Chapter 145
Chapter 145
idanun nasa ke akan gashin nata ya janyesu yana zama bakin gadon. Batare da yayi mata magana ba ya miƙa mata wayarsa. Amsa tayi duk da bata fahimci mi yake nufi ba, sai dai ganin sunan Granny da alamar tana online yasata kai wayar kunnenta tai sallama murya a marairaice. Dariya Granny tayi daga can da cewar, “Inno irin wannan marairaicewa haka?”. “Granny nayi kewarki ne”. “Nima haka Inno, shiyyasa nace Moddibo ya banike na karajin muryarki kafin na kwanta”. A take hawaye suka ziraro a kumatun Zinneerah, muryarta ta fara rawa alamun kuka. Kai kawai AK ya ɗan girgiza da mikewa tsaye, batare da yace komaiba ya zare wayar daka kunnenta.... Da sauri ta kallesa dai-dai yana maida wayar kunnensa. Idanun nasa ya ɗan juya mata da faɗin, “Daga gaisuwa kuma sai ki samin ita kuka Granny? To an fasa gaisuwar dake sai da safe”. Da alama wata baƙar maganar ta faɗa masa daga can, dan janye wayar yay yana murmushi. Batare da yacema Zinneerah dake sharar ƙwalla uffanba ya raɓata ya wuce inda ta ajiye masa system ɗinsa daya bari a ɗakin jiya. Ɗauka yay tare da nufar ƙofa yana faɗin, “Ki kawomin lipton”. Baki ta kuma tunzurawa tana matso hawaye da bin bayansa da kallo harya fice, babu yanda ta iya dole bayan ta gama kukanta ta share hawayen da ɗaukar turare ta ƙara a jikinta, hardasu fesa much freshener kamar yanda Hajiya Falmata ta koya mata, ta ɗauka wani ɗan kwalban turare da batasan kona minene ba ta shafa a bayan kinnenta da wuyanta, kamar yanda Hajiya falmatan ta sanar mata ta ringa shafa shi duk dare idan tai wanka, ta kuma ƙara da khumra mai shegen daɗi da narkar da mai shaƙa. Daga haka ta ɗau hijjab mai hannu jaa ta saka sannan ta fito. Kitchen ta nufa ta ɗaura masa lipton ɗin da ganyen shayin da hajiya Falmata ta bata shima, rashin wayonta yasa batai tunanin ko ganyen shayin na wani abu baneba daban. A wani butar shayi mai azabar ƙyau daya ɗauka hankalinta ta juye tare da kananun kofunansa tasa biyu, sai ɗan bowl ɗin data zuba suger shima ta ɗora da tea spoon guda ɗaya ta ɗauka tray ɗin tana addu'ar ALLAH yasa tayi komai dai-dai. Yana zaune a doguwar kujera ƙafarsa a miƙe yasa filo da ɗaura lap-top ɗinsa saman filon. Koda tai sallama bai dagoba amma ya amsa mata a saman laɓɓa yana cigaba da aikinsa. Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke idanunta, a centre table ɗin tsakkiyar falon ta ɗaura ƙaramin tray ɗin da jawosa kusa da shi tace, “Yayanmu gashi”. Ɗan ɗagowa yay yayi mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa, a taƙaice yace, “Zuba”. Kanta ta jinjina masa kawai ta tsugunna gaban table ɗin tana ƙoƙarin fara zubawar, yanda hijjab ɗinta yay ɗan bula lokacin da take kaiwa tsugunne ya bama hancinsa damar shaƙo fitinannun ƙamshin turarurrukan data sakama jikinta, duk da tun shigowarta ya jisu, sai haka datai ya ƙara ƙarfinsu fiye da farko a cikin hancinsa. Wani irin harbawa zuciyarsa tayi, har baisan yatsunsa sun kauce wajen tafa saƙon shirme ba a system ɗin. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta yana ɗan cizar lip dinsa na ƙasa. Zinneerah da batasan mi yake cikiba ta miƙo masa ɗan mitsilin tea cup ɗin irin na larabawa bayan tasa suga ɗaya dan tasan yanda yake so tunda yasha sata aikin sanda suna gida, tsaf ta gama haddace adadin da yake so. Idanunsa da suka canja launi lokaci guda ya zuba mata, dai-dai yana amsar shayin muryarsa a ƙasan maƙoshi yace, “Cire wannan hijjab ɗin banaso”. Mamakin maganar tasa yasata ware idanu sosai tana kallonsa. Sai dai yanda fuskarsa ke a ɗinke ya sata yin ƙasa da kanta ta hau ƙoƙarin cirewa tana haɗiye abinda ya tokare mata maƙoshi, dan duk da doguwar riga ce a jikinta tsananin kunyar zama take a gabansa a haka saboda santsin rigar yasa ta kwanta mata a jiki ta lafe, musamman da yazam ita da kanta ta rage faɗin rigar tun suna gida ita dasu Bahijja. Hannu ya miƙa mata alamar ta bashi, dole ta miƙa masa, kusa dashi ya ajiye hijjab ɗin dan son tabbatar da shike ƙamshin ko ita?. “Zauna”. Ya faɗa yana matsar da ƙafafunsa. Yanzun kam kasa haƙuri tayi sai da tace, “Yayanmu zanje na kwanta inajin barci”. “Nima ba gadin gidan zanyiba ai”. Ya bata amsa a daƙile. Tashi tai tsam ta zauna inda ya nuna matan har jikinta na neman hayemasa ƙafafu, tai saurin muskutawa kanta a ƙasa. Idanu ya tsira mata yana kurɓar shayin kaɗan-kaɗan saboda zafinsa. Amma dai haka yafi bukatarsa musamman wannan da yay masa matuƙar daɗi, ga wani irin ƙamshi mai daɗi dake fita a cikinsa. Ya fahimci ta matuƙar ƙwarewa da iya cuɗa hannunta cikin na juna idan tana waje a takure ko makamancin hakan. Ya danyi gyaran murya nason gusar da shirun nasu. Ɗagowa tai ta kallesa. Idanunsa a cikin nata yace, “Kin kira su baba ne? Kinji yanda su gwaggo sukaje gida lafiya”. Ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi, atake idanunta suka ciko da ƙwalla ta girgiza masa kai. “A'a ai bani da waya ta ɓata”. “Ɓata fa? A ina kenan?”. Da damuwa sosai a fuskarta tace, “A can gida, tun lokacin da Granny bata da lafiya zaku wuce london”. Cikin ɗan taɓe baki yace, “Kin dai jefashi wani waje”. “A'a wlhy Yayanmu, nifa ina gama waya da Mama a ranar daga ajiyewa naje na tarosu na nemeta na rasa. har yanzu kuma ban ganshiba, kuma ko ina su Meenal sun tayani na duba”. “Uhm to wani ya sace kenan”. Ya bata amsa cike da basarwa. Itako tace, “Amma kuma a gidan nan wazai saci waya?”. Wani ɗan murmushin daya bata mamaki taga yayi yana lunshe idanunsa. Cikin basar da maganar yace, “Ganyen shayin nan yanada daɗi waya baki?”. Badan taso barin waccan maganarba tace, “Hajiya Falmata”. “Wacece ita?”. “Nima sai kwanan nan na santa suna mutuncine da Granny”. “Uhm! Itace ta baki wannan turaren mai ƙamshi haka?”. Ya faɗa murya a shaƙe dan shayin da yasha ya fara aikinsa. Rasa amsar da zata bashi tayi, sai ta ɗan jinjina kanta kawai. “Baki da baki ne?”. “A'a kayi haƙuri itace ta haɗa, khumrah ne”. Komai bai sake faɗaba ya sauke lap-top ɗin dan aikin kam bazai iya cigabuwaba, ƙafafunsa ya zaro daga kusa da ita ya ajiye ɗaya a ƙasa ya tanƙwashe ɗayar, sake ɗaukar butan shayin yayi ya tsiyaya dasa suga ɗaya a ciki ya motsa. Cigaba da shan abinsa yayi da maida hankalinsa ga television. Itama gyara zamansa da yayi ya sakata jin ɗan sanyi ta koma kallon television ɗin da satar kallonsa. dan ya dage sai ɗora shayin yake hankali kwance. Daya shanye yake karawa, tanata lissafi sai da yasha kusa cups bakwai duk da dai ɗan mitsitsine kofin. Sai da aka kammala labaran da suke kallo ya miƙe, batare da yayi mata magana ba ya fice gaba ɗaya a sashen har tana mamakin ina zaije? Bata da mai bata amsa dan haka ta ƙudiri aniyar zaman jiransa ya dawo ita dai taje ta kwanta ta farajin barci. Shiko daya fita kai tsaye sashenta ya nufa, kitchen ya fara shiga ya kaso wutar can ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182