Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 43

Chapter 43

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

iyaye aynun. ★★★★ Tunda suka baro gidan babu wanda ya iya yin magana, sai da suna gab da shiga anguwarsune ma Gwaggo Maryama tai ƙarfin halin tambayarsu ina suka baro little kuma?. “Gwaggo ai baida lafiya an kwantar dasu a asibiti shida Umma”. Abdull ya bata amsa da damuwa a fuskarsa. Saurin juyowa Mmn Sadiq tai ta kalli yaron, kamar zatai magana sai kuma tai shiru ta maida kanta. Fahimtar hakan da Abba yayi ya sakashi faɗin, “Ban faɗa muku bane dan banason raba muku hankali biyu, amma jikin nasama Alhmdllh dan yanzu haka sun koma gida ta kirani cewar an sallamesu ga Naziru yaje zai maidasu gida. Bakomai ke damunsaba kuma sai zazzaɓin haƙora”. Addu'ar samun ingattacciyar lafiya sukai masa ita da Gwaggo Maryama. Daga haka suka ƙarasa gidan. Sai da sukayi sallar magriba suka huta Maman Halima ta shigo gaishesu ɗauke da Little daya rame sosai saboda yasha jiki. danma ALLAH yayisa mai kwaramniya ga karfin hali da akasan duk yaro da shi. Ƙiri-ƙiri sai gashi yana musu ƙyuya. Yaƙi yarda da kowa sai Zinneerah da kunya ta rufe kamar ƙasa ta tsage ta shige. Badan tasoba dole ta amshesa. Aiko ya wani lafe a jikinta yana kallon su Gwaggo Maryama dake jan kafarsa cikin tsokana tana fadin, “Aiko yaro nama fasa auren. Na maka saki goma sha biyu ni da kai baram-baram”. Dariya Mman halima tai tana tare masa. Ana cikin haka Maman Sakina ta shigo da yaranta wai zatai musu gaisuwa. duk da bataje can gidanba sai mmn sadiq bata nuna mata komaiba ta amsheta hannu bibbiyu suka gaisa tai musu godiya. ______________,★ Har washe gari babu wanda ya sake tada maganar komawar Zinneerah gidan hajiya Iya. Dan shi Abba ma ya fice kasuwa abinsa tun safe. Sai bayan sallar la'asar ne Mmn Sadiq da abin keta cin ranta dai ta tunkari ƴar uwarta da maganar. “Maryama nifa inaga kodan matsalar gidan nan zanbar yarinyarnan ta koma wajen Gwaggo, sai dai kuma idan na tuna kar ace dansu masu arziƙi ne mukai haka abin na damuna. Sannan shi kansa Yaya na fahimci baison maganarnan”. Murmushi Gwaggo Maryama tayi tana gyara zamanta sosai. “Yaya Hauwa nifa kin ganninan babu abinda ya dameni da cewa ta mutane. Abinda duk ra'ayina ya bani na kuma ji raina ya aminta da shi kuma bai saɓama addinina ko al'adata ba to tabbas yinsa nake dan bama kaina farin ciki. Shi ɗan adam babu wani abu da zakayi a rayuwa ƙyaƙyƙyawa ko mummuna da zai iya gani bakinsa bai tankaba koda kuwa shi a tare dashi akwai abinda yafi naka muni ɗin da ƙyau. Dan haka ajiye batun cewa na mutane muyi abinda ya cancanta. Tun jiya nima cikin nazarin maganar nakeyi da shi Yaya kansa. Shi kawai abinda na fahimta da shi gani yake kamar za'a nuna gazawarsa akan riƙon Zinneerah tunda ba shine ya haifetaba. To amma abinda bai tunaba kuma shine sufa mutanen nan bawai sunsan bama shine ya haifitaba. Sai dai ni har cikin raina na yarda da komawar Zinneerah can gidan kodan wannan fitinanniyar matar tasa dake ganin Yayan ne kawai keda arziƙin da ake zuwa a ci”. “Maganganunki duk suna a kan hanya Maryama. Harga ALLAH inason basu ita domin ALLAH da suka roƙa da kuma darajar zumincin da suma sukayi dan shi. sai dai inason tai nesa da su Saude kodan ɓata mata suna da suke a anguwatnan miji zaima Zinneerah wahalar samu. Dan damafa ni ko wannan bata tasoba nayi niyyar ta biki can ku zauna har muga abinda ALLAH zaiyi”. “A to tunda hakane a bani abata mu tafi”. Gwaggo Maryama tai saurin faɗa tana dariya. Itama Mmn sadiq dariyar tayi. Haka suka cigaba da tattaunawa har tsawon wani lokaci kafin subar maganar da nufin jiran dawowar Abba yau su tunkaresa da batun. Zinneerah da batasan mike faruwaba tana can ɗaki da Little wanda a yanzu yake maƙale mata baya yarda da kowa a gidan sai ita da Gwaggo Halima. Sai su Sadiq idan yaso. Makarantama yau da zata tafi kuka yayta zabgawa sai daga baya ya haƙura bayan yayi barci ya tashi. Wauta da ƙuruciyar dake tattare da ita kuma yasa bata ɗauki hakan komaiba saima tausayin yaron da ƙaunarsa dake ƙara ratsata. Maganar komawa gidan Hajiya Iya kuwa bata damuba ba kuma ta mantaba. Sai dai bata wani ɗaukesa da muhimmanci ba balle taji wani abu a ranta game da hakan. _________________★ Koda Abba ya dawo gidan sai da Mmn Sadiq ta bari yaci ya ƙoshi ya nutsu sosai sannan ta tunkaresa da zancen kasancewar yau itace dashi dama. Shiru yay mata tamkar baijitaba. Ita kuma tunanin baiji ɗin bane ya sata sake maimaitawa kai tsaye. Sai dai yanda ya sake tsuke fuska ya saka tasha jinin jikinta kuma. Bai kulataba sai da ya mula dan kansa sannan ya fara magana a ƙufule. “Hauwa'u kun shirya hakanne dama saboda abinda ya faru a gidan nan kwanaki shida da suka wuce komi? Shin halin Saude ne baki saniba a gidan nan ne? Da har zaki yanke hukuncin rabani da Zinneerah bayan ni har cikin raina ɗaya na ɗauketa da duk wani yaro dake a gidan nan”. “Yaya kayi haƙuri dan ALLAH, sam ba yanda kake tunani baneba. Ni abinda yasama kaji namaka magana saboda mu toshe ɓarakar da dangin mahaifiyarmu ke ganin mahaifinmu ne ya assasata. Su daina ganin tamkar muna gudunsune. Sannan baiwar ALLAHn nan ka duba yanda suka ɗauka Inno, wandama bai saniba zai ɗauka itace ta haifi Hajiya Iyan ai. Wlhy na tabbata da ace banan ta kawo Inno har ALLAH ya ƙaddara rasuwarta ananba da sai munyi kuka bana wasaba akan wannan rasuwar. Yanda zuminci ya taɓarɓare kowa zagayewa zaiyi yabar Buba da gawar Inno, da kuma sun bizneta su kama gabansu su barmu. Amma yanzu kaga yanda suke tururuwar zuwa nan hardama waɗanda bakai zaton ganiban. Amma kayi haƙuri nayi kuskure, dan babu yanda za'ai Zinneerah ta koma can bada yardarkaba”. Numfashi Abba ya sauke yana ɗan jinjina kansa. “Maganarki akan hanya take Hauwa'u, ni kaina naji daɗin wannan karamci da suka nuna akan marigayiyar, dan sun nunama sauran dagi su basu manta alkairin Inno ɗinba garesu har yanzun. Badanma ALLAH bai ƙaddaraba kinjifa maganar kaita india da suka fara. Da ace masu kuɗi haka suke daraja zuminci fiye da dukiyarsu dake tsone idonsu lallai da bamu lalace hakaba. Ace dan ALLAH ya baka wani abin jin daɗin duniya kakoma ƙyamar ɗan uwanka baka ƙaunar ya raɓeka. shiko yana gudun raɓar takane saboda karka wulakantashi. Kaiconmu da fifita abinda zai halakamu sama da abinda zai kaimu aljanna”. “Amin ya rabbi Yaya. Al'amuran kam sai dai addu'a. Ni kaina halayyar mutanen nan ta zaburar dani wani muhimmin abu insha ALLAH”. “Ai haka akeso dama. idan kaga wani ya aikata alkairi kayi ƙoƙarin koyi da shi, ka kuma nisanta kanka ga mai aikata mummuna. Dan masu iya magana kance zama da maɗaukin kanwa shike kawo farin kai”. “Sosai kuwa Yaya, ALLAH kai riƙo da hannayenmu”. “Amin. To amma nima kuma sai a duba ni dan har cikin raina inason zaman Zinneerah tare damu kodan kansu ya haɗu da sauran ƴan uwanta. Gashi kuma inajin matuƙar kunyar mutanen nan wlhy, yanzu hakamafa ɗazun sai da Alhaji Kabir ɗin ya kirani

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182