Chapter 4
Chapter 4
anan ba”. Cike da tsoro tace, “Wani abune ya faru kuma? Ko Innace tsiyar tata ta motsa yau?”. “To ba'ace ba dai Gajeje. Ƴar uwarkice ta dawo cikin wani yanayin da sam ban gane masaba. Yanzu haka na barota a gida tana maɗoɗowar yunwa. Gashi kuma naga ran Asabe a ɓace yake, dan ko uffan taƙi hiɗi mani, kinsan kuma bata barin kowa ya hiɗi yanda akai ko?”. “Wai Baba kana nihin Zinni ce ta dawo gida?”. Da damuwa ƙarara a fuskarsa ya ɗaga mata kai. Zanen kanta ta gyara kawai rai ɓace tace, “Muje baba. Dan inna zumace sai da wuta. Karta sake bi ta hanyar da tabi a baya ta maidata wani gun kuma”. Sosai yaji daɗin hakan. Dan haka suka kamo hanyar komawa Danya suna tattaunawa akan matsalar Inna Asabe da halin da Zinneerah ke ciki a dalilinta. ★★★ Baba da Gajeje sun iske ƙofar gidan a yamutse da hayaniyar Inna da wasu a mazan maƙwafta da suka kasa haƙuri suka tanka mata akan dukan Zinneerah da tahau yi tun bayan barin Baba gidan. Yayinda Zinneerah ke gefe tana murƙususun ciwon ciki. Ran Gajeje a ɓace da halin mahaifiyar tasu ta shiga cikin rikicin da ƙyar ta lafar da kowa. Kusan minti talatin aka samu wajen ya nutsa. Inna ta shiga gida mutanen dake a ƙofar gidan kuma kowa ya kama gabansa ana zagi da ALLAH wadai da halin Inna Asabe na rashin tausayi. Sai a lokacin Gajeje ta samu damar kama Zinneerah dake kwance gefe buɗu-buɗu da ƙasa tamkar an tonita a rami. Gidan ta shiga da ita, Inna zata fara sabuwar jaraba Gajeje ta haɗe fuska tana faɗin, “Innarmu! Innarmu!”. Shiru tayi saboda sanin halin babbar ƴar tata itama. Sannan duk yanda takai ga hawa akan masifarta da Gajeje tayi magana bata iya cigaba saboda wani dalilinta daba kowa ya gama saninsa ba. Itama Gajejen bata sake cewa komaiba sai kallon Tinene ƙanwarta tayi. “Ke Tinene ɗaukamin karauni a ɗakinku”. Baki Tinene ta cika da iska tana ƙunƙuni, sai dai kuma babu damar ƙinyi. Fuuu ta shige ɗakin kwanansu da ada can shine ɗakin mahaifiyar Zinneerah kafin tabar gidan. Wata tsohuwar tabarmar karauni ta ɗakko zuwa gindin bishiyar mangwaro dake a kusan tsakkiyar gidan. Zinneerah na zaune an jinginata da bishiyar, Baba na daga tsaye gefenta kaɗan yana kallonta dayin hawayen zuci. Sai Gajeje dake can kusa da Inna a gaban murhu taɗan kara ruwa jikin wutar ɗan waken Inna na saidawa dan yay ɗumi. Gidan yay tsit babu mai cewa uffan duk da kuwa kowa nada abin cewa a bakinsa. Musamman ma Baba, sai dai tsoron matarsa Inna bazai barsa iya furtawaba duk da tsantsar tausayin ƴarsa dake ransa. Gajeje ta juye ruwan ɗumin a wani roban wankansu ta sirka takai banɗaki tazo ta kama Zinneerah ta miƙar. Har banɗaki ta kaita da kanta. Bata wani tsaya jan zance ba ta ɗaurayema Zinneerah jiki da kanta duk da kuwa tanata mammaƙewa dan nauyin yayar tasu da suke kallo tamkar uwa a garesu. Tinene ta ƙwalama kira ta kawo mata zani da riga. Sosai Zinneerah taji daɗin jikinta da wannan wanka. sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi da lumshe idanu. Baba dake tsaye har yanzu da kansa ya gyara mata tabarmar ta kwantar da ita. Inna na kallonsu a kaikaice, watsama Baba wata uwar harara tayi tana yin ƙwafa. Sai dai kuma batace komaiba ta cigaba da tsame ɗanwaken ta. Duk da Gajeje taga harar da Innar tasu taima mahaifinsu bata tankaba. Sai ma kwance gefen zaninta tayi tana ciro nera hamsin data sha ƙudindina. “K Tinene zokije nan wajen Dijen kamaye ki sayo mani kunu da suga”. “Yaya Gajeje tallafa zan ɗauka, kina ganin Inna harta gama kwashe ɗanwake, gahi Sa'a bata dawo ba, Karima kuma na rimaye”. Wani mugun kallo gajeje ta watsamata, a hasale tace, “Ni kike hiɗima haka Tinene?”. Kafin Tinene ta bata amsa Inna ta dubesu a hasale. “Wai Gajeje miyasa ke baƙya son zaman lahiyane? Ai gaskiya Tinenen ta hiɗi, inke idonki bai gane miki na kwashe ɗanwakenba”. “To amma Innarmu koda shirin ɗaukar ɗanwaken take nanda gidan Dije ne zai gagareta zuwa ta sayo mani kunu? Kenan iya shegen da sukema kowa nima ya hwara zuwa bisa kaina?”. Yanda Gajeje ke magana a hasalene ya saka Inna cewa, “K Tinene amshi ki sayo mata, ni bansan wani kace-nace”. Tinene na faman tunzura baki da ƙunƙuni tazo ta amshi hamsin ɗin ta fice bayan ta ɗauki wani tsohon kofi. Babu jimawa sai gata da kunun kuwa. Kusan tare suka shigo da Sa'a ɗauke da ƙaton botiki mai ɗauke da sauran gyaɗa da riɗi da taje talla. Da sauri ta ƙarasa shigowa tana fadin, “Kai, Kai, Zinni! Yaushe kika dawo?”. Murmushin ƙarfin hali Zinneerah taima Yayar tata da itama ke ƙaunarta a gidan, sai dai kuma ta kasa bata amsa sai Yaya Gajeje ce dake zuba suga a kunun da Tinene ta sayo ta bata amsar. Kafin Sa'a da hawaye suka cikama ido tace wani abu Gajeje ta maida hankalinta ga Tinene. “K samo mani lidde”. “Mu bamu da lidde nan gidan”. Cewar Tinene tana murguɗa baki. Jikake bamm! A goshin Tinene, Gajeje ta jefa mata murfin kwano dake kusa da su. A take ta zube ƙasa ta fara kururuwar ihu kamar wandda aka kashe. Inna ta saki kwanon yaji a ƙasa ta nufi ƴar tata da sauri. “Gajeje kashemin yarinya zakiyi akan wannan sheɗaniyar yarinyar data gudu yawon tambaɗarta?”. “Kaɗanma na mata Innarmu”. Gajeje ta bata amsa rai ɓace. Cikin raɗa-raɗa Sa'a data je ta ɗakko mata ludayin tace, “Yaya Gajeje ki ƙyalesu dan ALLAH, karki tahi gida a huce kan Zinni. Kindai san halin Innarmu ai”. Shiru Gajeje tayi bata tankaba. Baba ma dake tsaye har yanzu bai tanka musunba, hasalima hankalinsa na kan Zinneerah da ke shan kunun cike da zalamar yunwar da takeji. Zuwan Gajeje gidan ya matuƙar taimakawa wajen bama Zinneerah kulawa. Inda kuma ya katange duk wani bala'i da masifar dake cin Inna a rai. Dan bayanma ta kammala saida ɗanwakenta su Tinene sun ɗauka wani sun wuce talla zani ta ɗauka ta fice gidan wai taje barka wani ƙauye dake can gefensu shima. Hakan yama baba daɗi sosai. Dan koba komai sa samu damar jin yaya akai Zinneerah tabar gida a kwanaki ashirin da shida da suka shuɗe, da kuma yanda akai ta dawo musu yau a wannan halin?. Suna zaune shi da Gajeje suna tattaunawa akan hakan Zinneerah dake barci tun ɗazun ta farka a firgice da ciwon ciki. Duk kanta sukayo suna tambayar ko lafiya?. Bata iya amsasuba sai da ya lafa mata. Ta share hawayen dake sauka a kumatunta. “Yaya Gajeje cikina kemin ciwo”. Basu kawo komai a ransuba sai yunwa. Dan haka Gajeje tace, “Zinni yunwace nasani. Sannu kinji. Idan zaki iya tashi kiyo alwala kiyi sallar azahar da la'asar sai kizo ga abinci kici”. “Zan iya yaya Gajeje” Ta faɗa tana maida kallonta ga baba dake kallonta cike da raunin zuciya dana idanu. “Baba ina wuni”. Murmushin ƙarfin hali yay mata da shafa kanta. “Lafiya lau Uwata yaya jikin?”. “Da sauƙi baba”. “To madalla. tashi kiyi sallar maraice na ƙara yi”. Bata musaba ta miƙe. Jin gidan shiru ya sata sanin Inna da su Tinene duk sun fice.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182