Chapter 144
Chapter 144
Zinneerah duk da itama fa a tsoracen take. Amma yanda su Jamal suka dafe ƙeya dasu Bahijja ya bata matuƙar dariya. Khalipha da shima dariyar yake dannewa tana kufcewa ya afka mota yana faɗin, “Mu kwana lafiya Yayanmu”. Kai kawai ya jinjina masa tashi fuskar babu ko ɗigon murmushi ammafa a ransa dariya yake ɗan rainin wayon😂. Dan duk dauriyarka dolene abinda su Meenal sukai ya baka dariya. Maigadi kansa dariya yakeyi dan har bangajesa sukai wajen gudu. Ganin Khalipha zai wuce Zinneerah ta shirya nata gudun itama amma tana ɗaga ƙafa zata fece taji an cafko mata hannu. Gaba ɗaya ta rikice, dariyar data rage a saman fuskarta ta ɓace ɓat. Baya ya dawo da ita gabansa yana kallonta da birkitattun idanunsa dake neman sakata sakin fitsari dan fuskar ta kuma tsukewa tamau. Shi dai Khalipha motarsa ya harba yana dariyar ƙeta, dan yasan dai Bahijja ta kunno wuta. Kuma gaskiya ta faɗa indai soyayya ce kam Yah Abdul-Mutallab ba'a magana, shi da yake rayuwa a gidansu yake shan kallo. Cikin tsagwaron marairaicewa Zinneerah da idanunta ke tara ƙwalla tace, “Yayanmu wlhy bance komaiba, ALLAH Bahijja ce ka tambayi Yah Khalipha kuma. Uffan baice mataba, sai jawota da yay a hankali ta faɗa saman jikinsa, rawa jikinta ya fara, batare da yabi takanta ba ya ɗauketa cak a bazata. Babu shiri ta cusa kanta a ƙirjinsa dason sauka amma tama kasa motsawa. Koda suka iso ƙofar falon da ƙafa ya tura, hakama da sukaje ta sashensa da ƙafa ya tura, duk yanda take zame-zame bai direta a ko inaba sai falonsa. Tanajin ya ajiyeta ta ɗago fuskarta daga jikinsa dajan jikinta dake ɓarin tsoro baya dan catake ko duka zataci, duk da dai bata taɓaji a tarihi ko labarinsa ya taɓa dukan kowaba a gidan nasu, barsa dai da barazana da mazurai, hana rantsuwa marin da yayma matarsa a london sanda ta shaƙeta, shima ba wani lura tai da ƙyauba ranar dan a firgice take sai da su Meenal suka bata labari. Baya ta dinga ja tana girgiza kanta. “Yayanmu ALLAH bance komaiba, ka tambayi Yah Khalipha”. Hannayensa ya zuba a aljihu duka biyu yana binta a baya fuska a tamke, sai wani lumshe idanu da buɗewa yakeyi akan lips ɗinda dake motsawa a hankali da yanayin tsoron daya bayyana ƙarara a fuskarta. Tana tafiya yana binta sai ji tai ta dangane da bango, juyawa tai a firgice ta kalli bayanta, ganin dai da gaske tazo ƙarshe hankalinta ya ƙara tashi, ta dubesa da saurin yin ƙasa zata durƙushe ya riƙo hannunta. “Yayanmu wl.....” “Shiiii!!!..” Ya faɗa a hankali yana saka idanunsa da suka canja launi cikin nata, tare da saka duka hannayensa a bangon ya dogareta yanda babu damar kuɓuta kenan. Gashi ya hana kuka dole kuma ta haɗiyesa, sai dai zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta ta fito. A wani irin ƙasa da murya sosai ya fara magana idanunsa cikin nata da takeson janyewa ya hana. “Dama idan kuka zauna gulman mutane kawai kuka iya ko?”. “Wlhy a'a Yayanmu, bama gulmar kowa ka tambayi Granny”. “Ni yanzu danaji ana tawa fa?”. “Y...y...Yayanmu ba gulm...ma bane fa?”. “To miye sunansa?” Shiru tai dan batasan mi kuma zatace ba itakam. Hakan datai ya sashi juya idanunsa yana sauke hannunsa ɗaya dake dafe da bango ya maida cikin aljihu. Yace, “Anyhow zan fara hukuntaki kafin ita mai baku lecture ɗin na kamata da sauran ɗaliban nata”. “Wayyo Yayanmu, wayyo Yayanmu”. Zinneerah ta faɗada iyakar marairaicewar data saka AK cije lip ɗinsa, yana binta da wani irin ƙasalallen kallon daya saka hawayen ƙaryarta ɗaukewa ɗaf ta shiga mar mar da idanu zuciyarta na harbawa da sauri-sauri..........✍ *_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 57* ...........“Nine kuma bana dariya sai shekara-shekara ko?”. “A'a wlhy Yayanmu bakai nake nufi ba, wani ne acan Danya”. Zinneerah ta faɗa tana duban gefen daya janye hannunsa. Hakan yayi dai-dai da wayarsa ta fara tsuwwa. Aljihunsa ya kalla da ƙoƙarin zira hannunsa zai ɗakko, ‘Alhmdllh’. Zinneerah ta faɗa a zuciyarta tana kwasa da gudu. Duk yanda AK yaso danne dariya a yanzu kam ya kasa, dole yay murmushi har haƙoransa na fitowa tare da girgiza kansa kawai. yace, ‘Zan kamaki har inda zakije ɗin ai” daga haka ya kai wayarsa kunnensa dan Hajiya iya ce. Zinneerah kam bata tsaya a ko inaba sai bedroom ɗinta nacan ciki, ta murzawa ƙofar key tana sauke numfashi da faɗin, ‘ALLAH na godema daka kuɓutar dani, Bahijja taso jamin salalan tsiya yau, dan ƙila zaneni yay niyyar yi ma’. Sai kuma ta kwashe da dariya saboda tuno su Bahijja, inama tanada waya yau data kirasu taji yanda aka kwashe. Bata taɓajin takaicin rashin wayarta irin yau ba, harta kaita da zama tunanin yanda wayar ta ɓata abin kamar almara ★★★ Tun abinda ya faru Zinneerah da AK basu sake ganin junaba har akai sallar magriba. Sai lokacin ta fito daga ɗakinta ta duba dining ɗin. Tasha mamaki ganin anci abinci data ajiye. Aranta take tunanin ashe ya shigo yaci abincin. Wajen ta tattara tare da falon, ta saka turaren wuta sannan ta koma ɗaki tai wanka. Tana fitowa sallar isha'i ta gabatar, bayan ta idar tai zamar gyara jikinta ranta fal tunanin mmn sadiq dasu Abdull, harma da Little da rabota dashi tun randa zata wuce danya. Tana kewarsa sosai harma da ƴan danya ɗin, yanzu da tanada waya ai da ta kira taji yanda suka sauka lafiya da jikin Tinene kuma. Tsaki ta ɗan ja ranta duk babu daɗi. Doguwar riga kawai ta saka yanda zata sake, tana ɗaure gashinta data taje taji an turo ƙofar ɗakin. Juyowa tai a hankali tana duban ƙofar aɗan rikice, wanda tayi zaton dai shine, yana sanye cikin wando jeans baƙi da baƙar t-shirt, sosai kayan sukai masa ƙyau duk da alamu sun nuna badan kwalliya ya sakaba. Ganin yanda idanunsa ke a kanta yasata yin ƙasa da nata, ya ƙaraso cikin ɗakin kansa tsaye da tafiyarnan tasa daba garaje, ga fuskar kuma babu alamar fara'a kamar ko yaushe, amma hakan bai hana ƙyawunsa da kwarjininsa fita ba a bayyane. “Barka da dare”. Ta faɗa kanta a ƙasa da ƙoƙarin jan gyalen jallabiyar zata yane kanta duk da bata kamla ɗaure gashin ba. AK da tunda ya shigo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182