah ai shine zai kaimu, taya matarsa na wannan halin yaga wani ta hutu?”. Murmushi Mahma tayi na takaici, muryarta aɗan hasale tace, “Duk mu da muke tare da ita bai wadatarba sai shi ya kasance a wajen?. Ai ya kamata a tausaya masa ya huta ga kuma yarinya an kawo zai barta ita kaɗai kenan komi?”. A take Mammah ta sake tamke fuska matuƙa. Ta kalli AK da yay tamkar bayama jinsu yanata latsa waya. Sai kuma ta maida kan Mahma, “Addah to in hakane muyi kwanciyarmu anan ɗin kawai basai yayi wahalar da kike gudar masanba..” “Bazai yuwuba, tunda dai ga gida can da zamu zauna mu kaɗai bamu takura kowa ba, ba'a takuramu ba, can zamuje. Abdul-Mutallab ɗauketa”. Yanda Mahma tayi maganar babu wasa a ciki ya sakashi zura wayarsa aljihu ya tako a hankali inda Mammah ke rungume da Farah. Ɗaukarta yay cak ya fita da ita duk da nauyin datai masa saboda yanda jikinta ya saki sosai. Duk yanda Mammah keta kumbure-kumbure Mahma batabi takantaba ta tasasu gaba suka fice suma. Dan ita aunty Zakiyya ma ta ƙagu subar nanɗin dama suje inda takeson amayar da abinda ke a bakinta. Aunty Zakiyya ce ta jasu. Suna ficewa daga gidan AK yaɗan lumshe idanunsa da murza goshinsa yana furzar da huci. Sai kuma yay murmushi da girgiza kansa saboda harar da Mammah keta faman antaya masa da gargaɗi da idanu. Juyawa yay zuwa cikin gidan dan shima wani ma zazzaɓi-zazzaɓi ke neman rufesa, sashen Farah ya koma ya kashe komai da maida ƙofar ya rufe, koda ya fito sashensa ya nufa dan yafi buƙatar watsa ruwa a yanzu. ★★★ A ɓangaren Zinneerah kam kuka taci sosai, sai da Mahma ta leƙo tai mata sallama akan suma zasu wuce, ta kuma ɗan lallasheta da ƴar nasiha sannan ta sassauta. Fitsarin da takejine ya sakata tashi dole ta shiga toilet ɗin ɗakin tayo, tana fitowa ta sake komawa saman gadon ta kwanta dan zazzaɓi takeji yana neman rufeta ga ciwon kai. Ba tare data damu da cire komai ba ta kwanta a haka dajan bargo ta lulluɓa har kanta saboda sanyi da takeji yana ratsata. Ga kuma ac a ɗakin dake aiki ta kasa kashewa. Batafi mintuna goma da kwanciyarba barci ya kwasheta sama-sama. A ɗan firgice ta farka saboda ƙarar buɗe ƙofa da taji, ta ƙanƙame jikinta waje guda jin tabbas mutum ne ya shigo. Sai dai ta kasa ko motsi saboda yanda zuciyarta ke wani harbawa da sauri sauri na tsananin tsoron wanda zataci karo da shi a matsayin mijin nata. AK da tun shigowarsa ɗakin idanunsa suka fara sauka akanta ya cigaba da takowa cikin ɗakin a hankali sassanyan ƙamshin turaren wutar da ɗakin yaji, da ƙamshin sabbin furnitures dana fenti na rige-rigen shiga masa hanci, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana ƙarasawa gaban gadon sosai. Hannayensa ya tura duka biyu cikin aljihun wandon blue pyjamas ɗinsa har lokacin idanunsa akan Zinneerah dake ƙudun-dune cikin bargo zuciyarta na nemam faso ƙirjinta ta fito. “Assalamu alaiki”. Sassanyar muryarsa ta daki cikin kunnuwanta. Sosai ƙirjin Zinneerah ya buga fiye da farko, dan idan har babu kuskure ai muryar Yayansu taji kam. ‘Kai ina ganganne’ ta ayyana a zuciyarta dake raunana. “Nasan ba barci kike ba”. Ta ƙara tsinkayar muryar tasa a karo na biyu, a yanzu kam kasa jurewa tayi dole tai ƙasa da bargon a hankali daga saman fuskarta. A hankali ta buɗe idanunta zuciyarta na gudu dai-dai da jinin jikinta dake tsinkewa daga cikin jijiyoyinta. A wani irin firgice ta yaye bargon babu shiri tana miƙewa zaune jikinta na rawa. “Y...y....Yayanmu!”. Ta faɗa da wani irin kiɗimammiyar murya dake nuna tsantsar tashin hankalinta a fili. Sosai yanda tayi ɗin ta bashi dariya, amma sai ya daure ko ɗigon fara'a babu a fuskarsa, sai dai idanunsa kafe suke a kanta ko ƙyaftawa bayayi yana ƙarema ƙwalliyar tata kallo, dan zaburar da tayi ta saka lafayar warwarewa daga saman kanta zuwa jikinta. Sai baƙar rigar jikinta mai dogon hannu data lafe da bayyana ainahin surarta da gyaran da fatarta ta samu wajen hajiya Falmata. Janye idanunsa dake binta da kallon yayi yana maidawa akan fuskarta, ganin yanda take ɗan ja baya da rawar jiki laɓɓanta na rawa alamar sonyin magana ya sakashi lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta yana zare hannayensa daga aljihun wandon barcin nasa. Cikin nuna rashin damuwa da yanayin nata ya kai zaune a bakin gadon yana facing ɗinta. Hannunsa ɗaya yakai akan goshinsa yaɗan shiga murzawa. Sai kuma ya ɗago ya dubeta da birkitattun idanunsa dake rikitata, batare da yace uffanba ya miƙa mata hannunsa ɗaya alamar tazo. Kanta ta shiga jujjuyawa tana ƙara nanema fuskar gadon, hawaye na gudu a saman fuskarta kamar an buɗe fanfo. “Yayanmu dan ALLAH kace bakai bane ba”. Ta faɗa cikin tsananin rauni da rawar harshe. A karan farko ya ɗanyi luuu da idanunsa da sakin guntun murmushin da ita ko alamarsama bata ganiba, ya ɗan ƙara ware idanunsa a kanta da kai hannunsa ya shafi sajensa dake a kwance luf duk da ba gyaransa yay ba, dan koda yay wankan ma turare kawai yasa da kayan barci ya fito domin dubata. Cikin muryarsa ta rashin sakewa yace, “Bani bane mi?”. Cijin suɓucewar baki Zinneerah tace, “Miji!, mijin da aka kawoni gidansa matsayin matars.......” Ta kasa ƙarasawa saboda yanda yay bala'in kafeta da idanunsa masu cikar gashi da kwarjini. “Ban cancanta bane?”. Ya faɗa yana cigaba da tsatstsareta da idanu. Babu shiri tai ƙasa da kanta kuka na sake kufce mata. Kansa ya ɗauke daga kanta jin wayarsa na vibration, hannu yasa ya cirota daga aljihun wandon barcinsa yana jan guntun tsaki alamar baiso shigiwar kiranba dai. Sai dai ganin Number aunty Zakiyya ya sakashi yi kamar bazai ɗagaba sai kuma ya ɗaga ɗin batare da yayi magana ba. Cikin sake fusata daga can Mammah tace, “Abdul-Mutallab nasan kana jina”. Runtse idanunsa yay da cije lip ɗinsa na ƙasa. yay ƙoƙarin daidaita kansa wajen faɗin, “Am sorry, bansan ke bace ba”. “Ai yanzu ka sani, na kiraka ne na gargaɗeka, wlhy ka taɓa musu yarinya sai ranka yay mummunan ɓaci, dan nayi alƙawarin wannan auren sai na tsinkashi wlhy, saboda haka karma ka ƙwaɗaitama kanka abinda zai dameka daga baya na faɗa maka”. A bazata ya saki murmushi mai sanyi da kai hannu ya shafi kansa, dan tana gama faɗa ta yanke kiran bata jira amsarsa ba. Ajiye wayar yayi yana miƙewa gaba ɗayansa idonsa akan Zinneerah dake cuɗa yatsunta cikin juna tana cigaba da kukanta harda shashsheka. Batare da tunanin kanta ya nufoba sai ganinsa tai ya hawo gadon sosai, filo ƙarami ya jawo daga gefenta ya kishin giɗa, dan ɗaura gwiwar hannunsa ɗaya yay ya tallafe kansa da tafin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182