Chapter 87
Chapter 87
ya gadama zaka fahimci yana tare da jin daɗin zaman. Hasalima aikinsa yaketa famanyi a lap-top kamar baya a wajen. Dan shima rashin ganin gilmawar Farah a gidan yasashi tunanin ko bata nan. Sai kusan gab da magriba sai gata ta fito da alamun barci ta tashi. Sosai yake binta da kallon mamaki. Itako tayi kicin-kicin da fuska cike da takaicinsa. Kenan har takai ya dawo gidan bazai nemetaba saboda yana tare da ƴan uwansa. Batare da tayi magana ko kula gaisuwar dasu Meenal ke mataba ta juya ta koma ɗakinta hawayen takaici na zubo mata. Da kallo duk suka bita harta shige. Fuskarsa na nuna alamun ɓacin rai yace, “Dama tana gidan?”. Babu wanda ya iya bashi amsa a cikin su Jamal. Sai Hajiya iya ce tace, “Nima duk zatona ta fice ai, dan tunda kuka bar gidannan wani cikinmu baiji ko motsinta ba. Lafiya kuwa take Moddibo? Ya kanata kaje kaji”. Maida kansa yayi ga aikinsa yana gyaɗama Hajiya Iya kai kawai, dan shi bazaiso ɗan sauran mutuncinta ya ƙarasa zubewa a idonsu ba. cikin son danne takaicinsa dason rufa asirinta, Ya miƙe yana faɗin, “Inaga to jikin natane babu daɗi. Granny wannan babyn naku na bama matata wahala ya kamata ku tsawatar masa”. “Kai kai Moddibo kana nufin ciki ne da ita?”. Hajiya iya ta faɗa cike da zumuɗi saboda jin firucinsa. Ƙayataccen murmushi ya saki yana kallonta. Hakan da yayi ya saka su Bahijja miƙewa suka hau murna da rawa. Yanda sukai ɗin sai ya sakashi jin ƙarin daɗi a cikin rai, a bazata suka haɗa ido da Zinneerah da take murmushi har haƙoranta na bayyana, ita dai tana daga zaune bata tashiba. Saurin maida nata idanun tai ƙasa tsigar jikinta na tashi, dan yanda yay murmushin ba ƙaramin sake fiddo kamanninsa da Little yayiba. A hankali shima ya janye nasa da raɓasu ya wuce zuwa ɗakin Farah ya barsu hajiya iya na jero godiya ga ALLAH da kirarin farin ciki Khalipha da Zinneerah na amsa mata da amin. Dan su Bahijja shirmen da suke na murna yasa bajin mi hajiya iya take faɗa sukeba. Sai da suka bari yaja wasu ƴan mintuna da shiga sannan suka miƙe suma domin zuwa dubata. Sallama suka farayi ya amsa musu da cewar su shigo sannan suka shiga. kusan Zinneerah ce ƙarshen shigowa. Farah na kwance a gadon. shi kuma yana zaune kusa da ita gab hannunta cikin nasa. Dan tunda ya shigo zuciyarta ta bata shawaran cewar tai amfani da wannan damar kawai tace bata da lafiya. Hakanne kawai mafitarta gudun samun matsala. Sai kuma akai sa'a shima ya shiga tambayarta mike damunta? Shine ta sanar masa da zazzaɓi ta yini da ciwon kai. amma tasha maganin da Doctor ya bata. Kukan da tasha yasa idanunta kumbura dama gata fara. Ta ɗagosu da ƙyar tana ɗan dubansu da amsa sannu da addu'ar da suke mata. Koda idanunta suka sauka akan Zinneerah dake can ƙarshe bayan Khalipha sai da taji wani tuƙuƙin baƙin ciki. Ta janye idanunta dake sake cikowa da ƙwallar jin kishin kasancewar yarinyar a garesu, tanajin tsoron ganin wata mace da aure zai iya shiga tsakaninta da mijinta ta raɓesu, shiyyasa zaman Zinneerah a gidan yafi na kowa damunta a yanzu........ “Da alama ma dai yinin yau bakici komaiba?. ko kina da buƙatar wani abune a nema miki ƴar albarka?”. Maganar hajiya iya dake shafa mata kanta ta dawo da ita hankalinta. Kafin tace wani abu AK dake jin daɗin kulawar da Hajiya iyan ke nunawa akan matar tasa yace, “Nima abinda nake mata magana kenan kafin ku shigo, ya kamata ko tea tasha”. “Banajin cin komai ne ALLAH”. Ta faɗa a hankali cike da shagwaɓa tana kallon AK ɗin da shima ita yake kallo har yanzu hannunsa cikin nata. “A'a bazai yuwuba Farah. Zinneerah jeki ki haɗo mata ko tea ne da wani abin dan kinfi waɗanan nutsiwar yin abu”. Kai Zinneerah ta jinjinama Hajiya iya da nufar ƙofa. Duk da tanajin Farah na cema Hajiya Iyan ta ƙoshi bata dakataba ta fice. Dan ita dai har cikin ranta tausayin Aunty Farah taji ya shigeta. Ta ɗanɗana wahalar ciki tasan mi akeji, shiyyasa da ance ciki na wahalar da mace sai taji tsananin tausayinta. Bata wani zaman ɓata lokaci ba ta haɗa tea mai daɗi dan komai akwai, har kayan abinci akwai duk da ba irin wanda suka sani bane, dan mafi yawansu na gwangwanine da sauransu, taɗan ɗiba mata cake da Khalipha ya kawo musu ɗazun ta haɗa dashi ta koma ɗakin. Duk suna tsaye har yanzun, batare data yarda ta kalli kowa ba ta nufi gaban gadon, tana niyyar ajiye tiren a ƙasa ya riƙosa batare da yayi magana ba. Ita kuma batai tunanin shiɗin bane dan haka ta ɗago, saurin sakar masa tiren tayi saboda shigewar idonta cikin nasa. cikin ɗan daburcewa ta miƙe daga ranƙwafowar da tayi a gabansu taja jikinta baya. Da wani irin tashin hankali Farah ta tashi zaune tana duban Zinneerah ɗin dan komai akan idonta ya faru, zatai magana AK daya gama karantarta yay azamar katseta. Ganin yanda yay da fuska yasata haɗiye abinda tai niyyar faɗa akan Zinneerah ɗin, da wannan damar ya kalleta cikin ido yana jefa mata gargaɗin ki kama kanki. Tare da ɗaukar kofin shayin ya miƙa mata. A cinkushe tace, “Ni nace na ƙoshi”. “Ni kuma nace sai kinsha”. Ya katseta a kausashe. “Haba-haba Moddibo minene abin faɗa kuma anan, kaga bani ni na bata da kaina. Kai sam baka iya lallaɓa mutumba wlhy”. Hajiya iya da batasan dalilin kaushin nasaba ta faɗa. babu musu ya miƙa mata kofin shayin. Akan dole Farah tasha shayin da cake ɗin badan tasoba. Dan har wani ɗaci-ɗaci suke mata a maƙoshi. Musamman da idanunta suka sake gano mata AK na kallon Zinneerah da kanta ke a ƙasa tana latsa wayar Jamal hankalinta kwance. Ita kanta da take mace sai da taga annurin fuskar Zinneerah ɗin musamman yanda hasken wayar ya haskata ga kuma wani ɗan murmushi bisa fuskar tata dake da nasaba da abinda take gani a wayar. Itako Zinneerah ba komai yasata murmushin ba sai hoton Little da take gani a wayar Jamal ɗin. Khalipha daya fahimci inda Farah ɗin ke duba rai ɓace ya sakashi cewa suje falo, duk da shi baiga kallon da Yayan nasu kema Zinneerah ɗinba sam. Bama shiba kowama ba lura da AK na kallon Zinneerah ɗin yayiba, dan itama ɗin dai shegen zargi dabin ƙwaf-ƙwaf ɗintane ya kaita ga hango abinda yake neman saka zuciyarta bugawa. Fita sukai suka barta da hajiya iya da Yayan nasu. Koda suka dawo falonma Zinneerah shigewarta tai ɗaki acewarta lokacin salla yayi. Tanason kuma tayi tilawar karatu yau dan ta kwana biyu batayiba. Suma ganin lokacin sallar yayi sai duk basu zaunaba suka nufi ɗaki, har Meenal dake fashi binsu tayi kawai...........✍ *_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182