Chapter 51
Chapter 51
bandaki ta Mopping da turaren wanka a kan kudi 3,000 kacal indai q cikin watan September dinnna ne daganan kuma zasukoma *normal price dinsu, hakanan turarukqn wuta da humra dinmu anyi masu ragi duk me bukata se nememu a 08034236800 ta what's app kokuma ya ziyarci shafinmu a instagram* @turare_by_awwaba mungode* ______________________ *Page 19* ...........Sosai zaman hutun nan yayama Zinneerah daɗi. Dan koba komai shaƙuwa sosai ta sake shiga tsakaninta da Little, dan yanzun taɗan rage yin kawaici akansa. Hakama ƙannenta koda yaushe suna nane da ita. A randa ta cika kwanaki goma sai ga su Jamal babu zato wajen sha ɗaya na safe. Lokacin suna shirin fita gidan sunan ƙanwar Maman Halima. Duk da taso taje gidan sunan sai zuwan nasu ya kauda son fitar, ta shiga murnar ganinsu. Su maman Halima kam dake goye da Little suka tafi bayan sun gaisa dasu Bahijja iyayen rawar kai. Sukam babu ruwansu da wata baƙunta. Dan sakin jikinsu sukai tamkar a gidansu. Sai hakan yayma maman sadiq daɗi sosai, dan koba komai hakan girmamawace suka nuna mata. Maman Sakina da yaranta kam sai suka shige ɗaki suna leƙensu ta Window da gulmar a ina su mmn sadiq ɗin suka samo yaran ƴan gayu haka?. Basu da mai basu amsa, dan haka suka cigaba da habaice-habaice da sukar mmn sadiq ɗin harma dasu Meenal da basusan da zamansu a gidanba. Harda cewa kodai a gidansu Zinneerah ke zaune aikin wanke-wanke yanzun?. Sai suka yarda a haka duk da suma sun san faɗane kawai danjin daɗi. Dan Zinneerah batai kama da wadda taje aikatauba. Su Jamal ma sun sami rabon nasu zagin sosai, dan koda sukazo suka iske Maman sakina a tsakar gida dasu Luba ko kallo basu ishesuba. Sai mmn halima data tarbesu da fara'a suka gaida cike da girmamawa. Hakanne ya sake baƙanta ran mmn sakina taja ƴaƴanta suka shige ɗaki. Wainar filawa Zinneerah tai musu kamar yanda sukace suna buƙata, sai da sukaci suka ƙoshi Abba ya dawo gidan bayan la'asar suka gaisa sanan driver yazo ya kwashesu harda Zinneerah da taso yin sallama da Little da sauran yaran, dan sanda maman halima ta wucene da shi yana barci, ko ganinsu su Bahijja ma bayi sukaiba. To da yakema ba sanin labarinsa sukaiba basu kawo komai a ransuba sun zatama ɗan mmn halima ɗinne duk da dai basuga fuskarsaba. Sosai Hajiya iya dasu Yah Moos'ab suka nuna farin cikinsu na dawowarta. Tare da faɗi mata sunyi kewarta kowa a gidan. Cikin ƴar dariyarta tace, “Nima nayi kewarku ai, wani lokacin har mafarkinku nakeyi”. Sunji daɗin maganarta har cikin ransu, dan itama suna mata kallone na ɗaya daga cikinsu bawai wadda tazo cin arziƙi gidansu ba. Moos'ab da bai cika yawan maganaba shi dama yaɗan ɗage gira yana gyara kishingiɗar da yay a kujera da faɗin, “Ni ba yarda nai dakeba fa yarinya”. A hankali Zinneerah ta ɗago manyan idanunta farare tas ta zuba a kansa, irin kallon da yake matane ya sakata saurin maida nata ƙasa tsigar jikinta na tashi, ba yaune karan farko da Yah Moos'ab ɗin ke mata irin wannan kallonba, shiyyasa a mafi yawan lokuta bata wani cika sakewa da shiba sosai. Kasa bashi amsa tayi, hakan yasa Saifudden kwashewa da dariya yana faɗin, “Wataran dai zata fashe”. “Minene zai fashe?”. Cewar Haneef dake a kusa dashi yana latsa waya. Saifudden yace, “No jaridar mai tsadace, duk maiso ya tanaji kuɗi akwai ranar da zan saida muku”. Abidah ce tai dariya tanama Saifudden alamar jinjina. “Ai Yah Saif nima na daɗe da harbo jirgin, kasanfa idanuna sun iya gane-gane nima, duk randa suka tashi saya ka nemoni zan ƙara da nawa rahoton”. Tsam Zinneerah ta miƙe zata bar wajen, dan haka kawai ta tsargu da zancen nasu, tanaji a ranta kenan suma duk suna sane da Yah Moos'ab ɗin komi?. “A'a, auta ina zuwa?”. Cewar Safiyya da sauri. “Im ihm Aunty Safiyya zanje cikine nayi wanka”. Da sauri Ni'ima tace, “Wankafa? Ba shigowata Granny ke faɗin kina ciki kina wankaba Auta (Mafi yawan lokaci haka suke kiranta auta). Kasa magana tai, hakan yasa Saifudden kwashewa da dariya yana raira waƙa. Duka Moos'ab ya kai masa. Yay saurin wuntsilowa a kujerar yana cigaba da dariyarsa. Da sauri Zinneerah tabar wajen ranta fal tsoro. Ɗakin da har yanzu ta kasa sakin jiki da zamansa ta shige tare da faɗawa saman gadon a karo na farko. Tai ɗan murmushi dajan filo ta cusa kanta a ciki. A ranta kuwa rayawa take itakam karsu Yah Saifudden su jawo mata rigima. Ina ita ina soyayya da waninsu bayanma duk kallon yayu take musu itakam. Wannan zance ai da girma yake idan har yazo a yanda zuciyarta ke hankaltar da ita game da take-taken Yah Moos'ab ɗin. Haka ta kasance cikin dogon tunanin da har barci mai nauyi yay awon gaba da ita batare data saniba. Harsuka gama hiratsu kowa ya miƙe zuwa makwancinsa basu sake ganintaba. Hajiya Iya kam dama ta kwanta tuni saboda maganin mura da tasha, kuma dama ita ba'a doguwar hira da ita, tanada saurin barci. Wani lokacinma sai jikokin nata suzo su ƙaraci shirmensu a sashen bata saniba. Dan kullum nanne wajen hiratsu sai dai idan yayansu na gari kam babu sakewa, duk da suna zuwa a hakan. Sosai Zinneerah taji daɗi barci akan wannan gado da yau ya zame mata na farko, dan ko fitsari bata farka yiba yau saboda daɗin barci. Sai kiran sallar farko na asuba ta buɗe idanunta da ƙyar tana karanto ɗaya daga cikin addu'ar tashi daga barci. "الحَمْدُ لله الذِي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ النُّشُور" Alhamdu lillahil-lazee ahyana ba'ada ma amatana wa-ilayhin-nushoor. Sai da ta bada ratar kusan mintuna uku bata motsaba dan idanunta su ƙara saki sosai sannan ta tashi zaune tare da zuro ƙafarta ta sauka a gadon. Tayi mamakin ganin an kashe mata wuta da lulluɓa mata bargo, sai dai tasan bazai wuce ɗaya daga cikin su Aunty Safiyya ba. Wanka ta farayi da ɗauro alwala ta fito. Bayan ta gabatar da nafila raka'a biyu ta ɗakko AL-QUR'ANI ta fara duba inda akai mata ƙari jiya a islamiyyasu data koma zuwa ta anguwar su mmn sadiq. Tana zaune a wajen har akai salla. Bayan an idar tai Azkar kamar yanda Hajiya Iya ke maimaita mata muhimmancin yinta a kowacce safiya da maraicen duniya. Sai da ta kammala gari yay haske ta miƙe ta gyara ɗakin tsaf kamar yanda ta saba, ta saka kayan ƙamshi ta fice zuwa taya su baba Rahi aiki. Amma sai da ta fara shiga ta gaida Hajiya Iya da mura sannan. Sai da suka kammala komai tsaf suka shirya tebir sannan ta koma ɗakin domin yin wanka. Sanin ba kowa ke shigowa ɗakinba sai Hajiya iya yasata fitowa kanta tsaye da towel. Sai ƙarami da take ƙoƙarin naɗe kanta data wanke a ciki. Wani irin mugun tsargawa zuciyarta tayi dai-dai lokacin da take fitowa daga ɗan lungun da toilet ɗin yake. Tsabar ruɗani da firgici batama san ta saki towel ɗin da take ƙoƙarin ɗaurawa kantaba a ƙasa.... Ƙyaƙyƙyawan matashin dake zaune hakimce a bakin gadon ƙafa ɗaya kan ɗaya waya manne da kunnensa ya ɗago dara-daran idanunsa masu cikar gashi da haske yana kallonta da alamun tsantsar mamaki a cikinsu. Hannunsa yakai bisa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182