Chapter 130
Chapter 130
mike damun kanki? A ganina kamata yay ki nutsu ayi magana ta fahimta amma kinzo kinama mutane shirme. Kifa sani yanda kike da haƙƙi akansu Adilah haka shima mahaifinsu keda haƙƙi a kansu, yakumayi iya bakin ƙoƙarin sa wajen yimiki kawaici akansu, ai idan kinason yaranki su kasance dake basai ta hanyar ƙarfi da iko ba tunda suma sunsan ke uwa ce a garesu. maimakon ki damu dajin ta yanda akai Abdul-Mutallab ya samar da yarog yarinya a waje ke damuwarki kawai ƴaƴanki zasu suɓuce miki, haba wane kalar son kai ne wannan?”. Kuka sosai Mammah keyi, tace, “Haba Addah kinajinfa yanda suka haɗa kai zasumin taron dangi, taya zasu ma yaro aure bada saninaba haka ake rayuwa?......” “Ke sanda kikai masa aure bada saninmu ba wace gadarace baki manaba”. Baffah ya katseta a fusace. Ransa a ƙololuwar ɓace ya cigaba da faɗin, “Hindatu idan kin manta bara na tuna miki, matar da Adnan ke aure karki manta sai ana gobe ɗaurin aurensa da ita kika faɗa mana, amma duk da rannmu ya ɓaci Inna ta tilasta mana haƙuri mu barki tunda aurene, yarinyar kuma ƴar uwarki ce. Haka muka danne zukatanmu muka amsheta a cikinmu da hannu bibbiyu amma ki ka ɗorata akan keken ɓera wajen nuna mata muɗin mutanen banza ne bama sonki da ƙaunarki, sai kuma a yanzu dan mun maimaita abinda kika aikata zakiji zafi? Ai dama na faɗa miki ƴaƴana sai sun dawo gareni tunda ke bakisan mutunciba, burinki kawai ki nisantasu dani da ƴan uwana to muzuba mu gani ɗan halak ka fasa ni da ke a garin nan”. Mammah zata sake magana Mahma ta dakatar da ita da sauri. “Kuyi haƙuri Kabeer, tabbas Hindatu ta aikata laifi, amma inason ku fahimceta itama, kunsan a duk sanda mace ta rabu da uban ƴaƴanta babbar fargabarta shine barin masa ƴaƴanta wata tazo ta cuta musu koshi uban ya nisantasu da ita. Na tabbata wannan shine fargabar Hindatu tun a wancan lokaci da yanzu haka. Amma bawai hakan na nufin ina goya mata baya akan abinda takeyi nason ganin ita ta nisantasu da ku ba duk da kawaicin da kukai mata na tsayin shekaru. Ina son dan ALLAH a wannan gaɓar mu haɗu wajen yafema juna, mukuma fahimci juna dan mu duka munada ƙarfin iko akan Adilah da Abdul-Mutallab. Sai dai hakan ba yana nufin mu cigaba da raba hankalinsu ba da ƙarfin ikon da ALLAH ya bamu akansuba na iyaye”. Tsit falon yayi dan maganar Mahma tayi tasiri a zukatansu sunkuma san gaskiya ta faɗa. Hakan yasa AK dake tsaye tun ɗazun daga bakin ƙofa ya ƙarasa shigiwa. Zama yay ya gaidasu batare da ya yarda ya haɗa ido da kowaba dan ransa a jagule yake babu daɗi. Mahma ce ta dubesa da kulawa, “Abdul-Mutallab nasan duk kaji mike faruwa. Sai dai jin naka bashine mai muhimmanci ba, a yanzu mu munfi buƙatar son sanin a ina aka haihu a ragaya game da haihuwar yaro mai sunanka?”. Iska yaɗan furzar kansa a ƙasa. “Mahma wlhy nima ban saniba”. “Kamarya baka saniba, a ruwa ake shan ciki balle kace mana itama acan tasha?”. Aunty Zakiyya tai magana karon farko tun shigowarsu a hasale “Tabbas ba'a sha, amma inaga itakam dai acan ta shashi. Dan ni dai ban taɓa tarayya da wata mace bayan matata ba ALLAH shine shaidata. Sannan ban taɓa ganin yarinyarnan da idanuna ba sai a gidan nan. Amma kuma tabbas na yarda Abdul-Mutallab ɗa nane, ina kuma kan binciken ta yadda aka samar dashi insha ALLAH”. Shiru falon yayi tsahon lokaci, sai Uncle Ahmad da wani tunani yazo masa a zuciya dan shidai shedane akan AK bai iya ƙaryaba yace, “Abdul-Mutallab maganar nan ba wadda mutane zasu ɗauka bace balle su fahimceka. Amma sai nake tunanin ko kun taɓa yunƙurin yin wannan dashen na zamani da aketa nusar al'ummar musulmi rashin anfaninsa?”. A karon farko AK ya ɗago ya duba Uncle ɗin nasa da rinannun idanunsa. Hakama Mammah da aunty Zakiyya a razane suka dubi Uncle Ahmad har hakan ya bama Mahma da Hajiya iya mamaki. Da sauri AK ya girgiza masa kansa. “Wlhy Uncle ni ban taɓa son hakanba dan bayama birgeni, na tabbatar idan ALLAH yaso zai bani, da bai baniba kuma ƙila haka shine mafi alkairi a gareni”. Cikin jinjina kai Uncle Ahmad yace, “Na yarda da kai Adnan dan baka taɓa min ƙaryaba, sai dai wannan al'amarin na buƙatar bincike, musamman ga matarka kota taɓa wannan yunƙurin aka samu kuskuren ɗaukar sparm ɗinka aka saka ga ita yarinyar bada sanin ku ba ku duka tunda wannan matsalar kan faru saboda son zuciyar wasu likitocin, kokuma daga likitocin matsalar take baki ɗaya”. Wani irin mugun tarine ya sarƙe aunty Zakiyya har sai da aka bata ruwa. Ita kanta Mammah sai zufa take gogewa a kaikaice. Cikin rawar murya tace, “Hakan bamai yuwuwa bane, tayaya za'ai yunƙurin hakan shi bada saninsa ba, kuma shi da ke a london yarinyar na ƙauyen katsina taya ya hakan zai faru, yadai zauna yayi tunani ko wani akasi ya taɓa faruwa”. Hajiya iya da zuciyarta keta kaikawo da nazarin kowa a wajen tace, “Inaga to wannan maganar babbace gaskiya, mu ajiyeta a yanzu idan an gama biki lafiya saimu yita a tsanake, dan yanzu haka ga Huzaifa nata kirana kunsan ana jiranmu a wajen walimar can”. Baffah da shi kansa tunanin zuciyarsa ya fara canjawa daga akalar zargin Ak da yake har yanzu zuwa zancen ɗan uwansa cikin gamsuwa yace, “Hakan shine dai-dai Inna”. Tabbas a wannan gaɓar suma su Mammah sunfi buƙatar tsayawar zancen su sami dama da sararin yin nazari, dan haka duk suka amince. Sai dai basuso zuwa wajen walimarba Mahma ta takura musu akan saifa sunjeta dole ko shima AK ɗin zaiji sanyi a ransa ai. Gudun zargin wani abu daban daga AK yasasu yarda zasuje. Dan ya tsatstsare su da idanunsa da gaba ɗaya suke a birkuce da abubuwa kala-kala da shima baisan adadinsu ba. ★★ Sun isa ƙaton hall ɗin da za'a gudanar da walima and liyafar cin abinci rana daya ƙawatu matuƙa. Ya kuma cika taf da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W). Ga manya manyan malamai da zasu gabatar da lectures. Sashin mata daban na maza daban babu ruwan wani da wani, hakkane ya samama AK nutsuwar da yake buƙatar samu. Suna isowa aka gabatar da addu'oi da suka shafi komai na rayuwa bayan ma'auratan, kafin a fara abinda ya tara mutane. Malamai sun ragargaza lectures masu ratsa jiki akan aure da zamantakewar rayuwa data saka jikin mutane da yawa yin sanyi, Zinneerah amarya da duk da basan waye mijin nataba tasha kuka itama, lectures ɗin kuma sun shigeta matuƙa. Lokacin salla nayi aka fita akai sallar zuhur sannan aka dawo aka ɗora dacin abinci, a hakanma dai malamai na cigaba da aikinsu har zuwa la'asar da aka rufe da addu'oin fatan alkairi ga ma'aurata damu da muke a gidan auren sannan aka tashi. Da yawan mutane daga nan suka fara kama gabansu, wasu kuma suka koma gidansu AK domin rakiyar amarya ɗakinta da za'ayi da wuri, duk da dai hajiya iya tace ƴan danya bazasu koma a yau ba kamar yanda suka sanar, tace su bari sai ALLAH ya kaimu gobe su da ƴan ɗan musa saisu tafi.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182