Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 179

Chapter 179

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

dawo ta koma sashenta tasa Saliha haɗa abin sha da motsa baki takai musu, ita kuma ta ɗauka abincinsu na dare da aka girka gaba ɗaya ta nufi sashen nasa. Ta iske Khalipha nata tsokanar Saliha dan mutuniyarsa ce sosai. Bayan ta gama zata wuce ta kirata tazo ta tattara yaran suje. Ɗaukar Anam tayi da tisa ƙeyar little da Amaan suka fita. Itama ta gama shirya abincin a dining zata fita Uncle Ahmad ya dakatar da ita. “Dawo ki zauna Inno ai maganar ta shafeki kema”. Dawowa tai babu musu ta zauna. Bayan Uncle Ahmad ya buɗe taron da addu'a ya fara musu da nasiha mai ratsa jiki, kafin ya duba AK da yay kicin-kicin da rai. “Abdul-Mutallab ayi haƙuri, a cigaba da haƙuri a ƙara haƙuri. Ita ƙaddara haka take babu abinda ya isa tsaidata ga bawa. UBANGIJI ya riga ya hukunta faruwar hakan a garemu tilas. Hakan jarabawa ce. Maganar tone-tone bama ta tasoba tunda anyi komai ya wuce sai ayi haƙuri kuma a sake kafa sabuwar rayuwa. Ga Farah nan ta dawo cikin iyalinka. Ina fatan zaku manta da komai ku ringumi junanku kuyi haƙuri. Darajar haƙurin da zakuyi sai ALLAH ya ƙara muku kwanciyar hankali da farin ciki kaji”. Kan AK a ƙasa yace, “Dady taya zan zauna da wadda bata amshi laifinta ba, girman kai ya hanata neman yafiya ga wadda suka zalunta duk da rawar gani data taka wajen hana katsewar igiyar aurenta”. Shashshekar kukan Farah ne ya fito, tace, “Wlhy ba girman kai ya hanani neman gafarar Zinneerah ba kunya ce kawai da nauyin girman laifin da aka aikata mata, duk da ALLAH shine shaidata ban sanma wadda aka sakama ciki ba. Amma inajin nadama da kaico da kawunanmu saboda son zuciya. Zinneerah ki yafe mana domin ALLAH badan halinmu ba. Duk da nasan munzo a makare ga neman gafarar taki. Amma dan girman ALLAH ki gafarcemu, gwiyawunmu bisa ƙasa........” Sauron katseta Zinneerah tai da faɗin, “Haba aunty Farah, wlhy ni ban rikeku ba tun a waccan ranar komai ya wuce a gareni. Sai dai muyi fatan ALLAH ya yafe mana baki ɗaya. Ya kuma bamu zaman lafiya da haƙuri da juna”. Da amin duk suka amsa. Yayin da AK ya ballama Zinneerah harara. Murmushi kawai tayi ta ɗauke kanta. Shima AK ɗin gafararsa Farah ta nema, duk da dai bai kulataba bai kumace uffanba. Uncle Ahmad dai ya ɗora musu da sabuwar nasiha data ƙara sanyaya jikinsu. Da ga ƙarshe ya rufe taron da addu'a suka tattara suka tafi aka bar Farah anan. Tashi Zinneerah tai zata barsu AK ya dakatar da ita wai ta haɗa masa ruwan wanka. Kafinma ta nufi ɗakin shi ya shige. sai taji duk babu daɗi ga Farah zaune ko kallonta baiyiba. Tayi tunanin Farah zata ɓata rai, sai taga kawai ta bisa da kallo tana murmushi da share hawaye a kaikaice. Ta maido dubanta ga Zinneerah datai shiru kanta a ƙasa ta kasa tashi. “Mamin Abdul kije karya ga kin ɓata masa lokaci, sai dai ki sake roƙamin shi gafara dan ALLAH, da kuma keys ɗin sashena”. “Kiyi haƙuri dan ALLAH aunty Farah komai zai wuce. Kinsan dai halinsa kinma fini sani. Keys kuma suna wajena ma bara na ɗauka miki”. Tai maganar tana nufar hanyar ƙofar fita. Da sauri Farah ta dakatar da ita tana miƙewa. “A'a kinga jeki ki cika umarninsa zanje na jiraki a general falo”. Kai Zinneerah ta kaɗa mata kawai cike dajin nauyi ta nufi ɗakin nasa. A cike fam ta iske AK da haushi. Kamar jira yake tana shigowa ya balbaleta da masifa wai ta wulakantasa bayan ya faɗa mata bukatarsa. Hankalintane ya tashi dan faɗa sosai yakeyi. Ganin abin karya juye mata yasata faɗawa jikinsa ta manne bakinsu waje guda ta shiga lallashi ta hanyar da yafi buƙata. Ai ko saigashi yay bulum harma yana neman zurmawa. Da ƙyar ta ƙwace kanta ta na masa dariya. Ƙwafa yay da fadin, “Zan kamaki ne ai, zakimin bayani dalla-dalla tunda na fara zama abokin wasanki”. Ita dai shigewa toilet tai tana masa dariya. Da taimakon su Saliha Farah ta gyara sashenta, Zinneerah takai mata abinci da kanta tana sake mata sannu da zuwa. Dan harda yara taje mata. Jawosu Farah tai jikinta ta rungume ƙwalla na cika mata ido. Little kam daga jikin Zinneerah ya makale yana gaisheta. Duk yanda taso yazo gareta yaƙi dole ta haƙura. Anan ta bar mata Amaan da Anam suka fita ita da little tana masa faɗa. Buɗar bakin yaron nan sai cewa yay, “Mami ni bana sonta...”. Baima rufe bakiba ta make bakin har yana fashewa. Ta shiga masa masifar da ta kai har AK dake falonsa fitowa dan suna a general falo ne tsaye. Kallon yanda bakin little din ke jini yana kuka yayi. “Lafiya? miya miki haka harda fasa baki?”. Ranta a ɓace tace, “Idanma ya sake maimaita abinda ya faɗa wlhy haƙwaran zan zubar ƙasa. Dalla matsamin na wuce mara mutunci”. Ta faɗa tana turesa tai shigewarta sashenta. Da kallo AK ya bita ransa a ɓace, dan ya tsani ana dukar masa yara itama kuma ta sani, yakance ko laifi sukai ta zaunar dasu ta musu nasiha bawai dukaba dan baya magani. Hannun little ɗin ya kama suka shige sashensa yana tambayarsa miyayi mata?. Abinka ga yaro saiya maimaita abinda ya fadama Farah ɗin. Faɗa shima yay masa da nasiha akan karya sake itama Momy ce. Yaron sai yace bazai sakeba ya kuma bashi haƙuri. Tare da cewa bara yaje itama Mami ya bata haƙuri. Cayay ya barta idan sun dawo salla saiya rakashi ya bata. Haka kuwa akai bayan sun dawo salla sashen Zinneerah ɗin suka shiga shi da little. Acan ɗakinta na ƙurya suka sameta ita da Saliha suna magana. Saliha ta gaishesa ta fice. Zama yay bakin gado little kuma yaje gabanta ya durƙusa. “Mami kiyi haƙuri bazan sakeba dan ALLAH”. Shiru tai masa tamkar batajiba sai da AK ɗin yace tunda ya baki haƙuri ba kuma sai ya wuce ba. “Yayanmu so kake na haƙura gobe ya sake kenan? Shi ɗan karamin nan dashi har yasan wani cewa baya son mutum?”. Kuka little yasa mata yana ƙara bata haƙuri hannayensa riƙe da kunnuwansa. Nanma dai baki AK ɗin yasa harta haƙura. Little ya fita ya barsu a ɗakin saboda aikansa da tayi wajen Saliha. Mikewa tai tana ninke abin sallar da take kai zaune, AK dake binta da kallo yace, “Kemafa masifanki yayi yawa”. Baki ta kumbura gaba amma batace komai ba. Hakan yasa AK kamota ta faɗo jikinsa. Lips ɗinta ya ɗalla da yatsunsa yana faɗin, “Dan wulakancin kin fasamin bakin yaro harda jini”. Murmushi tayi tana cusa kanta a ƙirjinsa da faɗin, “Kaga gobe idan zaima wani rashin kunya sai ya tuna da wannan ai”. “Uhmyim, to ai ba ƙyaleki zanyiba sai na rama masa”. Yay maganar yana ɗaura lips ɗinsa kan nata. Daga hukunci aka zarce soyayya. Daga karshe dai sai da aka kai gayin wanka...........✍ *_Dan ALLAH ku saka ɗan uwana addu'oinki na yinin yau, ya ɓata an rasa inda yake kuma babu labarinsa. ALLAH ya bayyanashi, ya karama mahaifiyarsa damu nutsuwa. Ya kuma tsaresa a duk inda yake. Ya bashi kariya daga abokan banza ko miyagun mutane. Tare da sauran al'ummar musulmi

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182