Chapter 37
Chapter 37
ke duƙe a ƙasa alamar kuka take little. “Ki tashi ki masa wanka a bashi abinci tunda yayi shiru”. Sai lokacin Zinneerah ta ɗago tana share hawayenta. Ta amshi little ɗin kafin ta gaida Maryama. Amsa mata tai tana binta da kallo, hakan yasa Zinneerah miƙewa ta shige ɗaki da Little a hannu. Ajiyar zuciya Maryama ta sauke bayan shigewar Zinneerah ɗin, duk maman sadiq dake ƙoƙarin kawo mata ruwa na kallonsu. Sai da ta ajiye ruwanne ta sake maimaita mata tambayar ɗazun. Maryama tace, “Lafiya ƙalau, sai dai lafiyar mai rauni. Inno ce jikin nata babu daɗi, dan sunce shekaran jiya da daddare kamarma bazata kwana duniya ba”. “Innalillahi wa'inna ilairraji'un. Yanzu nan har jikin Inno yakai tsanani haka amma baza'a sanarminba Maryama, har ke dake a Minna kiji”. “Kiyi haƙuri Yaya Hauwa, wlhy ba laifinsu bane. Buba yace tunda ciwonta ya fara motsawa a cikin satin nan suke neman wayarki data Yaya amma basa samunku. Ni kaina Baban su Atiku suka samu tunda kinsan dai ba wani muhimmanci wayata kedashi ba”. “Eh kuma sun fini gaskiya, dan layin nawane ya samu matsala wlhy, Yaya kuwa bansan yaya akai suka gaza samun nasaba, kokuma matsalar network ne. UBANGIJI ALLAH ya ƙara mata lafiya. Jikine na tsufa sai dai Alhmdllh”. “Wlhy jiki kam na tsufa. Dama na biyo ne idan babu matsala sai mu wuce Baucin tare mu dubata, to saima ina shirin tahowa danai waya da Buba yake sanarmin ai Hajiya Iya taje garin taga halin da take ciki ta ɗakkota suna anan kano wajenta”. “Tofa, ita Hajiya Iya ɗin dama suna anan kano ɗin har yanzu?”. “A'a yaya yakike wannan magana haka. Handa Hajiya Iya da iyalanta sukai ƙarfi a garin nan kina ganin zasu iya barinsa kuwa? Kenan baki cikama Inno alƙawarin da kikai mata na neman inda suke ɗinba?”. “Humm Maryama bazaki ganeba. Ni wlhy kin ganni nan harka da masu kuɗin nan ba sonta nakeba sam. Bani ƙaunar shiga inda akafi ƙarfina a wulaƙantani”. “Kai Yaya kenan har kin sani dariya. Aiko kinga Hajiya Iya bata da wannan, mace ce maison zuminci sosai. Danni kinga mun taɓa haɗuwa da ita kusan sau biyu kuma duk banga wani nuna ƙyama daga garetaba. Saima jana da taitayi a jiki tana min faɗa da cewar Baba ya rabamu da dangi bamusan kowaba sai Inno”. “To kinsan abinne da wuya wlhy Maryama. ALLAH ya ƙaddara bazanje ɗinba sai ta silar zuwan Inno ɗin. Dan yanzu hakama ni nama manta yanda adireshin gidan yake”. “Wannan mai sauƙine ai Yaya sai a kira Baban su Atiku ya kira Buba muji. Nidai na kasa haƙuri, dan ALLAH wai wacece wannan mai kamanni damu haka? Inaji a raina jininmuce yarinyarnan”. Murmushi Maman Sadiq tai tana mata harar wasa. “Rashin haƙurinki na nan dai Maryama. to ƴarki ce ta Danya ƙaddarar rayuwa ta kawota nan”. Da matuƙar mamaki Maryama tace, “Wai Yaya kina nufin Zinneerah?”. Kai kawai Mama ta gyaɗa mata tana amsa sallanar Maman Halima. Shigowar Maman Haliman ta saka Maryama yin shiru, Maman Halima ta ajiye mata kular abinci tare da zama suka gaisa cikin mutunta juna da tambayar lafiyar iyalai. ta mike zata fita Maman Sadiq ke sanar mata dalilin zuwan Maryama ɗin. Jajanta musu Maman Halima tai cike da alhini, tare da addu'ar samun lafiya ga Inno ɗin kakarsu data haifi mahaifiyarsu. Bayan sun mata godiya ta fice. Maman sadiq kuma ta ƙwalama Zinneerah kira. Koda Zinneerah ta fito sai Maryama dake sharar hawaye ta miƙa mata hannu tana faɗin, “Zonan ɗiyata dan ALLAH, zo naji ɗuminki”. Babu musu Zinneerah ta nufeta duk da batasan wacece itaɗin ba. Sai dai kamaninta da mahaifiyarta ya tabbatar mata jininta ce. Haɗata tai ita da Little da yasha wanka duk ta rungume kukanta na ƙara ƙarfi. Maman sadiq ta miƙe tana ƴar dariyar ƙarfin hali da faɗin. “Oh halin naki dai bai canzuwa kenan har sai ƴar taki ta ganoki itama. Nikam bara kiga na miƙe, kema idan kin gama kukan kizo kiyi sallar la'asar kiɗan watsa ruwa sai ki zaman cin abincin ƙyafi jin daɗi”. “Yaya dole nai kuka kodan kunya da takaicin kammu akan yarinyarnan. Zinneerah ki gafarcemu dan ALLAH, munsan bamu ƙyauta mikiba, bamuyi miki adalciba a rayuwa. Dan ALLAH ki mana afuwa”. Zinneerah bata iya cewa komaiba. Sai murmushi kawai da take famanyi da ƙoƙarin danne nata kukan dake neman kufcewa. Sai da Maman Sadiq data sake fitowa mata maganar tazo tai wankan ne ta lallaɓeta da ƙyar ta share hawayenta da sakin Zinneerah da itama zuwa yanzun hawayen take sharewa. ★★★ Bayan Gwaggo Maryama tayi wanka da salla sukai zaman cin abincin zuminci da ƴar uwarta. Yayinda little kenan tare dasu a falo nata wasansa konace ɓarna. Zinneerah kam tuni ta shige ɗaki dan zazzaɓi nema ke neman rufe mata jiki. Gwaggo Maryama ƙanwa ce ga Maman Sadiq. Uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Sukaɗai mahaifiyarsu ta haifa a duniya ALLAH yay mata rasuwa, dan haka akwai shaƙuwa mai ƙarfi da ƙaunar juna tsakaninta da ƴar uwartata wadda ƙaddarar aure takai can Minna jihar Niger. A yanzu haka itama ta zuba iyalai acan Alhmdllh. Kaf labarin Zinneerah da dalilin zuwanta nan wajensu da samuwar Little Maman Sadiq sai da ta zayyanema ƴar uwarta dakeshan kukan tausayin Zinneerah har cikin ranta. Tare da ɗaukar dukan laifi ta ɗora akansu suda sukai wasarere da lamarin Zinneerah ɗin bayan sunsan rashin imani irin na Asabe. Tunda har ta iya rabo Maman Sadiq da mijinta itama Zinneerah ɗin ba barinta zataiba. Murmushi mama tayi, cikin son kwantarma da ƴar uwarta hankali ta shiga nuna mata komai ƙaddara ne. Tunda UBANGIJI ya hukunta sai Zinneerah tai irin wannan rayuwar babu wani daya isa hana hakan a cikinsu ai. Sai dai su cigaba da mata fatan alkairi kuma a rayiwarta ta gaba. Wannan kam ta rigada ta faru kuma. “Hakane Yaya Hauwa. Amma wannan tabon bazai taɓa goguwa a zuciyar yarinyarnanba dangane da watsi da mukai da ita bayan duk munsan a inda take”. “To yadai wuce yanzu dan ALLAH. Muci abinci koma kimtsa kafin Yaya ya shigo gidan muji yanda za'ai tafiya inda Inno take. Dan da san samune mu tafi yau duk da naga garinma dai yana haɗe fuska alamar hadari”. Da wannan maganar ta Maman Sadiq bakin Gwaggo Maryama yayi shiru. Suka ƙarasa cin abincin da saida ta matsa mata. Daga haka suka zauna zaman hirar zuminci da jiran dawowar Abba gidan. Kamar yanda su Maman Sadiq ke jiran dawowar Abba iyalan Maman Sakina ma zaman jiran dawowar tasa gidan suke cike da alwashin sai Zinneerah tabar gidan yau ɗin nan. Duk da sun shige ɗaki basubar zage-zage ba da aibanta Maman Sadiq da Maman Halima. Dan ko abincin rana yau sunƙi zuwa su ɗakko na ɗakinsu har yamma tayi yara suka dawo daga makarantar islamiyya. Tunda su Abdull sukaga Gwaggo Maryama suka rikice da murna sosai. Itama taji daɗin ganinsu. Ta haɗasu a jikinta ta rungume harda Little daketa walwalar ganinsu. Bayan an idar da Sallar Magriba Sadiq yazo yana sanarma Mama Auntynsu bata da lafiya. Kafin tace wani abu sallamar Abba ta shigo kunnuwansu alamar ya dawo gidan kenan. Duk da suna a cikin ɗaki ba kuma nan ya shigoba kai tsaye sai da suka amsa. Su Sadiq duk suka fice
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182