Chapter 31
Chapter 31
ƴar takarda dake a linke da alamu suka nuna cheque ne na kuɗi. Takardar Mama ta amsa batare data fahimci ta minene ba, yayinda su kuma mutanen wajen suka sami damar yin dariyar yanda ta ruɗe musu ɗazun. Mama ma dasu Alhaji duk dariyar sukeyi, daga haka suka ɗunguma ɗakin da aka kwantar da Zinneerah. Mamaki ya kama Mama ganin ashema ta farka har likitan daya shigo ɗakin dubata yana ɗan musu faɗa akan fita su barta ita kaɗai haka. Haƙuri mama ta bashi, tare da masa bayanin dalilin fitar tata. Ya ɗan murmusa yana faɗin, “A mama ai asibitin nan akwai tsaro sosai, motsin kowa dake ciki ana ganinsa ta cctv, dan haka ku kwantar da hankalinku babu abinda zai faru harku tafi insha ALLAH”. “ALLAH yasa hakan” suka faɗa kusan a tare. “Amin ya rabbi. Yanzu ga wannan, shine list ɗin komai na kuɗaɗen da zaku biya, sai kuma jini da zaku samo yanzu dan za'a ƙara mata. Dama jiran farkowarta muke mugani koda yuwuwar hakan, to yanzu kam naga alamar tana buƙatar jini leda ɗaya”. Amsar takardar Alhaji yayi yana masa godiya, daga haka Doctor ya fice. Gaban gadon suma duk suka ƙarasa sunama Zinneerah sannu, da kai kawai take iya amsa musu batare data iya kallonsu ba. Sai faman haɗiyar zuciya take dan ita kaɗai tasan mitakeji a ranta. Ganin kamar batason hayaniyar ne ya saka Nurse Salima dake ɗauke da ɗan jinjirin daya gama shige mata rai har yanzu faɗin, “Inaga batason yawan hayaniya yanzu, idan kun gama dubata sai muɗan fita waje a bata waje”. Gamsuwa da bayaninta ya sakasu amsa mata. Mama ta kalli Salimar tana faɗin, “Yauwa ƴarnan kinma sa na tuna. Ina dabinon da kika bada shawarar a tauna a bashi? Kinga yanzu tunda ga Alhaji sai ya bashi ɗin ko”. Cikin ɗan nuna shakku Salima tace, “Aiko mama na muku laifi ko nace shishshigi, nazo da dabinon danna kawo mikine na biya office ɗin Dr Mahmud ɗin inda na sami Oga acan. To daya sanar min ɗakin da zan kawo yaron sai nake cewa dama can zani nakai dabino a bashi ko zai rage kukan yunwar da yakeyi. Jin hakan da kuma kukan da yaron keyi har lokacinne ya saka Oga ya amshi dabinon da kansa ya tauna ya bashi, har yana faɗin ALLAH yasa ya gaji sunansa”. Alhaji dake saurarensu yace, “To masha ALLAH, ALLAH ya saka masa da alkairi duk da mu bamusan shi wanene ba”. Salima tace, “Baba ai shine mai asibitin nan”. Dukansu sai da suka ɗan ƙwalalo idanu waje. Mama tace, “Babbar magana, shima likitanne kenan?”. “A'a mama, shi ba likita baneba, ɗan kasuwane. Nasan dai bazaku gaza sani kojin sunan *_AK SHIRA_* ba a garin nan ai”. “Lallai kam sani bana wasaba, duk da dai ba sani na zahiri bane, amma wannan sunan ba ɓoyayyen suna bane, dan a Shira Family kowa yasan *AK SHIRA* ba ɓoyayye bane, kodan gidajen mansa kawai ai sun isa ka sanshi, balle kuma hidimar da yake ga bayin ALLAH mara iyaka”. “To aiko Baba shine da kansa ya bama jaririn nan dabino yau, tare da wannan takarda da nake kautata zaton kuɗine rubuce a ciki”. Sosai maganar ta sake girgizasu, mama ta mikama Alhaji takardar cheque ɗin. Amsa yay ya duba yana jinjina kansa. “Uhm lallai wani aiki kam sai manya. ALLAH ya saka masa da alkairi. ya azurtashi da duk alkairan duniya da lahira, ya kuma cigaba da karesa a duk inda ya saka ƙafa. Kuɗine zunzurutu harna dubu ɗari biyu ya rubuta anan”. Sosai suka ƙara jin mamakinsa, ace lokaci guda mutum yay ƙyautar dubu ɗari biyu wa jariri kawai. Alhaji ya katse zantukan nasu da faɗin, “To lallai kam abokina dole kaci sunan AK Shira ai”. Dariya duk sukayi banda Maman Sadiq datai ɗan murmushin kawaici. Hakama Zinneerah dake saurarensu kawai tana share hawayenta a ɓoye. Alhaji ya buƙaci Salima ta rakashi yaymasa godiya, daga nan yaje wajen neman jinin da biyan kuɗaɗen da sukace. Bata musaba ta miƙama Mama jaririn suka fita. Office ɗin Dr Mahmud sukaje. Bayan Salima tai knocking ya basu izinin shiga suka shigo. Shi kaɗaine a ciki, sai dai mayen ƙamshinsa na nan manne da office ɗin duk da babu shi a ciki. Dr Mahmud yace, “Salima lafiya dai?”. “Laya ƙalau Doctor, dama Baba ne yace na rakosa yayma Oga godiya. Sune masu jinjirin nan na ɗazun”. “Oh ALLAH sarki, Baba ina yini”. “Lafiya lau likita, ya aikin naku?”. “Alhmdllh baba. Sai dai gashi kuma shi harya tafi, kasan shi uziri ba ƙaremasa yakeba. Dama yakan zo duk irin wannan ranar a tsakkiyar shekara da ƙarshenta ne ya bada jini inhar yana kano, yanzu hakama zaije Lagos ne ya biyo tanan ya bayar, ina ƙyautata zaton yanzu haka ya isa airport”. Alhaji yace, “Ashsha. Naso kam na gansa nai masa godiya wlhy, sannan ya cika ladansa nama yaron nan huɗuba ya kuma saka masa sunan nasa dan ya cancanta”. Cikin jin daɗin wannan karamci Mahmud yace masha ALLAH, shi da ya faɗa da wasa ashe ALLAH ya amsa mai sunan nasa aka samu, duk da nasan yanzu yayi nisan kiwo, amma bara na taɓasa a waya muji ko zamu samu ya ɗaga baba ka zauna”. Zama Alhaji yayi yana murmushi. Dr Mahmud ya ɗauka wayarsa shima fuska ɗauke da murmushi ya shiga kiransa. Tana gab da tsinkewa aka ɗaga. Harma Mahmud ya fidda ran hakan. Cike da zumuɗi Mahmud yace, “Afuwan ranka ya daɗe kaga na kiraka”. Basusan amsar da aka bashi daga canba. Cikin ƴar dariya yace, “Tona gode ranka ya daɗe. Dama masu jaririn daka ɗakko ɗin nan ne sukazo maka godiya, tare da sake kawosa ka cika ladanja ta masa huɗuba da saka masa sunan naka”. Nanma basuji miya faɗaba, sai dai yanda fuskar Dr Mahmud ta ƙara washewa da fara'a zaka tabbatar da magana mai daɗi yake masa. Sai kuma ya saka wayar a amsa kuwwa (Hansfree) ya ajiye gaban Alhaji. Wata tattausar murya mai cike da tarin nutsuwa kamar ta rowa sukaji tace, “Assalamu alaikum, baba barka da rana”. Da sauri Alhaji yace, “Wa'alaikissalam, barka dai ranka ya daɗe, yaya ƙoƙari?”. “Alhmdllhi baba. Yanzun nakejin daddaɗan albishir na samun takwara, gashi kuma nayi gaggawar tafiya”. Yanda yake maganar cike da nutsuwa kamar bayasone ya saka Alhaji yin murmushi mai faɗi. “Alhaji ai kowa zaiso samun mai sunanka a gidansa kodan tarin alkairan dake tattare dakai. Munga hidima ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara buɗi. Amma naso ace kaine da kanka kaima yaron nan huɗuba da sunan daka zaɓa masa”. Kaɗan sukajiyo sautin murmushinsa daga can, cikin sake nutsar da muryar tasa mai sauti a tausashe yace. “Nima naso hakan Baba, dan kun bani abu mai daraja da bazan mantaba a tarihin rayuwata, amma duk da haka na bama Mahmud wakilcin yima takwarana huɗuba. ALLAH ya rayasa ya albarkaci rayuwarsa, ALLAH yasa ya zama mai tausayinmu da jin ƙanmu anan gaba”. Atare suka amsa da amin kowa cikin jin daɗi. Musamman ma Alhaji dake mamakin yau shine ke magana da AK Shira baki da baki ta waya. Wata hikima sai UBANGIJI. Shikam dai har abada bazai taɓa mantawa da haihuwar wannan yaro ba a rayuwarsa. Kamar yanda ya bada wakilci ga Dr Mahmud hakance ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182