Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

Chapter 32

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

faru, dan har ɗakin da aka kwantar da Zinneerah Dr Mahmud yaje yayma yaro huɗuba. Ya kuma ajiye kuɗi dubu hamsin shima yace asai rago a yankama takwaran abokinsa, kuma ogansa ranar suna. Shima sun masa godiya sosai, kowa na jinjinawa a ransa yaro yazo da farin jini. yayinda Maman Sakina keta taɓe baki a kaikaice, a ranta kuwa tana ganin tsabar iya asirine na ƴan ƙauye kuma Katsinawa da kullum take ambata ga maman Sadiq. Tare Alhaji suka fita da Dr Mahmud. Sai bayan kusan mintuna talatin ya dawo ɗauke da madaidaicin kwali da aka zubo masa magungunan da Doctor yace su sayo da drips, sai jini leda ɗaya. Kwalin Maman Sadiq ta amsa takai ɗakin dan sun fito waje. Tana fitowane yake faɗin, “Wani iko sai ALLAH, kunga jininma da naje nema a lab ɗin nasu saina samu bawan ALLAHn nan ya bada nasa a ajiye idan masu bukata sunzo nema. Cikin ikon ALLAH sai gashi ni na fara zuwa kuma. Gashi sun bada ƙyauta babu ko sule”. Cikin riƙe haɓa Maman Sakina da hassada kecin ranta tace, “Oh har jini yake zuwa ya badar a asibitin kuma? Dan tsabar jin daɗi irin na masu arziƙi”. Alhaji ya bata amsa da cewar, “Wlhy kin gani dai, dama likitan daya kira mani shi a waya yace jinin yazo badawa kawai shiyyasa bai jimaba ya tafi”. Sudai su Maman Sadiq godiya suka sakeyi da jera masa addu'oin gamawa da rayuwa lafiya. ★★★ Sai yamma Zinneerah ta farka sosai cikin hayyacinta, bayan an cire mata jinin da aka gama ƙara mata. Bayan likita ya shigo ya fita suma su Maman Sadiq suka shiga. Zaune suka isketa jingine da filo ta zubama yaron dake gefenta yana barci ido. A zahiri shi take kallo, amma idan ka nutsu kaima a kallonta zaka fahimci sam batama tare da duniyar mutane gaba ɗaya. Dan yaron kuka yake iya iyawarsa amma da alama ba jinsa takeba. Matar Naziru ce tasa hannu ta ɗauki yaron tana faɗin, “Haba Zinneerah, yaro na kuka ke kuma kin tsaya kallonsa kawai”. Nan ɗinma ba jinta tai ba. Sai da Maman Halima ta taɓata sannan ta kawo numfashi. “Oh ni Binta, mi kike tunani haka Zinneerah?”. Maman Halima ta faɗa tana tsatstsareta da idanu. Ƙasa kawai Zinneerah tai da kanta tana ƙoƙarin haɗiye kukan daya tokare mata ƙirji tun ɗazun. Matar Naziru dake jijjiga yaron dai yay shiru tace, “Haba Zinneerah ai yanzu ba lokacin kuka bane, lokacibe da zamu taru mugodema ALLAH ne. Jiya iyanzu muna nan cikin tsananin tashin hankali da fargabar rasaki, amma cikin amincin UBANGIJI yau gaki zaune da ƙyauta mai girma da wasu kecan suna bulayin nema da kuɗi amma ALLAH bai ƙaddara samuwarta garesuba. Kiyi haƙuri kibar kukan nan, mu yanzu babban fatanmu kuma ALLAH ya baki lafiya mu koma gida”. “Maganarki kam gaskiyace Maman Abu. Zinneerah yanzu lokacine na godiya ga ALLAH kinji. ALLAH ya ƙara miki lafiya. Kinga yaron nanma ya kamata a bashi abincinsa dan wannan kukan bana komai bane sai na yunwa, tunda likita yace zaki iya ɗan gwada bashi yanzu sai a gwada ɗin ai ko”. Sake fashewa da kuka Zinneerah tayi, dan ita kaɗai tasan yanda takeji a ranta akan wannan al'amari mai rikitarwa da matuƙar ruɗani. Tunda take bata taɓajin labari irin nataba. Tayaya zaka haifi ɗa na mutum batare da kasan yanda ka samu cikinsa ba. Anya kuwa yaron nan baɗan wani aljanin baneba?...... Shigowar Alhaji da Maman Sadiq da gayyar yaran gidan gaba ɗaya har da ƴaƴan Maman Sakina ya katse mata tunani. A take kuma ɗakin ya kaure da hayaniyar yaran. Dan bayan sun mata yaya jiki gaba ɗaya hankalinsu suka maida ga ɗan jinjirin suna yaba ƙyawun da ALLAH yay masa. Sai da Maman Halima taga kukansa na ƙara ƙarfine ta amsheshi cikin tilastawa suka saka Zinneerah bashi abincinsa tanata kuka. Alhaji da Maman Sadiq ne kawai suka iya fahimtar kukan Zinneerah saboda sune sukasan labarin tushen samuwar yaron. Dan ita kanta maman Sadiq konawarsu gida tasha kuka, a yanzu hakanma kukan zuci takeyi. Su Maman Halima kuwa da basusan dawan garinba sai tunaninsu ke basu Zinneerah tana kukane saboda tunawa da mahaifin yaron da akace rasuwa yayi. Da ƙyar aka samu ta bari yaɗan kama na wasu mintuna. Dan kuka take sosai tana yarfa hannu wai zafi. Maman Halima ta ɗaukesa tana mata faɗa akan karta sakama ranta fargabar tsotso dan yaron nan daga gani ba wasa zaiyi da cikinsaba. Ita dai Zinneerah zamewa ma tai ta kwanta a hankali tana matse baki dan inda aka yankata na mata ciwo sosai har yanzun. Sun daɗe a asibitin yaran na cigaba da jagwalgwala yaron da aka samu yay shiru, yayinda Zinneerah ke kwance shiru bata sake kula kowa ba. Idonta a lumshe suke tana zirar da hawaye ta gefensu, yayinda hancinta ke shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren dake manne da jikin showal ɗin yaron da batan a ina ya kwasoshi ba. Ƴar hayaniyar yarance ta saka Doctor shigowa ɗakin yace suyi haƙuri a barta ta huta hakanan, ya kuma bada damar a bata abu mara nauyi tasha, kamar shayi ko kunu haka. Godiya sukai masa ya fice. Alhaji kuma ya tattara iyalansa shima sukai musu sai da safe suka tafi. Aka barta daga ita sai Maman Halina dake haɗa mata kunun da akace zata iya sha ɗin. _____________★ Haka Zinneerah ta cigaba da jiyya a asibiti. yayinda abokan arziƙin Maman Sadiq na anguwa da dangi ɗai-ɗai dake anan suke ɗan shigowa dubata. Kulawa da take samu na abinci ya saka komai yake tafiya kan tsari Alhmdllh. Dan jikinta yayi ƙyau sosai a kwanki shidan data ɗauka a asibitin. Idanma ba'a faɗa makaba bazaka taɓa ɗauka cs akai mataba. Sai dai sam babu mai ganin walwalarta, sannan ko kallo yaron bai ishetaba sai Maman Halima ta mata jan ido. Matsalar da suke fuskanta da yaron kawai shine idan yasha nono cikinsa sai ya kumbura yayta kuka. Da farko basu fahimci hakanba sai suke ɗauka cibiyarsa ne ke ciwon. Sai daga baya Doctor ya gane inda matsalar take. Dan haka ya dakatar da Zinneerah daga bama yaron nonon gudun kar a cutar da yaron kuma. Sai dai sun ɗorata akan magani zuwa wani lokaci sai ta cigaba da shayar da shi. shi kuma yaron suka bada shawarar a ringa bashi madara. Hakan yama Zinneerah daɗi, dan a shirementa ayyanawa take a ranta ta huta da ciyar da ɗan aljanu, dan har cikin ranta ta yarda aljanune sukai mata ajiyar yaron kawai a cikinta. Babu wanda yasan da wannan shirmen nata, sai dai ranar tsabar jin daɗi har ɗan sakin jikinta tai sukai hira da Maman halima da ada take danganta rashin walwalar Zinneerah ɗin da rashin ƙarfin jiki. Washe gari Alhaji ya sayi raguna biyu aka raɗama yaro suna Abdul-Mutallaf a masallaci, wato dai takwaran AK Shira kenan kamar yanda akai masa huɗuba. Ba ayi wani shagaliba kasancewar mai jego na asibiti, sai dai maman Sadiq tayi abinci ta bada sadaka ko zata samu sassauci a ranta da nutsuwar rugumar wannan ƙaddara a garesu. Da yamma da sukazo dubasu a asibiti Alhaji yake sanarma Maman Halima cewar yaro yaci suna Abdul-Mutallaf. Cike da murnarta da farinciki taita jera addu'a ga jariri tana tsokanarsa. Zinneerah kam ko motsi

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182