Chapter 69
Chapter 69
basu izinin shiga sannan ta shigo riƙe da Zinneerah da ganin Khalipha yasaka kukan nata tsagaitawa. Miƙewa Dr Mahmud yayi yana mata sannu, shiko kansa yana duba wani file bai ɗagoba balle ya nuna yasan sun shigo office ɗin. A kujerar dake kallon wadda yake zaune Dr Mahmud yasa Nurse ɗin ta zaunar da ita. “Sorry ƙanwarmu kukan ya isa ko?”. Dr Mahmud ya faɗa yana murmushi da kallon Zinneerah ɗin a zuciyarsa yanaji kamar yasan fuskarnan. Kanta taɗan jinjina masa tana ƙara takure kanta waje ɗaya a cikin kujerar dan kusancinsu ya sakata jin ta takura, duk ya cika wajen da kwarjininsa. Kallonsa taɗan sata taga har yanzu yana a yanda suka samesa. ta janye tana maidawa ga Dr Mahmud daya jeho mata tambaya. “Ƙanwarmu mike damunki ne?”. Ɗan jimm tai kamar bazatace komaiba dan har sai d Yah Adnan dake saurarensu ya ɗan ɗago ya dubeta ya maida kansa. Fahimtar da Dr Mahmud yay kamar tanajin nauyin maganar saboda AK ya sashi faɗin “To ko dai zamu tada boss a wajen nan ne? Ranka ya daɗe kamarfa........” Saurin katsesa tai da cewa, “Cikina ke ciwo”. AK daya ɗan ɗago ya dubeta a karo na biyu saiya girgiza kansa kwai kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya sake maida kansa ga takardun hannunsa. Takarda da pen Dr Mahmud ya tura mata, “Idan babu damuwa rubuta anan kawai”. Har cikin ranta taji daɗin hakan, babu musu taja takardar ta fara rubutawa tana cije baki. Koda ya amshi takardar ya duba yaga mita rubuta sai baice komaiba ya jin jina kansa yana nuna mata ɗan gadon duba marasa lafiya dake can gefe. “jeki kwanta acan ina zuwa”. Miƙewa tai cike da ƙarfin hali ta nufi gadon ta kwanta. Shima sai ya miƙe ya bita da wani ɗan dogon roba a hannu da syringe. Tambayoyi ya ɗan ƙara mata tana bashi amsa cike da jin nauyinsa. Daga haka ya ɗiba jininta. A dai-dai nan Khalipha yay sallama ya shigo office ɗin. Ɗagowa Yah Adnan yay ya dubesa da ɗan mamaki. Amma baice komaiba. Khalipha da hankalinsa duk yana ga yanda yaga Zinneerah ɗin ya ƙaraso yana faɗin, “Yayanmu barka da dare”. “Dama kana nan?”. “Eh wlhy ban jima da zuwaba. Dr Muneer ne ya kirani mukai wani aiki. Miya samu Beauty ɗin ne?”. Wani ɗan luu da idanu yayi da tsatstsare Khaliphan da idanu tamkar baiji miya faɗa ba. Shima Khaliphan sai yanzu ya fahimci katoɓarar da yay na cema Zinneerah beauty ɗin. Ya ɗan sosa gefen wuyansa yana murmushi. “I'm sorry yayanmu”. “For what?”. Ya faɗa cike da salon basarwar tasa yana maida kansa ga file ɗin hannunsa. Dariya Khalipha ya ƙyalƙyale dashi yana barin wajen ya nufi can inda Zinneerah da Dr Mahmud suke. “Oh oh sweet sister sorry, dama haka kike ragguwa ashe?”. Dr Mahmud ne ya bashi amsa cikin dariya. “A'a Khalipha karfa ka cika baki, dan sai na bata labarin naka rakin kaima”. “Lalala Yah Mahmud yi haƙuri kar kaja ta rainani, mike damunta ne? Naga kamar sun shigo tana ɗingishi”. Kai tsaye Dr Mahmud yace, “Tana complain ne na mara, inaga zamuyi mata text mugani, duk da ina zargin dai bazai wuce....” Sai kuma yay shiru yana ɗan duban sashen da AK yake zaune. Addu'ar samun lafiya Khalipha yay mata yana ɗan murmushi da kauda zancen ta hanyar cewa, “Bara naje da jinin lab to”. Daga haka ya fita. Duk abinda suke tattaunawa Yah Adnan na jinsu. Amma saika rantse ma baya office ɗin, daga ƙarshema waya ya kira har Khalipha ya dawo bai gamaba. Drip Dr Mahmud ya sakama Zinneerah ya dawo inda AK yake ya zauna suka cigaba da tattauna abinda ya shafesu har Khalipha ya dawo da result ɗin da magunguna daya sayo. Bayan Dr Mahmud ya amsa ya duba yace, “Dama abinda nai zargi kenan, bazai wuce harda Imfection ɗin ba, zamuyi treating ɗinsa insha ALLAH zai barta tunda baiyi ƙarfi ba. Tunda ma ka haɗo maganin inaga kai mata allurar nan kawai”. Miƙewa Khalipha yay yana faɗin, “Okay ALLAH yasa dai bata tsoron allura to”. Dariya kawai Dr Mahmud yayi, shima bayan ya mata allurar duk da barci naɗan figarta sai ya fita ƙarasa uzirinsa. Yabar Dr Mahmud suna cigaba da tattaunawa da Yayan nasu da ya koma kamar baya office ɗin. ★★★ A gida kuwa Farah tamkar zatai ƙaramin hauka a cikin ranta. Tanada kishi sosai wanda ita kanta wani lokacin abun har tsoro yake bata, dan Adnan dai ba taɓa mata alƙawarin bazai ƙara aure yayi ba. Ko lokacin da su Hajiya Iya suka takura masa saiya ƙara aure badan tsayawar Mammah a kansa ba da babu abinda zai hanashi ƙarawar duk da ba nuna mata yanada buƙatar hakan yayiba. Tsaf hajiya iya tana lure da ita. Kuma dama da biyu ta hanata bin nasu. Dan haka ta shige ɗaki abunta tai shirin barci ta kwanta tunda tasan dai ba binsu Farah ɗin zataiba a yanzu. Kamar yanda ta ƙware akai ƙara wajen Mammah yanzu ɗinma sai da ta faɗa mata tana kuka. Ran Mammah ya ɓaci sosai jin yarinyarma ba'a cikin ƙannensa takeba kamar yanda ita Farah ɗin tace tana tunani. Koda Mammah ta kirasa ashe wayar a nan gida ya barta, bai fita da ita ba, na hannunsa na alaƙar business ɗinsa ne kawai. Wannan abinne ya ƙara ƙular da Farah ta dinga kai kawo tsakanin ɗakinsa da falo ita kaɗai dan hajiya iya dai ta shige. yaran kuma da suka dawo basu shigo nanba dan a gajiye suke. ★★ Sai kusan sha ɗaya ruwan da aka sakama Zinneerah ya ƙare suka nufo gida. Tana a baya ita kaɗai, Khalipha ne yanzu ya amshi driving ɗin, shi kuma yana a gefensa zaune. Babu mai magana a motar dan duk sun gaji kwanciya duk suke buƙata, sai sanyin ac daya takurama Zinneerah, hakan ya sata dunƙulewa waje guda barci sama-sama nason figarta. Koda suka iso gidan Khalipha ne ya buɗe mata ta fito, ganin yanda take ɗan tangaɗin barci dana rashin ƙwarin jiki yace, “Ƙanwata kodai na kamaki ne?”. Kanta ta girgiza masa a hankali cikin yanayin kasala tana dafe jikin motar dan ji take tamkar zata faɗi. Ɗan matsawa Khalipha yay da ita gab yana ƙoƙarin kai hannunsa zai kamo nata. Yah Adnan dake kallonsu ta gefen ido, amma saika ɗauka gaba ɗaya hankalinsa baya tare da su ya katse hanzarin Khalipha ɗin dake neman kamo hanun Zinnerah, “Besty kaje da takardun nan ɗakinga zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu saika dubasu zamuyi magana daga baya”. Dole Khalipha ya haƙura daga son taimakon Zinneerah ya juya garesa ya amshi takardun. “Kaje kawai sai da safe muma bara mu shige dare yayi. Ke kuma muje”. Ya sake faɗa ciki-ciki yana duban Zinneerah da duk tana saurarensu. Dole Khalipha yay musu sai da safe yana nufar sashen samarin gidan. Shikuma ya tasa Zinneerah dake tafiya da ɗan layi na barci suka nufi sashen hajiya Iya. Abin tsautsayi tana tura ƙofar falon da niyyar shiga hannunta ya gota akan handle ɗin saboda tuntuɓe da takalmi da tai. Saurin tarota yay ganin zata faɗi, saboda ya rigada ya kawo jiki ita kuma tayo baya. Sai kuma ya ɗagata da hanzari yana miƙar da ita tsaye sosai akan ƙafafunta. Ɓoyayyen numfashi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182