Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ɗaya sai yanzu na tuna. Gashi Atine tace tuwo aka ɗora yanzu da za'aci da rana. Kinga kuma dole ne miyar ɗaurin aure ma na gobe a haɗa da miyar yauƙi dan taushe ɗin nan ba isa zataiba”. Kai Magajiya ta ɗan kaɗa mata, sai kuma tace, “Amma nikau da dai kin aiki ko Tinene ko Sa'a mana. Ke da mutane keta shigowa kuma ace kinje wani waje ai babu daɗi. Sannan waɗanan masu tahiya asibitin ya kamata ki jira kiga dawowarsu ko”. Nannauyan numfashi Inna ta sauke tana ƙyaɓe fuska. Tace, “Kinga Magajiya hita batun waccan watsatstsiyar yarinyar. Dan babu mai ɓata mani taro aradu. Maganar amso kuɓewa kuwa gara naje da kaina. Dan daga Tinene har Sa'a mashiririta ne da kike ganinsu”. Magajiya tace, “To ni haɗani da Tinenen muje. Ai in dani dai batacewa bata zuwa ko?”. Sosai wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ya turniƙe zuciyar Inna. Ji take kamar ta kaima Magajiya duka. Da ƙyar ta shanye abinda ya tokare maƙoshinta ta ƙaƙaro murmushi dan tasan nacin Magajiya batun yanzu ba. Tace, “To nahi yarda da wagga shawarar kau. Bara naga giccin Tinenen saina hiɗi maki ku tahi”. Da to Magajiya ta amsa, tare da ɗaukar buhun da garin masara ke ciki wanda dama shita shigo ɗauka ta fita. Da wata muguwar harara Inna ta raka bayanta tana jan tsaki. Ta sauke gyalen nata tana ƙudundunesa ta cusa cikin lalitar bujenta na ciki. Ganin ya kwanta babu mai ganewa ta fito a ranta tana ayyana. (Ai idan kinsan wata bakisan wataba magajiya). Shigewa tai cikin masu hidimar aikin abinci ta cigaba da harkokinta. Sai da taga kowa hankalinsa baya kanta tai wuff zuwa bayinsu tabi ta cikin dannin geza da akai musu sakamakon zubewar katangar bayin lokacin damuna daya wuce. Har yanzu kuma ALLAH baiba baba damar gyarawa ba. Saurin zaro gyalenta tai ta warware ta aza bisa kai. Cike da sauri da sassarfa ta dinga ratsawa ta cikin gonaki dan kar wani ya ganta........ ★★★★ A asbiti kam bayan tabbatar da Zinneerah ba suma tayi ba ruɗanin maganar likitace kawai ta haifar mata da hajijiya sai suka saka mata ƙarin ruwa. Hankalin su Gwaggo Laritu bai kwanta ba sai da likita yay musu bayani. “Ku kwantar da hankalinku tana cikin ƙoshin lafiya. Kuma Alhmdllhi bama suma tayiba. Yanayin da take cikine ya kawo hakan, da alama kuma ko karin kumallo bataibama kuka fito”. A kusan tare suka sauke ajiyar zuciya. Rabilu yaron Kawu Haruna daya kawosu yay saurin faɗin, “Likita to ko za'a samo mata wani abune taci?”. “Eh za'a iya. Amma a yanzu dai mun saka mata ƙarin ruwa ta samu barci. a cikinsa kuma akwai abinda zai taimaka mata akan yunwar, da alama dai kai ne mai-gidan nata ko?”. Murmushi kawai Rabilu yayi batare da ya amsawa likitan maganarsa ba. Sai dai Cikin ƙarfin hali duk sukai masa godiya. Amma a ƙasan ransu su kaɗai sukasan irin tashin hankalin da suke ciki game da wannan ciki na jikin Zinneerah. Suna tsananin tausayin yarinyar saboda halin data tsinci kanta a ciki a gidansu na rashin mahaifiya. Ga yayansu shi da babu duk ɗaya a gidansa saboda makircin matarsa Asabe. Sunyi iya ƙoƙarinsu dan ganin sun maidosa hayyacinsa tun tuni amma Asabe ta sake shiga ta fita ta raba tsakaninsu da shi. A yanzu haka ko mu'amula bayayi da kowa a cikinsu, ko maganar auren Karima bai sakasuba sai ji sukai a gari. Abin bai ɓata musu rai ba sosai saboda sunsan baya a cikin hayyacinsa ne sam. Yanzu haka maganar cikin nan Sa'a ce taje ta sanarma Gwaggo Laritu tana kuka, kuma da'ace ba Zinneerah abin ya shafaba cikin ƴaƴan Inna ne ko takansu bazasubi ba. Lallai lokaci yayi da zasuyi wani abu game da gidan yayan nasu kam a wannan karon. Dolene kuma susan wanda ya shiga mutuncin Zinneerah kar rayuwarta ta ƙarasa shigewa cikin garari sunaji suna gani. Kusan su dukansu haka suka dinga tanani a cikin zukatansu har ruwan da aka sakama Zinneerah ya ƙare, sai dai barci takeyi sosai. Sallar azhar su Kawu suka tafi yi massallaci. Itama Gwaggo Laritu saita fito dan neman inda zata gabatar da tata. Bayan duk sun idan da sallarne Rabilu yaje ya samo musu abinci dan su ɗanci, dan su kansu akwai waɗanda basu karya ɗinba a cikinsu.......... ★★★★ Sauri sosai Inna ta dinga zabgawa harta iso ƙauyen mahuta dake can yamma da su. Ƙauyene sosai dan gidajen garin bazasu gaza biyarba ma gaba ɗaya. A farkon shiga garin ta gamu da yara sun dawo ɗibar ruwa rafi. Tsaidasu tai ta ɗiba ruwan tasha sosai tana sauke numfashi a jajjere. Dan ba ƙaramin sauri ta zabgaba a tafiyar tata. Daga haka ta isa gidan dake ƙarshe a jerin gidajen ƙauyen. Tun a ƙofar shiga zauren gidan ta zabga sallama. Daga ciki akai gyaran murya tare da amsawa, sannan aka bata iznin shigowa. Babu kowa a soron, sai dai akwai ƙofar dake nuna alamun ɗakine, dan akwai labule da takalma a ajiye, sai wata a gefe ta shiga ainahin gidan kuma. “Gahwaranku dai”. Inna ta sake faɗa tana matsawa ga ƙofar ɗakin. Daga ciki muryar namiji dattijo ta sake amsa mata da “ALLAH yay mana aikin gahwara shigo”. Labulen ta ɗaga ta shiga ɗakin dake cike da shirgin da zama lissafasu ma ɓata lokacine, sai Dattijon dake zaune yana rubutu a allo da tawwada da alƙalami. Kallonta yay cike da fara'a kamar yanda itama take faman washe haƙwara. “A'a Asabe ce a garin yau?”. “Wlhy nice malam kallamu. Kasan gobe ne ɗaurin auren ƴar wajen tawa, gashi kuma banzo na amshi abinda ka ce ba tun kwanaki idan auren yazo. Bayan nan kuma ga watama matsalar datake neman sake taso mani kuma”. “Tofa babbar magana. Ai dama inata tsumayen zuwan naki, dan kwanaki hudu da suka shige na shigo Danya ɗin nakejin auren yarinyar wajen naki ya tashi. Harma naita mamakin banji daga garekiba”. “Ayya, ka gahwarceni malam. Abubuwane sukaima kaina yawa a tsakanin nan wlhy. Amma zuwa nanɗin yana raina kodan a shiryamin yarinyar tunda kaima kasan dai yanda abubuwan suke ai”. Murmushi yayi yana ajiye allon da yake rubutun da gyara zamansa. Ya jawo wani ƙwarya yana tura mata gabanta. “Kinga komai ma na haɗa. dama ko bakizoba ni zanje ɗaurin auren gobe, to niyyata dama naje miki dasu ai”. “Kai madallah madallah malam kallamu, nagode nagode sosai da wannan karamci naka. ALLAH ya saka maka kaima da alkairinsa”. “Amin. Yanzu minene gudar matsalar kuma?”. Nannauyan nishi Inna ta sauke tana gyara zama. Cike da takaici da baƙin ciki tace yarinyarnan da uwarta ta bar mani ciki ya bayyana ga jikinta jiya. Tofa shine shaggun dangin uban nata sukazo sukai tsaye akan lamarin har suna iƙirarin sonjin ina taje kwanaki. Kasan kuma munyi aiki kwanaki akan rihe bakin kowa bai sake tambayarta ina taje. Itama kuma karta hwaɗi ma kowa ɗin. To wlhy yau malam kallamu suna neman ɓalloman aiki musamman ɗiyar wajena dake aure Sanni. Kasan nayi-nayi na rabata da yarinyar abun ya hwaskara”. Kai malam kallamu yaketa girgizawa yana saurarenta. sai da taje har ƙarshen zancenta ya fara magana. “Kamar yanda na hiɗi maki tun kwanaki uwar yarinyarnan shu'umace ta gaske. Dan duk da kin hiddata a gidan nan bawai ta

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182