Chapter 93
Chapter 93
ɗiba ne a tahiyar da nayi, dan nasan iyayensu hankalinsu a tashe yake. Nafara zuwa nan wajenki dan naji ko yarinyar gidan nan ta dawo ita kafin naje sauran gidajen suma naji yaya ake ciki? Dan naje can gidan hajiyar da nake kaima yaran a katsina na iske wai ta tahi saudia shekara biyu kenan”. Ɗan waige-waige Inna ta fara, ganin su Sa'a har yanzu suna ɗaki tare da Karima dan Tinene ma ta fito tuni ta samesu. Ƙasa-ƙasa ta maida muryarta tace, “Ta dawo tun bayan mako uku da tahiyarku ai”. Cikin zumuɗin dajin daɗi Hajja lanti ta ce, “Kai ALLAH na gode maka”. Baki Inna ta taɓe tana gyara zama. “To ai baki saniba da ɗan ƙunshi ta dawo mana, nikuma a sanadinsa na kaɗa kanta tabi duniya yanzu haka ance tana birnin ikko ta kama ɗaki”. “Kina nihin ciki tazo dashi Asabe”. “Ƙwarai da gaske hajja lanti, dan ciki ma ya giyata ya hito duniya ta sani kahin nasata barin garin nan bayan na rihe bakin tambaɗaɗɗiyar gudun karta tona mani asiri dan na hiɗima duniya cewar yawan tazubar dama ta tahi tunda dagani sai ke mukasan yanda akai”. “Amma asabe.....” “Karkice komai hajja Lanti, dan kema kinsan komai akan tsanar ɗiyar nan danai, kinga can wajen” tai nuni da ƙasan turminsu na daka. “Acan na binne tsiyar, kinsan malam kallamu, shine yay mani aikin nan na rihe bakin kowane shege har abada kuma babu maiji, kema na hiɗi maki ne dan nasan abikiyar cin mushe ce. Kema kuma baki rihemani komai na rayuwarki”. “Hakane Asabe. Amma ni abinda yaban mamaki ma a ina yarinyarnan ta samu ciki to? Kodai dashi ta tahi daman? Dan inda na kaita bawata harkar banza akeba, inbadai bayan barina ta samu wajen aiki ba acan komai ya hwaru”. “Sudai suka sani lanti, ni dai tunda na kaɗata kuma bakin kowa ya rihe miye damuwata. matsalata kawai tahiyar malam adalilin barinta gida, amma inaji a jikina shima ya kusa dawowa gareni”. “Ban ganeba yimani karin. bayani”. Babu musi Inna ta shiga bata labarin komai tana matsar hawaye, dan tana son baba so mai yawa da itama batasan adadi ba a rayuwarta. Sa'a dake laɓe a bayansu tanajin komai ta sharce hawaye da fitowa kamar batajiba ta fara haɗa wutar ɗorama Karima ruwan wanka kamar yanda innar tace. tana ƙoƙarin aza garwar wankan maƙwafta suka fara shigowa ƴan barka da ganin ƙwaƙwaf dan sai yanzu labarin dawowar karima gidan ya fara zuwa kunnuwansu. Daga haka hirarta da hajja lanti ta watse. tashi hajja Lantin tai ma ta tafi bayan taje taga baby itama. dan mutane sai kallonta suke tunda ita ba ɓoyayya bace a garin dama tayi dillanci kafin fara ɗaukar yara tana kaiwa aikatau birni. Ta tafine ranta makale da zancen Inna akan cikin Zinneerah. Itakam wahalar da taci a rayuwa yasa tayi nadama. Ta nunama Inna tana tare da itane kawai danta samu bakin zaren da zata taimaki Zinneerah. dolene saita koma katsina ta binciko ainahin gaskiyar abinda ya faru da ƴar mutane kozata samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya. Yanzu hakama zataje sauran ƙauyikan data ɗakko waɗancan yaran ne dan taji sukuma yaya suke ne? Ta kuma nema gafarar iyayensu. Firar Inna da Hajja Lanti tasa Sa'a kuka sosai a yinin yau, saboda ƴan barka daketa shigowa yasa taketa ƙoƙarin dannewa har dare ya rufa. Saboda ƙudirin dake ranta yasa yau tai shirin kwana a gidan nasu. Bata kwantaba kuwa har wajen sha ɗaya da ƴan barka suka gama shigowa Tinene ta dawo gidan. Kallonta kawai Sa'a tai ta watsar, dan ko uffan batace mataba akan ina ta fito ko taje. Tunda dama zance nata yawo a gari Tinene na yawon dare, amma ko an faɗama Inna saita karyata tace anama Tinene sharrine dan ba'a ƙaunarta. Sai da taga Tinene ta kwanta sannan ta fito kamar zata bayi, ta Window ta leƙa ɗakin Inna taga duk sunyi barci ita da Karima da jaririya. Kanta tsaye wajen turmin sissikar hatsinsu da inna ta nunama hajja lanti ta nufa. dana tunda rana ta jiƙa wajen da ruwa dan ƙasar tayi laushi. Aiko an dace, dan tana ture turmin ta fara tona da fatanya a hankaki tana addu'a. Cikin sa'a ALLAH ya bata damar tone ƙasar sosai har takai ga abinda take buƙata. Wata ƙaramar kwanon tasa ta tono, jikinta har rawa yake ta ajiyesa gefe ta maida ƙasar wajen da ruwa ta rufe, ta ɗebo busashen ƙasa ta zuba sannan ta mauda turmin ta ɗauka tasar taje ta ɓoye akan sai da safe zatayi abinda ya dace. Daga haka ta koma ɗaki cike da danuwa da tashin hankali ta kwanta. Barci barawo shine kawai ya sace Sa'a a wannan dare amma bawai dan taji zata iya yinsaba. Kuka tasha sosai na tausayin ƴar uwarta Zinneerah da taji Inna tace wai tana Lagos yanzu tana zaman kanta. Wannan kalma ta tsaya mata a rai, itace kuma take ƙara rura wutar tashin hankalinta akan zancen fiye da komai.......... _________________★ *_LONDON_* Halin da Zinneerah take ciki na zazzaɓi ya hana sake tada wata magana a gidan. Duk da kuwa Hajiya Iya da taji komai akan ƙaddarar Zinneerah ita da Baffah dake anan Nigeria zukatansu basu hutaba da saƙawa da kwancewa akan little. Hakama AK duk da baisan komai game da Zinneerah ba shi nashi tunanin akan kamanninsa da little ɗin suka tsaya da kuma damuwar Farah. Dan yanason matarsa bai kuma son shigarta tashin hankali. Yaje can gidan domin lallashinta ya kuma fahimtar da ita gaskiyar zancen taƙi yarda su haɗu, saima kulle kanta datai a ɗaki. Duk lallaɓata da sukai shi da Mahma danya sanar mata komai itama amma fir Farah daketa kwasar kuka taƙi buɗewa. Sai ma jiyota sukai tanata fashe-fashen abubuwa tana tabbatar masa cewar ta tsanesa. bakuma zata sake zaman aure dashi ba yaje ya zauna da karuwar data haifa masa ɗan ita ta haƙura. Duk da kalamanta na masa zafi a rai haka ya dannesu yana cigaba da lallashinta daga inda suke tsaye a bakin ƙofa dan yasan tanada hujjar yin hakan. Sai dai matsalarta data kasa kwantar da hankalinta taji ta bakinsa sam saboda rashin man kanta. Duk yanda sukaso ta sauraresu taƙi, hakanne ya bama Mahma haushi tace yay tafiyarsa kawai. Idan ta gadama ta fasa gidan tunda ita batasan lallashi ba. Badan yaso ba ya baro gidan ya dawo gida. Koda ya shigo bai nema kowaba ɗakinsa ya shige kansa na sara masa na azabar ciwon da yake masa. Wanka yayo kozaiji sassauci, yana niyyar kwanciya kiran Baffah ya shigo masa. Batare da tunanin komaiba ya ɗaga suka gaisa. “Mike faruwa naji muryarka haka?”. Baffah ya faɗa daga can jin yanda AK ɗin ke magana da ƙyar. “Baffah kaina ke ciwo”. Ya bashi amsa murya a raunane. “ALLAH ya ƙara afuwa, sai ka daure kasha magani dan zama da ciwo babu daɗi. dama na kirakane muyi wata magana, amma tunda naji baka da lafiya mayi daga baya kasha magani ka kwanta”. “Babu damuwa Baffah muyi maganar kawai, dan sai anjima nakeson shan maganin yanzu lokacin salla ya kusa anan”. Ɗan jimm Baffah yayi daga can, dan shima dai maganar cin ransa take yafi buƙatar suyita yanzu ɗin ko zai samu sassauci a ransa. Ya sauke numfashi da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182