Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

saukeku lafiya. Mikikeso na sayo miki idan zan dawo?”. Ƙasa Zinneerah ta karayi da kanta cike da girmamawa da ƙaunar wannan bawan ALLAH. Shima sai ya miƙe yana murmushi, “Shikenan tunda kin kasa faɗa, kafin dai na taso ki faɗama mamanki saita kirani a saya miki komi kikeso ɗin”. “Nagode Abba, ALLAH ya tsare ya bada sa'a”. Murmushi ya sakeyi cike dajin son yarinyar a ransa. Ya amsa idonsa akan matarsa. ___________________★ Tun daga wannan ranar babu wanda ya sakema Zinneerah magana akan sanin uban cikin jikinta da dalilin barowarta gida. saima kulawa ta musamman da Maman Sadiq, Abba, Maman Halima suka sake ninka mata. Koyaya aka ganta a damuwa sai anbi ba'asinta domin son kauda mata. Duk da Maman Sadiq na kawaici a kanta cikin hikima take jan abarta a jiki idan sun shige ɗaki, hakan yasa shaƙuwa mai ƙarfu ke sake shiga tsakaninsu, tana sake sakin jikinta sosai kuma. hakama ƙannenta idan ka gansu saika ɗauka dama can tare suka tashi. A wajen ƴaƴan Maman Sakina (Saude) ne kawai Zinneerah batajin daɗi da ita kanta Sauden. Dan ko ranar girkinta bacin Maman Sadiq nakai zuciya nesa da sun dinga tafka rigima akan abincin da ake zubama Zinneerah ɗin. Amma sai bata cewa komai ta barta da halinta. Tadai gargaɗi Zinneerah ɗin akan koda wasa karta shiga hurimin Maman Sakina da ƴaƴanta inhar ya wuce gaisuwa da girmamawa. Sannan duk wanda zai sakata aiki a gidan tai masa indai ya girmeta. Dayake Zinneerah ɗinma bamai kwaramniya bace sai tabi huɗubar mahaifiyarta aka zauna lafiya. Dan duk da cikin dake tare da ita da gadara Maman Sakina ke sakata aiki a gidan, itako babu musu takeyi koda batajin daɗin jikinta. Saima idan Maman Halima taga abin yayi yawane takanyi magana kota hana Zinneerah ɗin. Haka yakan saka Maman Sakina taita masifa a gidan da gori tana kiran Zinneerah da suna agola kinfi masu gida. Maman Sadiq bata taɓa tankawaba, bakuma ta taɓa gayama mai gidanba. Ta kuma roƙi Maman Halima akan karta faɗa itama, dan tasan duk dai iya zaman Zinneerah a gidan naɗan lokacine kafin ta koma gidan mijinta. Haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa Zinneerah na rainon cikinta dake bata wahala. dan bata taɓa ƙulla kwana biyu babu ciwo. Sai dai yanda cikin ya fito ɗas a jikinta ba ƙaramin ƙyau yasa tayi ba. Gashi tana samun kulawa sosai yanzun. Dan hatta da zuwanta asibiti Naziru ke zuwa ya kaita kamar yanda Khalipha ya bar masa sallaho. A ranar farko da suka fara komawa asibitin domin ganin likita Zinneerah ta samu damar ƙare masa kallon tsaf bayan ta karanta sunan asibitin tun daga waje. *_SHIRA HOSPITAL_*. Sosai take jinjina ƙoƙarin maginin wannan asibiti, dan yayi ƙyau sosai kuma an zuba masa kayan aiki bana ƙaramin kuɗiba. Ga likitoci ƙwararru da basa wasa da aikinsu kuma babu wulaƙanci. Sai dai abinda ke matuƙar bata mamaki yanda asibitin yay matuƙar haɗuwa zaka ɗauka sai wane da wane ne masu iya shigarsa neman lafiya, amma saika shigo ciki kai gamo da masu karamin ƙarfi bila-adadin suna amsar magani hankalinsu kwance. Samun damar ganin likita akan lokacine ya katse mata dukkanin tunaninta. Sai dai yanda aka karɓesunne ya sake bata mamaki, amma jin zancen Khalipha a bakin likitan kuma sai ta fahimci a dalilin shine ake mata wannan tattalin da kulawar. An bata magungunan da suka dace da ita, tare da sake gargaɗinta akan daina duk wani aiki dan cikin jikin nata yana buƙatar hakan saboda ƴar matsalar da suka hanga tattare da shi. Ƙuruciya tasa batako damuba suka dawo gida. Sai dai bayanin da Naziru yayi na maganar kula da hutun nata a gaban Yayansa da bai kai ga fitaba yasa Abba gargaɗin kowa na gidan akan yasa ido kar Zinneerah ta sake wani aiki. Baki maman Sakina ta taɓe cikin ƙunƙuni take fadin, ‘Wayaga agola kinfi ƴaƴan gida’. Babu wanda ya tanka sai shi Alhajin ne ya dubeta rai ɓace, “Saude mikike faɗa?”. A zabure ta mike tana yarfar da hannaye da tafasu, “A'a kaga Alhaji bance komaiba nikam, karkuma a bugamin gangar ɗan bazakuɗa babu gaira babu sabar”. Daga haka tabar wajen fuuu. Ƙwafa yay kawai batare da yace komaiba. Tun daga wannan zuwan sai yazam Naziru kanzo ya kaita asibitin ganin likita kamar yanda akan rubuta musu. A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai ga cikin Zinneerah ya shiga watanni na takwas. Zuwa yanzu ta saki jikinta sosai a gidan, musamman ma da mahifiyarta da kannenta dake faɗaɗa farin cikinta a koda yaushe. Idan ka ganta bazaka taɓa dauka ita bace, bakinta ya buɗe sosai alamar dama can rashin samun ƴancin kai ke sakata zama mai sanyi. Ita kanta maman Sadiq har mamaki take a ranta dama Zinneerah nada surutu haka? Ta tabbatar nan gaba idan ta sake warwarewa sai tafima haka kauɗi. Danma lalurar cikin kanɗan taƙaita mata wasu abubuwan. Duk da waɗanan sauye-sauye da Zinneerah ta samu a rayuwarta hakan baisa ta manta da Khalipha a rantaba. Koda yaushe yana nan maƙale a ranta, wani lokacin har mafarkinsa takeyi, kota zauna zugum tana tunanin yaushene zai sake dawowa gareta ne ko dan ta masa godiya akan ɗawainiyar da yayi da ita?. Idan kuma Naziru yazo gidan har ALLAH ALLAH take taji yace Khalipha na gaisheta, dan yana kiransa lokaci-lokaci idan ya samu dama. Sai dai bai taɓa cewa a haɗasuba dan shi duk zatonsa tanada aure ne. Yauma kamar kullum suna baje a falon Mamansu suna cin gyaɗa dafaffe da Zinneerah ta ƙwallafa rai sai da aka sayo aka dafa mata, kallo suke suna kwasar dariya. Maman Sadiq dake ciki tana shirin tafiya sashe Alhaji ta fito falon da kwalliyarta. Kallon yanda suke cikin nishaɗi tayi daɗi da farin ciki na ratsa ranta itama. Ta ɗauki tiren data shirya abincin Alhajin tana faɗin, “Zinneerah tashi ki tura muku ƙofar ni zanje na kaima Abbanku abinci, idan kunji barci kafin na dawo kimasu Aliyu addu'a karsu kwanta babu addu'a. Wannan sarkin fitsarin Abdull ki tabbatar ledan katifan bata zameba a inda zai kwanta. Ga kuma magungunanki nan kisha kema kafin ki kwanta”. “To mama sai kin dawo”. Ta faɗa fuskarta washe da murmushi. Suma sauran yaran duk adawo lafiyar sukai mata ta ɗauki tiren ta fice. Yayinda Zinneerah ta saka Sadiq zuwa ya tura ƙofar suka cigaba da kallonsu. A can ɓangaren maman Sadiq ko bayan Alhaji yaci abincinsa ya ƙoshi take dubansa da damuwa. “Yaya dan ALLAH karkace na takura, baka ganin kuwa ya dace mijin yarinyarnan yasan wani abu game da ita”. Murmushi Alhaji yayi na manya. Ya gyara zamansa da cewa, “Eh kina kan gaskiyarki Hauwa'u, nima bawai hakan baya raina bane. Dama inason dai ta gama sakin jikintane sosai ta manta da duk wani ɓacin ran da yabarota daga gidan sannan. A yanda kuma nake tunani bata wajenta ya kamata muji komaiba. Nine zan shirya da kaina naje Danya ɗin domin ganawa da Baban nata da Mijinta. Kinga idan mun samu bakin zaren saimu yanke hukuncin daya dace. Dan indai ba rabuwa tai da mijin nataba tofa sai dai yasan mai yuwuwa”. Murmushi kawai taɗanyi, “To duk hukuncin daka yanke ai shine dai-dai Yaya. ALLAH yay mana jagora”. “Amin” ya faɗa yana maijin daɗi a ransa na yanda duk ta sakar

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182