Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

masa ragamar rayuwarta batare da jin ko ɗarba garesa. ★★★ Bayan sati ɗaya dayin wannan magana Alhaji ya shirya zuwa Kusada ƙauyen Danya batare da sanin Zinneerah ba. Kasancewar a ranar yaje ya dawo kuma bata san komai akaiba tunda tasan yana fita kasuwa dama. Abinda dai kawai ta fahimta ranar Mamansu ta kwana cikin wani irin yanayi na tsantsar baƙin ciki. Dan harta kai washe gari ma sai da aka kwantar da ita asibiti. Kwananta ɗaya aka sallamota ta dawo gida. Zinneerah ta shiga damuwa da ganin yanayin na mamansu daya kaita ga kwanciya asibitin. Amma sai rashin wayo ya hanata tambaya koda suka dawo. Kallo ɗaya zakai mata itama dai ka fahimci tana cikin damuwar. Kusan kwanaki goma tana ganin Maman tasu a wannan bahagon yanayin, kafin kuma taga ta warware ta cigaba da harkokinta a gidan cike da ƙarfin hali. Abinda Zinneerah bata saniba shine mummunan labarin da Alhaji yaje ya samo a garinsune yakai ga mahaifiyarta kwantawa asibiti saboda motsawar hawan jininta. Sai dai kamar yanda Alhaji ya gargaɗeta yin gum da bakinta kar Zinneerah da abokan zamanta susan wani abu game da cikin Zinneerah ɗin yasata shanye komai a rai ta fawwalama UBANGIJI ikonsa da amsar ƙaddara. Musamman daya kasance duk wanda Alhaji ya jiyo labarin cikin Zinneerah a bakinsa saida ya yabi kyawawan halayyarta da wahalar data dinga sha ga matar ubanta. Harma takai wasu na ganin Inna ce silar komai akan cikin na Zinneerahn. Hakan yaɗan sake girmama danganarta ta shanye komai ko a fuska basu taɓa nuna Zinneerah sunsan komaiba daga ita har Alhaji. matan gidan kuma sun sanar musu cewar ashe mijin Zinneerah ɗinne ya mutu kawai, ruɗanin rasuwarne ya sata baro gida cikin gushewar hankali. Maman halima ta tausaya mata, Maman Sakina kuwa ko'a jikinta. saima ƙorafi data dingayi akan kenan an ƙara ma mijin nasu nauyi tunda dai nan Zinneerah zata cigaba da zama ita da abinda zata haifa. Babu wanda yabi takanta dan idan da sabo kowa ya rigada ya saba da halinta a gidan ai. Zinneerah ta cigaba da rainon cikinta aɗan tsakanin nan cikin rashin jin daɗin jiki, dan tunda ya shiga wata na tara komai ya sake mata wahala. Harma takai randa suka koma asibiti dole Doctor ɗin ya riƙeta akan zata cigaba da zama anan har saita haihu. Hakan baima Zinneerah daɗiba. Amma yaya zatiyi tunda ance wannan ne samun sauƙi a gareta. Yanzunma dai Maman Halima ce tare da ita, sai Mamanta dakanzo duk bayan kwana biyu ta amsheta ita kuma taje gida ta huta. Abba kam babu fashi kullum sai yazo safe da dare dubata. Ko'a fuska bai taɓa nuna ƙyamar cikin jikintaba balle bakinsa ya suɓuta wajen faɗama matansa dalilin samuwarsa. A randa ta cika kwana tara a sibitinne da Naziru yazo dubata yake faɗa mata kwana biyu bayajin Khalipha kwata-kwata. Yayi ƙuru ya gwada kiransa ranar kuma bata shigaba. ya tura masa saƙo babu reply har yanzun. Murmushi kawai Zinneerah tai na ƙarfin hali batare da tace komaiba. Hakan yasa shima bai sake cewa komaiba akan batun. Washe gari data cika kwana goma cif a asibitin jikinta ya ƙwaɓe ta fara zubar jini (bleeding). Hankalin likitocin ya tashi harma da su Maman Sadiq dan sun fahimci naƙudace tazo mata a bahagon yanayi. Tun suna ganin zata iya haihuwa da kanta har al'amarin yasoyin tsamari suka yanke shawarar mata cs kawai. Babu wani ja'inja Abba ya saka hannu matsayinsa na uba gareta. Daga haka suka shiga da ita ɗakin theatre su kuma suka koma gefe suna mata addu'ar rabuwa lafiya da abinda ke a cikin nata. Awa kusan uku Doctor Mansura ta fito fuskarta da murmushi. Duk miƙewa sukai suna mai sauke ajiyar zuciya ganinta a yanayi mai daɗi. Ta sake faɗaɗa murmushin da faɗin, “Alhmdllhi, an ciro baby boy ƙyaƙyƙyawan gaske, mai kuma lafiya insha ALLAH”. Basu gaza wajen ambaton Alhmdllh ɗinba suma, dan sunyi imani akan duk abinda kaga UBANGIJI ya jarabceka da samu ta hanyar da kai baka buƙatarsa ya fika sanin dalilin yin hakan. Basu isa canja ƙaddarar Zinneerah ba komai son hakan da zasuyi, sai dai su tayata da addu'ar ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Duk da har cikin ransu suna tsananin tausayin uwar da ɗan. Abbane yace, “Yaya jikin ita Zinneerah ɗin kuma?” “A Alhmdllh Alhaji. Itama dai insha ALLAH komai zai dai-daita zuwa nan gaba kaɗan. Kuyi haƙuri sai zuwa anjima zaku samu ganinsu koma da safe”. Godiya sukai mata. Ta wuce su kuma suka koma suka zauna kowa da abinda yake saƙawa a ransa. ★★★ Kamar yanda likita Mansura ta faɗa basu sami ganin Zinneerah ba a ranar dai kam, sai dai zuwa yamma an fiddo musu da jariri ƙaton gaske kuma ƙyaƙyƙyawa kamar yanda Dr Mansura ta faɗa ɗazun. Abba ne ya fara amsarsa yana mai yin godiya ga ALLAH tare da jin tausayin yaron da baisan wanene shiba. Bayan ya masa addu'a ya miƙama Maman Halima daketa faman washe baki. Tace, “Masha ALLAHU mijin nawa kam dai-dai ni. ALLAH ya rayaka ya albarkaci rayuwarka. Ya jiƙan mahaifinka kaji”. Da amin suka amsa. Kafin ta miƙama Maman Sadiq dake kukan zuci. Bata musaba ta amsa itama ranta fal tausayin yaron dabaijiba bai ganiba. Ta ƙura masa idanu na tsahon lokaci zuciyarta na suya akan samuwarsa ta hanyar da ba ita sukai fataba. Sai dai a gefen zuciyarta na gargaɗinta da ambaton Alhmdllh. Dan babu maima UBANGIJI dole akan abinda yaso. Babu kuma mai sakashi saɓanin hakan. Itama dai addu'ar tai masa tamkar kowa ta sake miƙama Maman Halima dake kusa da ita. Ita kuma ta miƙama Matar Naziru. Bayan sun gama ganinsa da masa addu'a Nurse Salima tazo ta amshesa tana faɗin, “To waye zai zauna a wajenta? Dan an kaita ɗakin hutu yanzu haka. Sai dai likita tace wadda zata zauna da ita kawai za'a kai sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zaku ganta”. Dukansu sun gamsu da hakan, kafinma kowa yay magana Maman Halima tace ai bama sai anja zanceba itace zata cigaba da zama da ɗiyarta. Wannan karamcin na Maman Halima kesa Maman Sadiq jin daɗi sosai da sake ganin girmanta da kimarta a koda yaushe, dan mace ce data cancanci girmamawa kodan ƙyawawan halayenta. Sallama tai musu tabi bayan Nurse Salima. Su kuma suka fito domin komawa gida. ★★ Koda suka shigo gidan Maman Sakina batako leƙoba balle ta tambayesu yaya jikin Zinneerah ɗin tunda batabisu asibitinba. Duk da kuwa sanda Matar Nasiru tazo ta sanar musu ruɗewar jikin Zinneerah ɗin itama tana zaune a tsakar gidan. Amma taƙi bin Maman Sadiq. Bayan tafiyarta kuma bata kira waya taji halin da ake cikiba. Gashi yanzu sun dawo bataleƙo tajinba kuma. Hakan bai dami Maman Sadiq ba. Dan halin da take ciki ya wuce na matsalar Saude a yanzun. Tana shiga ɗaki fashewa tai da kuka, kamar Alhaji yasan za'ai haka ya biyo bayanta kuwa. Ganinta tsaye gaban mirror kanta a ƙasa tana shashshekar kuka ya sashi ƙarasowa cikin ɗakin sosai. “Haba Hauwa'u, minene kuma abin kuka anan dan ALLAH? Kenan bazaki iya karɓar ƙaddaraba? Ki tuna UBANGIJI ya fimu sanin abinda ke a ɓoye. Sannan yarinyar-nan mutane da yawa sun shaideta akan ba yarinyar banza bace. Kowa na ƙyautata mata zaton cewar tsautsayine kawai da ƙaddara

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182