Chapter 165
Chapter 165
yarda yay wannan taɓargazarba. Ki yafemin na ƙara roƙonki......” Da sauri Zinneerah ta shiga girgiza mata kai, “Mammah dan ALLAH ki daina roƙona. Wlhy ni bakimin komaiba sai tarin alkairi kodan zama mahaifiya ga Yayanmu da kikayi. Kuma ni kallon uwa nake miki daman, har abada kuma zan cigaba da kallonki da wannan kimar da darajar. Dan haka ki ɗauka bakimin komaiba. Idanma kinmin na yafe miki wlhy”. Tasowa Mammah tayi ta rungume zinneerah tana saka mata albarka. Kamar yanda zancen nata ya saka kowa dake falon murmushi, duk da ƙarancin shekarunta ALLAH ya bata baiwar shirya lafuza masu taushi ga nagaba da ita duk da kuwa ko ba'a faɗa da gaske an tauye mata haƙinta. Farah da Zakiyya dai babu wanda ya roƙa gafarar Zinneerah, babu kuma wanda yace dasu ƙala akan hakan, kai kowama basu roƙaba sai kuka da sukeyi kawai. Dan haka mai martaba ya umarci AK da mijin Aunty Zakiyya da shima yana a wajen akan su basu saki. Babu wanda yace komai a falon, sai AK ne ya miƙa hannu ya amshi takarda da biro daga hanun Baba Wambai. Haka shima mijin aunty Zakiyya. Gani kawai sukai Zinneerah ta tashi da sauri taje gaban AK ta durƙusa. Biron daya dasa akan takardar ta riƙe da fashe masa da kuka tana girgiza kai. Jajayen idanunsa ya ɗago yana kallonta. “Yayanmu dan ALLAH karka aikata, na roƙeka karka saketa. Kuma koba hakaba ka tausaya mata ba laifinta bane itama tursata akayi”. Tai saurin juyawa ga mai martaba dake mata kallon mamaki hakama sauran jama'ar falon. “Abbah dan girmana ALLAH kayi haƙuri ka janye wannan hukuncin naka koda kuwa sauran zasu tabbata. Gara komi za'a musu ai musu da igiyar aurensu kar'a rabasu da iyalansu na roƙeka Abbah. Dan ALLAH kodan maraicinsu ai musu afuwa, wlhy na tsani naga an saki mace inajin ciwo. Granny, Baffah, Mahma, Babana dan ALLAH kusa baki, Abba dan ALLAH ku bama Abbah haƙuri dasu Yayanmu karsu aikata”. Yanda take kuka kamar ranta zai fita sai duk hankulansu suka tashi. Dan har suƙewa takeyi, ƙoƙarin son fisge pen ɗin AK yayi yana harararta ta sake damƙesa da fashe masa da kuka. “Yayanmu dan ALLAH, kodan ƙyautar little da ALLAH ya azurtaka da shi ka taimaka karkayi, idan ka saketa ALLAH nima bazan zauna da kai ba, zan ɗauke little na tafi inda bazaka sake ganinmuba wlhy”. Kansa dake sara masa ya dafe, da wannan damar ta samu amshe takardar da biron, ta koma gaban Mai martaba ta gurfana tana cigaba da roƙonsa shi da su baba wambai da su waziri. Sosai ta basu tausayi ta kuma sake birge kowa. dan haka hajiya iya tai ɗan murmushi da duban mai martaba ɗin da shi kansa yakejin wani irin ƙaunar Zinneerah na shigarsa. Dan koda ƴaƴansa suka kasance masu laifi bazaiso mutuwar aurensuba ai. Sai dai kuma dolene ya yanke musu hukunci domin yin gargaɗi. “Inaga a amsa kukan Zinneerah dan ALLAH, za'a iyama su Farah hukunci bawai sai an katsa igiyoyin aurensu ba, dan koda abinda duk ya faru aka barsu ya ishesu tunawa da ishara har ƙarshen rayuwa. Ayi haƙuri dan ALLAH”. Ƙasa kawai mai martaba yayi da kansa dan yana ganin girman tsohuwar ainun, yanda yayi ɗin ne ya saka sauran ƴan falonma fara roƙonsa harma dasu AK kansu. Ganin sun masa taron dangi ya sashi jan numfashi da dafa kan Zinneerah ya shiga jera mata addu'oi masu daraja da ake jifan mutum mai daraja dasu. Sai da ya gama ana amsawa da amin sannan yace, “Shikenan zan janye maganar saki, amma kuma dolene sai sunje masarauta sunyi wancan zaman wlhy, sauran hukuncin kuma tsakanina da sune. ALLAH yay miki albarka ke kuma, daga yau kema kin zama cikin jerin ƴaƴana”. Kabbara aka ɗauka a take. Kowa na nuna jin daɗinsa da farin ciki. Daga haka Hajiya iya tai musu nasiha. Hakama baba wambai yayi musu sannan shima maimartaba ya ɗaura tashi, daga ƙarshe aka rufe taro da addu'a saboda lokacin sallar zuhur yayi. ★★★ Ana idar da sallar azhar aka gabatar da ɗaurin auren Huzaifa da Adilah bisa alƙawarin Baffah, dan dama sun gama magana da mahaifin Huzaifa tun daren jiya, ya kumace ya bashi wuƙa da nama dan zaman Huzaifa hakan ya ishesa dama. Shima dan baya Nigeria ne da dashi za'ai komai a yau. Koda suka dawo cikin gida tuni labari yaje kunen kowa. Zokaga murna wajen ango da amarya dan dama sun folama juna tuni. Daga haka sukai zaman cin abincin da matan Baffah suka shirya musu, suka kuma sake tattaunawa a tsakaninsu na maza. Kamar yanda anan cikin gida suma su Granny basu gaji da sake tattauna zantukanba a tsakaninsu. Mahma taja su Zakiyya gefe tana musu faɗa akan ƙin neman gafarar kowa da sukayi. Ta zazzagesu tas tai gaba ta barsu batare da kowa ya sani ba. AK kam bayajin daɗin jikinsa, dauriya kawai yakeyi, hakama Zinneerah tana gadon Granny ƙudunsune dan zazzaɓi na neman dawo mata sabo ga ciwon kai na kukan data sha. Tanason zuwa ta gaisa da Baba ma ta kasa. Zuwa la'asar su maimartaba suka fara tafiya bayan ya tasa su Farah dake faman kuka gaba ya wuce dasu masarauta, harda Baba dan yanason ya shiga har ƙauyen Danya yayma baba rakkiya ya kuma gana da dagacin garin danya ta silar baba. Hakan yama Zinneerah data fito suka gaisa da ƙyar daɗi, yau ga babanta ga maimartaba wata hikima sai UBANGIJI. Shima kansa AK hakan da maimartaba yayi ya masa daɗi sosai. Bayan wucewarsu suma su mmn sadiq suka wuce, suma hajji Lanti tafiya sukai bayan sun sake gurfana neman gafara ga Zinneerah da AK dama su Hajiya iya baki ɗaya. Da wannan damar Mammah ta samu suka sake zama ita da Mahma dasu Baffah ta ƙara neman gafararsu da sake tattauna duk abinda ya faru. AK dai bai zaunaba ɗakinsa ma ya shige yay kwanciyarsa dan bayajin daɗi, ya tabbatar yau jininsa yayi ƙololuwar hawa tabbas. Hajiya iya ce ta hana su Mammah komawa gidan mijin Zakiyya. Tace Khalipha zaije ya ɗakko musu kayansu suyi zamansu anan har randa za'aje ga yarinyar datake rainon cikin a Morocco. Zinneerah ma dai magani Granny ta bata tasha ta kwanta. ________________________ *_DANYA_* Su baba sun iso danya da tawagar maimartaba. Inda tsabar ruɗewar da maigari yayi kai kace zai kife ƙasa. Maimartaba da kansa yau a ƙauyensa, bayan ko'a labari bai taɓa jin ko kusada wajen hakimi yaje ba sai dai ya aiko wakili idanma wani abune ya taso. Ai baima san ya gurfana yana kwasar gaisuwa ba. Hakama garin danya cikin ƙanƙanin lokaci labarin zuwan maimartaba da baba a tare ya shiga kunnen kowa harsu Inna da ke kwance rijib cikin ciwo. Dan tun zancen cikin Tinene dajin uwar sata da Karima ta kima na sarƙar zinarin wata hajiya da har yay silar Babawo yimata dukan mutuwa ya korota gida ta yanke jiki ta faɗi aketa fama har yanzun. Dan saki uku Babawo yayma Karima. Ga kuma aike daga kotu cewar Karima zata biya naira dubu ɗari huɗu na sarƙar mata bayan tara kuma da zaman kaso na wata shidda bayan ta yaye ɗiyarta. Ga zancen cikin Tinene ya baje ko ina na garin danya da kewaye har ƴammata sun dasa mata waƙar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182