Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 101

Chapter 101

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

rashin fahimtar inda zancen nasa ya nufa yace, “Gayya kuma ranka ya daɗe?”. “Uhm, ko bakaga motocin dake biye damuba?”. Ta mirror Dr Mahmud ya duba bayansu, a nazarce yace, “To inaga dai ba tafiyarmu ɗayaba gaskiya”. Shiru AK yayi duk da bai gamsu da hakanba, sai ma ya jawo wayarsa kawai ya shiga daddanawa. Tafiyar da bata gaza awa ɗaya ba suka iso gidan mutum ɗaya, kai tsaye hanyar kusada suka shiga, a lokacin kuma AK ya sake tabbatar da tafiyarsu ɗaya da motocin nan, amma sai yay shiru bai sake magana ba. Abinka da lafiyayyun motoci ga kuma lafiyayyar hanya cikin ƙanƙanin lokaci suka iso cikin kusada. Basu wani tsayaba suka ɗauki hanyar Danya. Haka kawai AK ya samu kansa da nutsuwa a kallon hanyar zuciyarsa na masa wasu tunani daban akan rayuwar Zinneerah a ƙauyen, rashin ƙyawun hanya ya ɗan jasu lokaci mai tsaho kafin su shigo cikin ainahin ƙauyen Danya. Duk da ba safiya bace garin akwai mutane sosai, dan lokacine na shigowar farkon damuna mazan garin nata dawowa gida domin haramar noma. Sosai idanu suka dawo caa akan dalla-dallan motocin kowa na tunanin daga ina haka?. Wasu suce ƴan siyasa wasu suce daga fadar sarkin katsina ne. to basu dai da tabbas, duk da kuwa kai tsaye Abba gidan maigari ya nufa dasu, dan shine jagoran tafiyar tasu. A ganinsa kuma hakan shine yafi cancanta da wannan tawagar tasu dan bayaso ai musu irin wulaƙancin da akai masa a wancan zuwan. Su maigari suna zaune a bishiyar ƙofar gidansa shi da fadawansa sukaga motoci galla-galla na tsayuwa. Ba karamin kaɗawa hantar cikin maigari da ƴan fadarsa tayiba. Dan duk zatonsa samame aka kawo masa daga fadar sarikin katsina. Duk da yasan baya aikata wani mummunan al'amari ga ƴan garinsa sai da yaji tashin hankali. Bai ƙara rikicewaba sai da su AK suka fara firfitowa. Daka gansu kaga manyan ƙasa masu ci da tsinin allura, dan duk sun jiƙu cikin shaddoji masu maiƙo da ɗaukar idanun mai kallo. Abba ne ya matsa inda suke yaɗanja maigari dake a ruɗe gefe sukai ƴar magana. a take bakin maigari ya washe ya shiga sakin tagwayen ajiyar zuciya. Bai tsaya jan jikiba yasa ƴan fadar tasa shiga cikin gida suka fara fitowa da tabarmi sabbi ƙal tare da manyan dardumai aka shishshimfiɗa a babban zauren maigari dake share ƙal ga sanyi mai saka nutsuwa gaduk wanda zai zauna. Duk ciki suka shiga, akabar Baffah da Abba da Alhaji Mansur da Alhaji Yusif a waje suna son yin magana da maigari, dan Alhaji Yusif Mande da Alhaji Mansur Tofa manyan aminan Baffah ne da kowa yasani, tun kuma a daren jiya ya sanar musu abinda zasuzo yi anan ɗin. Abba ne yayma maigari bayanin nason ganin dangin Malam Sule baduku. Da kuma abinda ke tafe dasu. Jin sunan Zinneerah ya saka maigari jin dunbin daɗi a ransa, dan shi wlhy yama manta da yarinyarnan sam a rayuwarsa. sai dai yau dalilin ambatonta yasakashi farin ciki musamman da yaji dalilin zuwa waɗanan manyan mutane. Bakinsa a washe yace, “Ai Alhmdllh ma kun yanka akan gaɓa Alhaji, dan Malam Sule ɗinma ya dawo garin jiya-jiya, zanma iya cemuku yanzu da safen nan sukabar gabana shi da fitinanniyar matarsa akan rikici data tada dan yazo da sabuwar amarya daga Niger. Inaga yanzu bara na aika a kirashi shi dasu Rabilun ku zauna ku huta”. Sosai su Baffah sukaji daɗin jin cewar mahaifin Zinneerah ya dawo gida. Dan Abba ya sanarma Baffah cewar wancan zuwan da yayi ya iske bayanan ya bar gari ba'asan inda yakeba. A take maigari ya aika kiran Baba da su Kawu Rabilu, shi kuma ya shiga gida yasa aka fara haɗa fura da sauran cimar ƙauye domin fitoma baƙi. Bayan ya aika a siyo musu ruwan leda da lemo acan kusada dan musamman ya tada mai mashin. ★★ Baba na ƙofar gida tare da ƴan uwansa yana basu labarin tun barinsa gida ashe Niger ya dosa, acan yayi gamo da wani bawan ALLAH daya taimakesa saboda fahimtar baya cikin hayyacinsa da yayi. Shine ya dage masa da addu'a da neman magani harya samu lafiya acikin watanni shida. Koda yaga ya warke duk da ya tuna komai daya faru sai yace bazai dawo gidaba zaiyi zamansa can neman arziƙinsa. Aiko wannan mutumi yaji daɗin haka. a take ya ɗaurasa akan hanyar sana'a, cikin ƙanƙanin lokaci ALLAH ya amince masa abubuwa suka canja ya fara juya kuɗaɗe duk da bawai masu ɗunbin yawaba. Nadai rufin asirin ALLAH dai-dai gwargwado. Ganin zaman nasa bana ƙare bane mutumin daya taimakesa ya bashi auren ƙanwarsa da mijinta ya rasu bakuma ta taɓa haihuwaba, hasalima shekarunta biyar kacal dayin aure. Ya amsa hannu biyu yayma ALLAH godiya da wannan bawan ALLAHn nan, ya kumayi sa'a Zainaba nasonsa itama. cikin amincin ALLAH basu rufa wata uku ba sai gata da ciki, sunyi murna sunyi farin ciki mara musaltuwa. Da cikin ya tsufane yaga ya dace yazo gida da ita ta haihu a cikin danginsa, shine dalilinsa na ɗakkota suka taho yanzun. Cikin jin daɗi Kawu Sabi'u yace, “Yaya to yanzu kadawo garemu baki ɗaya kokuwa haihuwa kawai aka kawo yayarmu tayi ka sake gudu ka barmu?”. Kafin Baba ya bashi amsane ɗan aiken maigari ya iso. Tun anan ya gumtsa musu zancen baƙi. Cike da mamaki suka tashi suka bisa dan su dukansu fes suke cikin shiga ta kamala babu wani damuwa. Lokacin dasu baba suka iso sun iske an cikama su AK gaba da kayan abinci, duk da dai fura ce da ruwa da lemo, sai zabi da maigari yasa aketa yankawa ana shiga dasu cikin gida dan yacema matansa dan ALLAH suyi maza a gyara a gasasu gashi mai ƙyau. Fahimtar muhimmancin baƙin ya sakasu miƙewa suma babu sanya suka haɗu da ƴaƴansu suka fara aikin babu wasa. Koda su Baba suka iso Baffah ya buƙaci su zauna a waje suyi magana iyakarsu manyan. Sanin maganace mai muhimci tafe dasu maigari yasa aka sake saka musu tabarma ƙatuwa a zaurensa na biyu dake ƙarami bai kai na farko girmaba. Bayan duk sun zauna sukai gaisuwa ta mutunta juna. Inda Abba ya bama baba sani. Baba da dama tuni yake masa kallon sani yace, “Haba koda naji, tun ɗazun naketa tunanin wannan fuskar kamar na santa amma na kasa. Kai sannunku da zuwa, sannunku”. Fuskar Abba da murmushi yace, “Yauwa mun gode sosai Malam Sulaiman. Nasan zakai mamakin wannan zuwa namu, sai dai ba abin mamaki baneba. Kwanaki nazo garin nan amma ban samekaba. Zuwan nawa kuma yanada nasabane da Zinneerah ”. Da sauri baba ya dubesa jin sunan gudan jininsa abar begensa a koda yaushe. Murya a raunane yace, “Zinneerah kuma Alhaji Abubakar? Ai ina mai baƙin cikin sanar dakai muma nemanta mukeyi tun bayan wani babban al'amari na ƙaddara daya giftama rayuwarta”. “Eh nasan duk wannan Malam Sulaiman, dan akansama nazo kwanaki, sai dai rashin samunka ya sani komawa. Yanzu dai a taƙaice Zinneerah tana tare damu, dan waɗanan bayin ALLAH daka ganni tare dasu ma a dalilinta sukazo nan. Wannan” ya nuna Baffah. “Shima kawuntane, dan yayane ga hauwa'u, nasan dai bazaka gaza jin labarin dangin mahaifiyarta dake a bauchi ba sanda kuna tare? To Alhaji Kabir Shira yana ɗaya daga cikinsu,

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182