Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 159

Chapter 159

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

bashi tare da masa bayanin a yanda abun ya kasance bada shiriba. Yasha mamaki matuƙa, amma cewar hajiya iya zaman nasu nada nasaba da auren yasa mai-martaban yin shiru bai nema ƙarin bayani akan zancen little ba da yana a falon jikin Abbah, dan tunda ya gansu shi da mmn Sadiq kuma ya maƙale musu cike da murna dan duk duniya su yafi sani fiye da kowa, tunda ko uwarsa batai wahalar da sukai a kansaba bayan ta haifesa. Waziri ne ya gabatar musu da addu'a. Kafin hajiya iya ta fara magana. “Zan fara da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai, dan shine yay sanadi da silar taramu anan ta dalilin wani saka mai sarƙaƙiya da duk ta sarƙe zukatanmu kafin shi wannan zaman. Anan mu dukanmu iyayene kuma kakannine, dan haka ina fatan zamu bada haɗin kai wajen nutsuwa mu fahimci abinda ya taramu, sannan duk wanda al'amarin ya shafa dan ALLAH ina mai roƙonsa dayaji tsoron ALLAH mai zartar ga hukunci a sanda yaso ga wanda yaso ya faɗi gaskiyar abinda ya sani. Mun cire hukuma ne a wannan zancen saboda wasu dalilai. Ba kuma hakan na nufin bazamu iya maida komai garesu bane duk da mun kasance a ƙarƙashin inuwar zumunta ta dalilin aure da sauransu. Wannan yarinya da kuke gani.....” Ta nuna Zinneerah da kanta ke a durƙe tamkar Farah. “Sunanta Zinneerah. Malam Sulaiman gashi nan zaune shine mahaifinta. Wannan kuma Hauwa'u ɗiyar ƙanwata itace mahaifiyarta. Waɗan nan iyaye sun rabu sanadin ƙaddara data saka Zinneerah zama a hannun matar uba bayan barin Hauwa'u gidansu. Inda ita wannan matar uba nata ta raineta cikin gallazawa da son zuciya, a ƙarshe kuma ta miƙata aikatau bada sanin mahaifintaba. Sanadin wannan aikatau ta dawo musu da ciki da suka rasa daga ina ta samosa. Aka turketa da tambayar duniya da barazana tace ita bata aikata komaiba kuma batasan mai ciki ba. An turza iya turzawa tace bata saniba. To a yanzu dai wannan yaro dake jikin Alhaji Abubakar shine ɗan data haifa. Nasan kuma duk wanda ya kallesa zaiyi mamaki da ruɗani akan kamanninsa da Moddibo. Kuma komi za'a faɗa bazai yardaba zai dangantashi da shi a matsayin mahaifinsa kamar yanda muma mukaitayi. Bazan kaiku da nisaba, ga dai wadda ta kai Zinneerah aikatau birni, zamu fara ji daga gareta yaya aka haihu a ragaya. Hajiya Lanti bismillah”. Hajiya iya ta ƙare zancenta da kallon Hajji lanti dake zaune ita da hajiya Haule da kallo ɗaya zakai mata ka tabbatar a gigice take tun zuwansu gidan. Zama hajji lanti ta gyara. Kanta tsaye ta fara magana da iya gaskiyarta. “Ni Lantana nayi alƙawarin faɗar gaskiya kamar yadda Hajiya mama ta buƙata, zanyi hakanne kuma domin na fita har a wajen UBANGIJI na. Wannan sunanta hajiya Haule. a garin katsina take zaune. Na santane dalilin wata ƙawata ƴar kankia da muke zuwa sarin kayan koli kano, itace ta haɗani da ita akan na dinga kai mata yara masu aikatau. Zuminci ya ƙullu a tsakaninmu mai ƙarfi saboda kai mata yara da nakeyi akai-akai. Har ALLAH yasa Zinneerah ta shiga sahunsu a dalilin matar mahaifinta Asabe. Labarin kuɗin da ake samu a dalilin aikatau yasa Asabe ɗaukar Zinni ta bani saboda ta mallake babanta ga shinan bai iya ce mata bai iya musata. Na ɗauka Zinni na kaita garin katsina aikatau tare da wasu yara, washe gari na juyo da nufin komawa gida ƴan doka suka kamani a tsaranci dalilin wata yarinya. Kusan shekarata biyu a gidan kaso, na fito shine naci karo da mummunan labarin Zinni ta dawo da ciki. Wlhy, wlhy, wlhy, wannan shine kawai abinda na sani, amma bansan komai game da cikin Zinni ba”. Kowa ya gamsu da zancenta, dan haka suka maida dubansu ga Hajiya Haule dake sharar zufa. “Nima nayi alƙawarin zan faɗi gaskiyata ni Hajiya Haule, dan faɗan da yafi ƙarfinka masu iya magana sunce ka maidashi wasa. Kamar yanda Hajiya lantana ta faɗa duk anyi haka. Ta kawomin yara ciki harda wannan yarinya Zinneerah saboda dama muna irin wannan huɗɗar. Inda ni kuma na danƙata hannun Hajiya Zakiyya. Amma kafin ita Zinneerah dama akwai wata yarinya da na taɓa bama ita Hajiya Zakiyya ɗin. Wadda ta sanarmin zasuyi mata aikine kuma zata bani maƙudan kuɗaɗe harda iyayen yarinyar. Babu wani ja'inja na yarda duk da kuwa bata fito ta sanarmin da ainahin aikinba, amma jin kuɗi ya sani ruɗewa na amince mata. A tashin farko ta diremin dubu ɗari biyar, hakan yasa a haukace na kai mata wata yarinya da aka kawomin dan sama mata aiki. Sai dai kuma bansan yaya akaiba bayan kusan sati ɗaya ta dawomin da yarinyar akan na sama musu wata ita bazata iya aikin da suke buƙataba. Nasha mamaki saboda yarinyar dana basu babba ce, nasan kowane irin aiki aka sakata zata iya. Dan haka na kasa daurewa na tambayeta duk da inajin tsoro saboda girmanta da kasancewar wadda ta fito daga masarauta. A lokacin bata kulani ba. ta daice naje idan an samu tana jira. Haka na baro gidanta cike da wasiwasi amma bani da mai bani sani sai ALLAH. Anyi haka da kusan wata ɗaya sai ga Hajji Lanti da yara. Da farko dai ƙyawun ita wannan yarinya yasani jin sha'awar kai mata ita, dan nasan masu kuɗinnan dason ƴar aiki mai tsafta da ɗan fasali haka. Cikin amincewar UBANGIJI kuma tana ganinta sai tace tayi, ta kuma ɗauka cikon kuɗina har naira miliyan ɗaya ta bani, duk da dubu ɗari biyar ya kamata ta cikamin. dan munyi da itane akan miliyon ɗayan, nawa dubu ɗari biyu na iyayen yarinya dubu ɗari uku, na yarinya ɗari biyar, amma ban saniba ko jin daɗin samo yarinyar yasata bani ƙarin dubu ɗari biyar, bakuma tamin bayanin ta karanba sai da naje gida na kirata dan duk zatona ko bata kulaba ta bani. Amma sai tace min tana sane. Samun yarinyar dai-dai da ra'ayinsu yasata ƙara mana waɗanan kuɗi mu da iyayen yarinyar. Ta kuma ɗora da faɗamin zasuma yarinyar dashe ne na ciki, idan yakai wata biyu zasu ɗauketa zuwa ƙasar waje har saita haihu musu su sallamota da tagomashin arziƙi, amma wannan sirrine tsakaninmu, ko iyayen yarinyar bataso su sani kawai nace dasu ta tafi turai ne da yarinyar inda take zama da mijinta. Iya abinda ta sanar min kenan ta yanke wayarta. Harga ALLAH na girgiza da zancen sai dai inda aka fi ƙarfi nane bani da damar cewa komai. Kamar yanda ta buƙaci karna bar Nigeria sai aikinsu ya kankama na amince, dan dama kuɗin data bani so nake na koma ƙasar saudia inda dama can nake zaune a da. An yayonine an maidoni rashin kuɗi yasa ban komaba. Gaba ɗaya na mallake kuɗi har na iyayen yarinya dana yarinya da tace, ko Hajji Lanti data kawomin yarinya ban nema ba. Dan na shirya kamfinma ta dawo amsar kuɗaɗen yaran data kawo nabar ƙasar insha ALLAHU. Bayan anyi haka da sati uku inata shirina sai ga wayar hajiya Zakiyya, ta tabbatarmin aiki yayi zan iya tafiyata cikin murnarta. Nima naji daɗi sosai dan dama kayana a shirye suke, hakan yasa kwana biyu dayin magana da ita na wuce saudi-arebia da yara guda biyu. Daga haka ban sake sanin komaiba sai jiya da ƴan sanda

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182