Chapter 38
Chapter 38
yima Abban sannu da zuwa kamar yanda suka saba idan ya shigo suna gida. Wuff Maman Sakina ta fito daga ɗakinta tunda taji sallamar mijin nasu. Kusan a tare suka shiga falonsa da ita da yaran. Sama-sama ta gaidashi, zata fara kumfar baki ya ɗaga mata hannu dan dama tun a yanayin data shigo yasan gidan babu lafiya. Ga kuma Aliyu na faɗa masa Auntynsu bata da lafiya tana ɗaki kwance. “Salla zanyi, sannan kinsan dokata a gidan nan bana buƙatar yin maganar da duk bata shafi alkairiba a gaban yarana. Dan haka ki koma sai anjima idan na nutsu kizo miyi magana ba yanzu ba”. Wani irin baƙin cikine ya turnuƙe zuciyar Maman Sakina. Ta fito fuuu kamar zata tashi sama. Da kallo kawai ya iya binta yana mai girgiza kansa. A ɗaki kuma Gwaggo Maryama ce da kanta ta miƙe zuwa wajen Zinneerah da Sadiq yace bata da lafiya. Ƙudundune ta sameta cikin bargo tana rawar sanyi. Saurin ƙarasawa tai gareta tana faɗin “Subahanalillahi Zinneerah dama baki da lafiya amma kikayi shiru?”. Kafin Zinneerah ta bata amsa Maman Sadiq ta shigo ɗakin itama. Duban inda take kwancan tayi tana bama Gwaggo Maryama amsar zancenta. “Tunda ta iya cin dambe ba dole tai zazzaɓi ba. Ki tashi kiyi wanka da ruwan zafi kici abinci kisha magani, dan wannan dai zazzaɓin bai wuce sanadin hayaniyar nan ba”. Cike da takaici Gwaggo Maryama tai tsaki. “Shi dai yaya ya auroma kansa masifa wlhy. Ayi mace bata son zaman lafiya kamar dangin yahudawa”. “Humm ai kaɗanma kenan Maryama, dan wannan fitinar ba mutuwa taiba rufa tai, na tabbata jiran dawowar maigidan take, bara kuma kiji zakice nina faɗa miki”. “Fitinanniyar banza. Gashi nan duk tabi ta koyama ƴaƴa hali mara amfani, aini Zinneerah ta birgeni sosai data nuna musu ƙyalesu dama kawai take ba tsoro bane. Shi kuma yayan tunda yasan halinta dama ai kinga sai yay musu iyaka yanzun”. “To ALLAH yasa. Dan da kike ganinta a haka son matarsa yakeyi”. Kiran sallar magriba da aka kirane ya katse hirar tasu. Zinneerah kam dama harta shige bayi tuni. Bayan idar da sallar magriba Gwaggo Maryama ta tsare Zinneerah taci abinci tasha magani sannan ta kwanta. Maman Halima ma ta kawoma Gwaggo Maryama nata abincin yaɗan zauna sukai hira bayan ta shiga ta duba Zinneerah data sanu barci. Kiran sallar isha'i yasata komawa nata sashen. Alhaji da yara kam basu shigo gidanba sai da aka idar da sallar isha'i. Harda Little da yay barci. Gwaggo Maryama ta amshesa ta goya tana maijin tausayin yaron a ranta. Sai da Maman Sadiq ta tabbatar Alhaji yaci abinci ya huta sannan suka fita ta raka ƴar uwarta danta gaidashi. Sai da sukai sallama ya amsa shi da Maman Halima dake tare da shi sannan suka shiga. Sosai fara'ar fuskarsa ta daɗu yanama Gwaggo Maryama lale da zuwa dan dama yara sun sanar masa zuwanta. Suna kaiwa zaune sai ga Maman Sakina tamkar an jehota falon dan ko sallama basa tunanin tayi. Kallonta Alhaji yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya maida hankalinsa ga Gwaggo Maryama. Hakan da yayine ya saka Maman Halima da Maman Sadiq suma yin kamar basusan da shigowar tataba. “An haɗa kai an shigo dan a ƙulla mana sheri ni da ƴaƴana. To ta ALLAH bata mutumba”. Babu wanda ya tanka mata. Sai da Alhaji ya gama gaisuwarsa ta zuminci da Gwaggo Maryama sannan ya dubeta fuska a tsuke. “Saude yaushe ne zakisan inda ke miki ciwo ne wai kekam?”. “Taya kuwa zansan ciwon kaina agola ta haɗani da ƴayana ta doka saboda an gina mata jiki da tuwon gero dana dawa Abban Luba”. Kallonta kawai yake batare daya tankaba. sanin baya son jan rai a magana ya sata fara zayyane masa abinda ya faru, sai dai tanayi tana haɗowa da ƙarya da sheri. Tsam Gwaggo Maryam ta miƙe zata fice ya dakatar da ita. “Maryam kina gidan duk akai wannan?”. “A'a gaskiya Yaya kafin nazone. Nadai iske kawai suna rikicin faɗa nashiga na taya Maman Halima rabawa”. Komai baiceba sai kallonsa daya maida ga Maman Sadiq. “Ina Zinneerah ɗin take?”. “Tana can kwance babu lafiya”. “A dalilin shi wannan rikicin kenan?”. Ya tambaya yana cigaba da dubanta. Kafin ta amsa masa Maman Sakina ta karɓe da faɗin, “Andai shirya munafunci kawai za'ace, yo inba munafun........” “Saude!”. Ya katseta a tsawace. Badan tasoba dole tai shiru. Yaja tsaki da faɗin, “Da safe inason ganinku dukanku har yaran”. Ya faɗa yana miƙewa ya fice. Ganin haka ya saka su Maman Sadiq miƙewa suma duk suka fito. Sai dai a mamakinsu sai hangarsa sukai ya nufi sashenta da alama duba Zinneerah zaijeyi. Hakan yama Gwaggo Maryama daɗi sosai, duk da dama tasan halin ɗan uwan nasu baya wasa sam da lamarin gidansa. Amma batai tunanin Zinneerah ta samu matsayi na musamman haka a garesaba. Bayan ya shiga ya dubata tana barci dan haka ya fito falo. Batare da dubansuba ya nufi hanyar fita yana faɗin, “A tada ita muje ko nan kyamis ɗin Umar ne tunda dare yayi”. Halinsa da Maman Sadiq ta sani yasa bataja zancenba taje ta tado Zinneerah suka tafi kyamis ɗin. Itako Saude nacan tana tijara a sashenta kamar zata haɗiye haƙoranta, musamman ma dataga Alhajin ya fita tare da Zinneerah da Sadiq. WASHE GARI Washe gari da safe Zinneerah ta tashi Alhmdllh babu zazzaɓin dan tasha allura jiya. Bayan idar da salla suka zauna zaman hira ita da Gwaggo Maryama dake janta a jiki cikin hikima. Sai da gari yay ɗan haske suna shirin fita gaida Alhaji sai gashima ya shigo duba Zinneerah ɗin. Kanta a ƙasa ta gaidashi. Ya amsa mata da kulawa kamar yanda ya saba da tambayarta kuma jikinta. “Alhmdllh Abba naji sauki”.. “Haka akeso ai, ALLAH ya ƙara lafiya”. “Amin” suka amsa gaba ɗaya. Sai da ya koma sashensa da kusan mintuna biyar sai ga Hussaina tazo kiransu. Maman Sadiq tasan Maman Sakina ce zata matsa da fitinar sai an zauna. Dan haka ta mike ita da Zinneerah ɗin suka tafi, aka bar Gwaggo Maryama na ƙarasa aikin da Zinneerah ta fara. Kowa ya hallara su kaɗai ake jira, dan haka suka sami wajen zama suma su Luba nata harar Zinneerah. Alhaji daya gama nazarin kowa a ƴan sakanni ya basu damar bayani ɗaya bayan ɗaya. Ya ɗan murmusa yana girgiza kansa. Sai kuma ya haɗe fuska ya balbalesu da bala'i su duka. Kafin ya dawo kan Aliya da Luba da sukaima su Maman Sadiq rashin kunya harda zagi. Ganinfa reshe zai juye da mujiya Maman Sakina ta miƙe da bala'i zata taresa ya daka nata tsawa itama. Cikin jan dogon gargaɗi yace, “Wlhy daga yau ya sakejin makamancin haka akan matansa saiya musu dukan mutuwa a gidan”. Ya kuma sakasu bama su Maman Sadiq haƙuri da ita kanta Zinneerah ɗin. Sannan itama yay mata faɗa akan marin Aliya da tayi tunda yayartace. Yayi hakanne dan kawai kar ace yayi son kai dan yasan dai Zinneerah ta fisu gaskiya. Daga haka ya sallami kowa suka fito Maman Sakina da ƴaƴanta ransu fal baƙin ciki da alwashin hana Zinneerah zaman lafiya a gidan cikin hanya mai sauƙi da Abban bazai gane komaiba. Maman Sadiq kam ko a jikinta dan bataji komai ga abinda Abban
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182