Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 154

Chapter 154

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

al'amarin Khalipha ya shigo gidan, shine ya musu ƙarin bayani akan kamo hajiya lanti da sukai a yanzu haka kuma tana hannun hukuma, Alhmdllh kuma ta bada haɗin kai akan cewar zata sadasu da hajiyar data kaima su Zinneerah dan itama saboda ita taje katsina. Amma sai ta tarar tana saudia dan can ta koma da zama. dama can sana'arta kai yara saudia aikatau, duniyace tai mata gwatson ƙyanwa tunda aka cimimiyota ta dawo kuɗin komawa ya gagareta. To yanzu dai Alhmdllh akwai bikin yaronta da akai a wannan satin rana ɗayama da nasu Zinneerah, itama jira take a gama bikin dama ta sameta dan tazo Nigeria. Sunji daɗin jin hakan, a take suka yanke zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu itama a damƙota kawai kafin ta sake tafiya, suma kuma su Mammah karsu bar ƙasar. A wannan tattaunawar AK da yazo gidan gaishesu ya samesu. Zama yay suka ɗan ƙara tattauna zancen sannan ya shiga ya gaida matan gidan. Daga haka ya ɗauka little daya maƙale masa suka wuce gida dan sai da ya fara zuwa ya gaishe dasu Mammah. Acan ɗinma bai nuna musu komaiba, dan koda Farah tace zata koma gida gobe a taƙaice yace mata, “Ƙofa abuɗe take” daga haka yaja bakinsa ya tsuke. Bai kuma bi takantaba harya baro gidan. Aunty Zakiyya kam bata tanka masaba shima bai tanka mataba dan idan taurin kai ne gidan ta taras. ______________________ *_DANYA_* Ƴan biki sun dawo gida lafiya, yayinda kowa ya fara ƙoƙarin fesar da maganar daya gumtso akan auren na Zinneerah da daular duniyar da ALLAH ya kaita ciki. Ga miji ɗan gaske acewarsu (🤣ba bily ba😂). Wasuma da biyu suke ƙara kambama zancen dan baƙanta ran Inna data haukace musu da bala'in su fice mata a gida. Ko'a jikinsu, dan da suka fitanma gaba suka ƙara wajen isar da labarai kala-kala harda waɗanda ba'ayiba ma. Gasu Yaya Gajeje kuwa ga labarin a ransu ga tsoron tunkarar Inna da batun abinda suke hasashe tattare da Tinene, dan tunda suka shigo gidan ɗaki ta shige ta ƙudundune a zani tana rawar sanyi. Da ƙyar Yaya Gajeje taja ƙafafunta ta nufi gidan saboda yara data bari, gashi yamma nayi tunda tana ƙauyen gaba dasune duk da babu nisa. Duk da takaici da zafin da inna keji a ranta da labarin ɗaukakar da Zinneerah ta samu hakan bai hanata zaman jin labari a bakinsu Atine dakeyi suna gatsine-gatsine ba kishi fal ransu. Abinda kuma sukazo dashi sai faman ci suke har Inna ɗin dan tace raba mugu da makami ibada ne.. (😂🤣gaskiya kam aunty Asabe) Shi Baba ma da amaryarsa dake jiyosu daga ƙofar ɗaki dariya suka basu, musamman Inna da baba yasan shegen kwaɗayinta bazai barta ta kasa cin abinda akazo da shi dinba koda kuwa tanaci tana kuka ne. Washe gari da safe jikin Tinene ya ƙara tsananta, tun dare taketa kwara amai har safiya ta tashi a galabaice. Baba ya ce ta shirya suje asibi maybe dai typhoid ne ke damunta, dan itace kesa zazzaɓi mai zafi haka da naci. Amaryar baba ba sanin ciki tai ba sosai, Inna kuma idanunta ya rufe da damuwar ɗaukakar Zinneerah sam taƙi fahimtar halin da Tinene ke ciki. Su kuma su Karima tsoron faɗar abinda ransu ke raya musu inna ta hau tsinarsu sukeyi. Ana haka sai ga Gwaggo Laritu tazo domin ai zaman raba alkairin da AK ya basu, bata jima da zama ba Yaya Gajeje ta iso itama. Cikinsu babu wanda yay magana akan shirin kai Tinene asibiti da baba ke shirin yi. Sai da Gwaggo Laritu tai wani tunani sannan tai magana. “Niko Yaya nakega kai Tinene asibiti bazai jawo komai a garin nanba sai kace nace. Musamman ma daya kasance asibitin garin nan zakuje”. Da mamaki baba yace, “Kace nace kuma Laritu, akan ciwon?”. “Tabbas kuwa Yaya, dan banga amfanin aita ɓoye-ɓoye ba akan abinda kowa yasan dama wajib ne. Dan shi dai sharri ɗan aike ne dama shiyyasa ake nusar damu illarsa ga aikama kowa. Asabe tama Zinneerah fata kuma ALLAH ya karɓa mata, sai dai kuma ga sakamakon nan ya dawo ga Tinene. Dan babu wani taifot dake damunta ciki ne jikin wannan yarinyar wlhy”. Ba baba da amaryarsaba hatta da Inna dake jiran Gwaggo Laritu takai ƙarshe ta sauke mata kwandunan bala'in da take Tattarowa a take ta saki robar ruwan wankan ƴar Karima data ɗauka zata sako ruwan zafi, ALLAH yasotama bata kai ga zubawarba. Wani irin shuuu taji abu ya gitta mata cikin idanu da ƙwaƙwalwa saboda tsabar razani. Cikin rawar baki tace, “Munahika annamimiya, Laritu kirasa wanda zakima wannan sherin sai ɗiyar zumunki. To wlhy sai dai kiga ciki a jikin jikokinki, ALLAH ya isa kuma sherin da kikaima yarinyata”. Murmushi kawai Gwaggo Laritu tayi. amma uffan bata sake cewa ba. sai Yaya Gajeje ce tace, “Inna ya kamata ki fahimci zancen Gwaggo, ku kuma nutsu wajen karantar Tinene wlhy cikine da yarinyar nan da gaske”. Baki sake tabi Gajeje da kallo, sai jitai Atine tace, “Wlhy Inna da gaske ne, ki kalla Tinene da ƙyau zaki tabbatar”. Tsitt gidan yayi saboda kakarin aman Tinene, Inna ta fashe da kuka jikinta na wani irin rawa lokacin da idonta ya sauka akan Tinene da har ciki ya fara tasawa sama kaɗan, da alama ma ya wuce watannin da suke hasashensa. Baba kansa baya yay sai da amaryarsa ta riƙosa jikinta na rawa itama dan batason damuwa sam, musamman ma yanzu data samu cikin nan. Kafin wani ya samu damar sake cewa uffan sukaji ana rangaɗa sallama daga waje. Da ƙyar baba ya iya amsawa da nufar hanyar ƙofar gidan domin duba wanene. Da Laminu ƙanin Babawo yaci karo, Laminu ya gaishesa da girmamawa yana miƙa masa takardar hannunsa da nuna masa kayan daya sauke a mashin ƙasa. “Baba Sule gashi inji Yayana Babawo, yace a bama Karima tare da waɗan nan kayan. Yace a sanar mata ta tuna yau saura sati biyu wa'adin da kotu ta bata na kai kuɗin sarƙar hajiyar data satamawa ya cika”. Cikin rashin fahimta baba yace, “Laminu ban fahimcekaba nikam sam, amma kaga shigo daga ciki kai bayani agaban Karimar”. Babu musu kuwa yabi baba ciki, bayanin daya zayyana masa shiya sake maimaitawa Karima. Gani kawai sukai ta saki ƴar sai da Atine tai azamar tarota tana ambaton, “Na shiga uku Karima baki da hankaline?”. Ina Karima ba saurarenta takeba, dan atakema gani sukai ta yanke jiki ta faɗi, Inna ma da tun fara bayanin garin ke juya mata da wata irin hajijiya sai tabi bayan Karima ta zube ƙasa. Ƙarar da Atine da Sa'a suka ƙwalla na firgici ya saka amaryar baba dafe bango saboda wani irin murɗawa da mararta tayi alamar tahowar naƙuda......... ____________________ *_KANO_* Bayan wucewar su mmn Halima salla kawai Zinneerah ta samu tayi ta la'asar. Duk yanda taso daurewa da zazzaɓin daya rufeta kasawa tai, dole ta rrrafa saman gado ta kwanta dajan bargo ta lulluɓe tana rawar ɗari. Cikin barcin daya ɗan fara figarta little ya faɗo mata a jiki yana faɗin, “Aunty!” cike da farin cikin ganinta. Buɗe idanu tayi da ƙyar tana kallon ƙyaƙyƙyawar fuskar yaron mai tsananin kama da mahaifinsa. Ta ɗan lumshe ta buɗe da ciro hannunta a bargon da ƙyar ta shafa kansa. “Kaga

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182