Chapter 161
Chapter 161
mafita a wajen Doctor ɗin da zaiyi aikin, idan an dasama wadda zata raini ciki ita zata fara pretending like pregnant, bayan yakai kamar 3months zata koma zama a Morocco ta hanyar wasu dabaru namu na mata har mai ciki ta haihu a bata ɗanta ta shayar ita da kanta. Cikin tsoro tace amma tayaya hakan zata faru bada yardar su Mammah ba. Niko nace mata Mahma ce kawai za'a ɓoyema gaskiyar zance, amma Mammah da ita za'ai komai. Tacemin ta yaya Mammah zata yarda da hakan?. Nace mata ta hanyar yin amfani da ita akan so da kishin da takema mahaifin Abdul-Mutallab da ganin laifin danginsa da take na rabuwarsu, da kuma ƙin son rabata da ƴaƴanta da shine babbar barazanarta a rayuwa. A lokacin Farah bata bani goyon bayaba, dan tace bata yarda a cutar da kowa ba, musamman ma Mammah da ta ɗauketa daidai da nata ƴaƴan saboda ƙaunar da takema mahaifiyarmu. Sosai na mata masifa ni da Muktar a lokacin, dan shine ya taimaka mana da likutan da zaiyi aikin ma. Da dai mukaga taƙi tanƙwaruwa ta sauki sai itama nabi da ita ta hanyar razanarwa da kshiya har tai laushi ta amince. Tun daga lokacin itama Mammah na fara aiki a kanta, sannan Doctor ya tsarama Farah yanda zamu sami sparm ɗin Abdul-Mutallab cikin sauƙi”. Babu wanda mamaki bai nema kashewa a falonba, musamman ma Mammah datai mutuwar zaune akan wannan labari na Zakiyya. Zakiyya ta cigaba da faɗin, “Bayan wani lokaci na tunkari Mammah da batun ya kamata musan halin da Farah da Abdul-Mutallab ke a ciki game da haihuwa, kar muyi sakacin da dangin mahaifinsa zasu aura masa wata zasu rabamu da shine kawai ya koma hannunsu. Na tabbata wannan kalma ta tada hankalinta matuƙa, dan babu abinda tafi tsana arayuwa kamar ace yaranta zasu koma hannun mahaifinsu. Bayan munyi wannan maganar washe gari taima Abdul-Mutallab maganar a gabana, amma sai ya nuna ɗan ɓacin ransa akan duka shekararsu nawa da auren da har za'a fara nuna damuwa basu haihuba, shi wannn maganar dan ALLAH a barta ALLAH ne mai badawa kuma zai basu lokacin da yaso. Da wannan furucin yabar gidan a zuciye. Hankalina ya tashi, dan gashi saura kwana biyu na baro london ɗin, dan haka na sake sabon zaman fanfa Mammah da kawo mata dalilai kala-kala da suka dinga ruɗa mata tunani itama tana ruɗashi. Tashin hankalin data nema sakashi a ciki ya sashi tattaro Farah suka gudo Nigeria a lokacin bamu sani ba. Sai da sukaje ta kira take sanar mini. Naji daɗin hakan, dan nima a gareni wata dama ce. Dan haka na sake buɗe wutar data harzuƙa Mammah harta kirasa ta tabbatar masa da inhar bai yarda da batuntaba wlhy zata iya tsine masa. Sosai Abdul-Mutallab na gudun ɓacin ran mahaifiyarsa. Dan haka furucinta ya tada masa hankali yace ya amince zasuje idan sun koma london. Still nice dai na sake bama Mammah shawarar suga Doctor Hannafi dake nan Nigeria shima kwararrene a wanna fanin kuma a can london ɗinma yay karatunsa da aiki harna tsahon shekara bakwai. Batare da wani jayayyaba ta kirasa da tura masa address da phone Number ɗin Doctor Hannafi dana bata nima kuma na tattaro na dawo Nigeria neman yarinyar da za'aima dashen. Ta farko bataiminba, dan tanada wayo kuma idonta a buɗe yake, hakan yasa nasa hajiya haule canjamin ita.” “Biyayyar da Abdul-Mutallab yake ma Mammah ya sashi ɗaukar ƙafa sukaje ga Doctor Hannafi, wanda dama mun gama tsara komai. Dan haka kawai abinda ya buƙata a garesu shine sparm ɗin sa, ita kuma Farah yay mata wasu gwaje-gwaje kamar gaske. Domin kawai bin umarni Abdul-Mutallab ya yarda ya bama Dr Hannafi Sparm ɗin nan, wanda da shine aka haɗa da ƙwan Farah akaima ita Zinneerah dashen bayan mun tabbatar zata iya. Dan ita bata kai waccan girma da wayo ba, amma yanayinta kawai zaka kalla bama zaka ɗauka a ƙauye ta fitoba dan ƙyakyawa ce. Da wannan karancin shekarun nata mukai amfani wajen yin komai na dashen batare da ita ta fahimci komaiba, dan ALLAH ya taimakemu sanda aka kawo min ita tana cikin halin zazzaɓi sai komai ya ƙara zuwa mana dai-dai muka tafiyar da ita akan treating ɗin zazzaɓin nata. Sai dai kuma bayan dashen muna fata da addu'ar ALLAH yasa ya zauna da kwana uku muka nemeta muka rasa. Hankalina ya tashi matuƙa a wannan lokacin, nama kasa sanarma Farah yanda akai sam. Sai dai munta tararrabin mu da neman yarinya ni da Muktar da Dr Hannafi. Gashi Hajiya Haule ta wuce saudia kuma bani da contact ɗinta nacan balle mu binciki garin da ta ɗakkota. Dr Hannafi ne ya kwantar min da hankali ta hanyar sanar min da wahalama cikin ya zauna, dan bai kai kwanakin da ake buƙatar nutsuwarta a waje guda ba, kawai yanzu dabarar da zamuyi a karasa AK ya bada sparm ɗin nasa kafin su wuce sai a sake yima wata dashen, wannan kuma mu ɗaukama bazai zauna ba kawai, musamman da ko magungunan daya kamata tasha sau daya ta shasu. Na ɗanji sanyi da wannan shawarar tasa, akanta kuma na yanke hukuncin tun karar Mammah da batun dashen cikin. A ranar na kirata, na sanar mata Dr Hannafi ya tabbatar mana AK nada matsalar bama mace ciki, amma za'a iya yin amfani da sparm ɗinsa ai dashe, sai dai matsalar itama Farah nada tata matsalar a mahaifa kuma”. “Hankalinta ya tashi, harta buƙaci na haɗata da Dr Hannafi ɗin, na kuma haɗata dashi ya sake mata bayanin daya kamata akan dashen da tsarin da za'ayi. Ta tabbatar masa da zata iya yarda ayin kodan a samu ɗan danginsa su daina harar mata yaro dason mallakesa. sai dai babbar matsalarta shine Abdul-Mutallab, tasan bazai taɓa yarda da hakanba koda zata tursasashi a wannan gaɓar. Cikin dabara Dr Hannafi ya shigar mata da shawararmu na yanda tsarin zai kasance batare da Abdul-Mutallab da kowama sun fahimci hakanba bayan mu. Tace ya bata dama zatai tunani da shawara. Cikin amincin ALLAH sai tai shawara dani, dan a tunaninta bansan komaiba game da dabaran. Babu wani ja'inja na nuna mata hakan shine dai-dai, tare da sake kawo mata dalilaina nima. Sai ko aka dace ta yarda dan nayi amfani da inda ke mata ƙaiƙayi. Amincewar tatace ta zama ginshiƙin tushen aikinmu na biyu, sai dai a wannan karon cikin bayin gidanmu na ɗakko, kuma da amincewarta dana iyayenta, ana kuma gamawa na maidota gidana ina kula da duk motsinta har ALLAH tasa ciki ya zauna ya kai wata biyu da wasu kwanaki sannan Mammah tazo da kanta ta tafi da ita Morocco. Zuwa sannan kuma Abdul-Mutallab da wasu a cikin danginmu sunsan Farah nada ciki, sai dai mun gargaɗi Abdul-Mutallab da sanarma danginsa zancen ciki har sai Farah ta haihu saji hakan zaisa sufi murna ya kuma musu surprise. Ya amince da hakan kuwa sai dai bamusan dalilinsaba. Sai dai ashe kana nakane ALLAH na nashi, dan randa Farah ta baro london da nufin zuwa tai goyon ciki a Morocco wanda tursasawar Mammah yasa Abdul-Mutallab yarda washe gari yarinyar tayi barinsa. Ranar ba Farah kawai ba hatta ni da Mammah sai da mukai kuka wlhy, Abdul-Mutallab kuwa a ranar ya baro london zuwa Morocco hankali
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182