Chapter 11
Chapter 11
musawa dangin Inna. Da ƙyar Zinneerah ta iya cinye guda ɗaya sai amai. Kowa ya tausaya mata anata mata sannu. Harma wata ƙanwar Inna na cewa shawara ce a nemamata sassaƙe tasha. Itadai bata iya magana sai amsawa da kai harta samu ta koma ɗaki ta kwanta. Cikin tsoffin da sukazo daga maraba ne ɗaya ta dubi Yaya Atine dake gefenta tana shayar da ƴarta da take goyo. “Niko nace Atine”. “Na'am Gwaggo ladi”. Yaya Atine ta amsa tana kallonta tana maido hankalinta gareta. Wadda aka kira da Gwaggo Ladi tace, “Wanan ƴar uwar taku tayi aure ne dama bamu da labari?”. Da mamaki a fuskar Yaya Atine tace, “Gwaggo wai kina nufin Zinneerah? Indai itace batai aureba. Yaya zatai aure baku jiba”. Cikin waro idanu na alamar gulma tace, “Kanjakar ubancan kayyasa. To lallai idon Asabe a rufe yake a gidan nan bata bahimtar komai daɗa”. “Gwaggo miyasa kika hiɗi haka”. Yaya Atine ta sake faɗa tana duban Gwaggon nasu da ƙyau. “Uhm-uhm babu komai Atine. Kawai dai naga abinda yafi ƙarhin ganina ne. Dan wannan ɗiyar ciki ke ga jikinta, harma ya tasa gashi nan”. A razane Atine ta saki ƴarta ƙasa da dukan ƙirjinta tace, “Gwaggo ciki?!! Zinni ɗince ke da ciki!!?”. Yanda tai maganarne ya jawo hankalin sauran mutanen dake a gidan kansu. Ga ƴarta data saki ƙasa ta tsage da kuka saboda zafin faɗuwar da taji.. Yaya Gajeje ma a ruɗe ta saki kwanon data ɗakko zata saka a sayoma Zinneerah kunu ko zata iya sha. Ta ƙaraso gasu Atine da sassarfa tana faɗin, “Atine wannan wane irin mugun alkaba'ine kike hiɗi dan ALLAH?”. Da sauri Atine tace, “A'a yaya Gajeje bafa ni na hiɗi ba....” “To waya hiɗi?”. Gajeje ta katse ƴar uwar tata. “Kunga bafa zancen hayaniya bane ba Gajeje. Ku kira yarinyar tazo nan”. Gwaggo Ladi duk ta katsesu. Zinneerah na ɗaki kwance tana sauke numfashin wahalar amai da tayi wata cikin ƴan bikin ta shigo ɗakin tana ƙwala mata kira. Miƙewa tai daga kwancen da take a razane tana dubanta batare data amsaba. Matar tace, “Kinga taso ana kiranki a waje”. Batare da tunanin komaiba Zinneerah ta miƙe ta biyo bayanta cike da dauriya. Tana fitowa gabanta ya faɗi ganin kowa na gidan ya zubo mata idanu, har waɗanda ke a cikin ɗakin Inna duk sun fito tsaye cirko-cirko. Rasa ina zata dosa tayi dan ruɗiya. Sai da yaya Gajeje tai ƙarfin halin kiran sunanta cike da tashin hankali. Dan ita kanta kam zuciyarta ta fara gaskata zancan tsohuwar saboda wani irin canjawar da Zinneerah tayi, wanda ada sam hankalinta bai taɓa bata abu makamancin ciki ba akan canjin.... Ƙarasowar Zinneerah inda suke ne ya katse tunaninta. Tsohuwa Gwaggo Ladi ta kamo hannun Zinneerah ta buɗe tafin tana kallo, ta kuma ɗago fuskarta ta gwale mata idanu nanma. Sai kuma tace ta buɗe bakinta ta turo harshenta waje. Ita dai Zinneerah babu musu komai yi take cike da tunanin ko wani ciwone ya kamata. dan a watani uku ɗin nan data dawo gida ƙwarai da gaske tanajin canji sosai a jikinta wanda batasan kansa ba..... “Wlhy wannan yarinyar ciki ne da ita Asabe. idanma baku yarda ba ku kaita ayi gwaji wajen likita”. Zancen Gwaggo Ladi ya katse tunanin Zinneerah. Yayinda a take gidan ya harmutse da salllami da gulma. Sam Zinneerah bata fahimci komai a zancen Gwaggo Ladi ɗinba, duk da yanayin mutanen dake gidan ya sake sakata a tashin hankali. A haukace Inna tazo ta kai hannu zata kai mata maguza wata ƙanwarta ta tare tana janye Zinneerah ɗin. “Haba Asabe, ita dake cikin wannan halin zaki kaima wannan bugun? Kamata yayi a bita a sannu asan inda al'amarin ya hito ai ko?”. “A ina ya hito banda wajen yawonta na tazubar Haule. Idan na hiɗi ya rinyarnan nabin maza sai ace sheri nake mata dan ban haiheta ba. Kwanan nan fa tahiya tai babu wanda yasan ina taje kusan mako huɗu sannan ta dawo. Amma da yake ubanta shashasha ne bai ɗauki wani mataki a kantaba. Wace irin makauniyar rayuwace wannan? Na rantse da ALLAH bata zaunamin gida da cikin rariya. Sai dai ta koma can gidan wanda ya ƙunsa mata masihwar su ƙarata tambaɗaɗɗiyar yarinya”. Yanda Inna ke masifa kamar zata haɗiye harshentane ya saka gidan yin tsit kowa yana saurarenta. Yayinda hajijiya take juyama Zinneerah garin a hankali. Babu zato sai ganinta kawai akai ƙasa ta zube. Babu wanda yay yunƙurin taimaka mata sai Sa'a dake kuka tun farkon fara maganar, ta taho da gudu ta durƙusa gabanta tare da ɗagota jikinta tana jijjigata. Tsawa inna ta daka mata akan ta tashi a wajen kota tsine mata. Cikin kukan Sa'a ke girgizama Inna kanta. “Haba Innarmu! Haba Innarmu!. Wlhy Innarmu Zinni ba ƴar iska bace. Wlhy Zinni bata iskanc......” Ta kasa ƙarasawa saboda kukan daya sarƙeta. Yaya Gajeje ce ta tako inda suke itama tana share hawaye da bakin zaninta. Ta durƙusa ta kamo kan Zinneerah dake a jikin Sa'a ta maido kan cinyarta tana fashewa da kuka maiban tausayi..... Bayyana irin tashin hankalin da Zinneerah ta tsinci kanta a cikin wannan rana da duk wani masoyinta ma ɓata lokacine. Hatta da maƙiyan nata jimami suke nunawa a zahiri, a baɗini kam ransu fari tas musamman ma Inna da ke ganin fatanta ya tabbata. Kamar yanda Zinneerah ta yanke jiki ta faɗi sai da aka zuba mata ruwa haka Baba ma da labarin ya riskesa tamkar saukar aradu ya zube babu numfashi sai da aka zuba masa ruwa ya farfaɗo da ƙyar. Kafin wani dogon lokaci garin ya ɗauki zance Zinneerah tayi cikin shege. Tofa abin nema ya samu ga masu ƴancin faɗin albarkacin baki. Wasu suce mugun alkaba'in Inna ne ya kamata, wasu suce wahalar da Innar ke batace ta kaita da fara bin mazan ai. Wasu suce babu wani dama halintane. Dan kawai tana shan wahala a gidansu sai ta bi maza. Kowa dai da inda nasa furucin ke sauka. Duk da ba yaune ainahin ɗaurin aure ba sai ga mutane na tururuwar shigowa gidan gulma da son ganin ƙwaƙwaf. Ƴammata kam harda waɗanda Karima ma bata gayyata zaman ƙunshin ba sai gasu. Inna kam tanata zabga bala'i sai Zinneerah ta bar mata gida ƴan uwanta na tausarta. Yayinda Zinneerah ke a ɗakinsu tare da Baba da Yaya Gajeje da Sa'a. Sai wasu ƙanen Baban maza su uku da mace ɗaya sun turketa akan saita faɗa musu a ina ta samo wannan jidalin?… Kuka Zinneerah keyi tamkar numfashinta zai rabu da gangar jikinta. A karo na babu adadi ta sake faɗin, “Wlhy! Ta-kwaran-kwatsa Kawu ban taɓa aikata iskanci ba. Wlhy ni banda ciki.” Cikin daka mata tsawa Kawu haruna yace, “Kinci uwarki Zinni. Su waɗanda sukace kinada cikin zasu maki ƙarya kenan? Bayan duk ga alamomin mai juna biyu tattare da ke. Idanfa baki hiɗi mamu wanda kukai wannan lalatar to kuwa kina barin garinga kije can ki nema wasu iyayen bamuba. Dan bamu zama da mai halin banza cikin zuri'armu kau...” “Ai bama barin gariba ni nan da kake gani rami zansa amani na bizneta da ranta har sai ta mutu idan bata hiɗi mamu gaskiya”. Tirƙashi. Tunfa su kawu nabin Zinneerah da lallami akan sanin gaskiyar magana har takai Kawu Sabi'u da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182