Chapter 40
Chapter 40
tasa ta sake share hawayen nata, sai kuma ta kalli Alhajin tana murmushi. “Shike nan ɗana ALLAH ya tabbatar da hakan. Tunda harkun gane kunyi kuskure na haƙura. Amma dan ALLAH ku gyara dan shi zuminci babban abune mai girma da ta silarsama za'a iya zuwa aljanna. Mu daina biyema sharrin sheɗan dana zamani zukatanmu nayin nisa da juna. Ina daɗi ace ƴaƴan Hafsat basusan inda nakeba saboda iyayenmu basa raye. Wajen gwaggo kawai kuke zuwa”. “Tabbas ba'a ƙyautaba Gwaggo. Amma dan ALLAH ayi haƙuri. Kamar yanda ya faɗa insha ALLAH zamu gyara. Wlhy zuwanma da kikaga banyiba nima rasa takardar da aka rubutamin adireshin da lambar wayar nayi. ALLAH kuma bai ƙaddara duk sanda na shigo bauchi na sake amsar wani adireshin ba a wajen Buba”. Hannu Hajiya Iya tasa ta kamo na Mman sadiq mai maganar, sai kuma ta kamo na Gwaggo Maryama duk ta haɗa cikin nata tana murmushi. “Ya wuce insha ALLAH, nima namuku hakane danku ƙara sanin muhimmancin zuminci, mu kuma sake dunƙulewa tsintsiya naɗaurinki ɗaya. ALLAH yayi muku albarka kuda zuri'arku damu baki ɗaya”. Cikin jin daɗi su mmn Sadiq suka amsa mata. Daga haka aka koma gaishe-gaishe kamar ba yanzu Hajiya Iya ta gama sharar ƙwalla ba. Sai da aka gama gaishe-gaishe da tambayar jikin Inno daketa kallonsu kawai dan ko magana bata iyayi amma tana jinsu. Hajiya Iya ta koma nuna musu sauran jama'ar ɗakin. “To ga ƴan uwanku nan nasan duk baku sansuba. Waɗan nan biyun matan yayanku ne. Waɗan nan kuma ƴaƴanku ne dukansu gasu nan. Badai zaku gane lissafinba anan sai munje gida”. Su mmn Sadiq dai murmushi sukeyi cike dajin ƙaunar ƴar tsohuwar, suka sake gaisawa da waɗanda ta nuna musun. Yanda suma babu alamun wulaƙanci a garesu yasaka jin farin ciki a zukatansu Mmn sadiq ɗin. Hajiya Iya ta nuna su mmn sadiq kuma garesu suma tana faɗin, “Ku kuma waɗannan ƙannenku za'ace kenan ko. Dan ƴaƴan Yaya Hafsat ne da ALLAH yayma rasuwa babbar ƴar Gwaggo da aure ya kai can Katsina, nasan dai bazaku gaza jin sunantaba a hirata ma. mahaifinsu ne bai barsu sakewa a cikinmuba tun suna kananu shiyyasa baku sansuba basu sankuba kuma. Amma insha ALLAH daga yau kowama zai sansu ɗin”. Duk suma amsa mata sukai da girmamawa dan babu mai jayayya da ita a kaf family ɗin harsu matan ƴaƴan nata. Sallama Alhaji yay musu ya tafi saboda ganin lokaci zai ƙure masa na kasuwa. ya wuce akan zai dawo anjima ya ɗaukesu idan ya taso. Sosai su Mmn Sadiq suka tsinci kansu cikin farin cikin kasancewa da dangin mahaifiyar tasu da suka gaza samun kusanta a lokacin ƙuruciya yanda ya kamata. Dan mahaifinsu baison kaisu su sake a cikinsu gudun karsu ƙwace masa su. Sukan dai je suga Inno naƴan kwanaki su dawo. Hakan yasa ko lokacin aurensu dangin mahaifiyarsu ba kowa yazoba dan haushin babansu. Su kuma bayan duk sunyi aure rashin sabon tun farko ya hanasu sakewa dasu, dan Inno kawai suka sani da wasu tsuraru a ciki. Babban abinda ya basu mamaki bai wuce yanda zuri'ar Hajiya Iya ke tururuwar zuwa asibitin duba jikin Inno ba. Saika rantse Hajiya Iya ɗince kwance ke jiyya. duk wanda yazo kuma saita masa bayaninsu suma sai ta musu bayaninsa. Alhmdllh kuma basuga raini ko wulaƙanci ga kowaba dukda kuwa sun shaida akwai kuɗi a wannan zuri'a kodan manya-manyan kulolin abincin da ake shigowa dasu na dubiya. Har dare suna a asibitin Inno bata wani san da zuwansuba saboda zafin ciwo, sai dai binsu da take da ido da kuma surarensu. Gashi kuma ɗiyar ƴar uwarta nata kaf-kaf da abunta gwanin sha'awa. Rigimar Hajiya Iya bata basu mamakiba sai da Alhaji ya dawo ɗaukarsu bayan ya taso kasuwa. Ta tubure akan babu inda zasuje gidanta zata wuce dasu su kwana dan asibitin Nurses ke kwana da Inno. Ana cikin wannan kicimilli babban ɗan Hajiya Iyan ya iso asibitin. Dawowarsa kenan daga tafiya ko gida bai shigaba ya wuto nan dan duba Gwaggo mahaifiyar tashi, shi kuma kakarsa. Tunda yay sallama cikin ɗakin Alhaji yay suman zaune. Akan laɓɓansa ya ambaci *_“Alhaji Kabir Abdul-Mutallab Shira_* babbar magana”. Alhaji Kabir Shira da baisan da zancen zucin Alhaji ba ya ƙarasa gaban mahaifiyarsa duk da shekarunsa na girma ya kai har ƙasa duƙe yana gaisheta da tambayar mai jiki. Amsa masa take da kulawa tare da tambayarsa yaya hanya?. “Alhamdulillahi innata. Ina fatan ana samun cigaban sauƙi a jikin Inno ɗin?. Dan tunda kika sanarmin halin da kuka sameta jiya da ƙyar nai barci. Inagama zuwa Laraba insha ALLAH kawai za'a wuce da ita India”. Cike dajin daɗi Hajiya iya ke jinjina kanta. “Wannan tunanin shine dai-dai Babangida. ALLAH yay maka albarka. jikin kam Alhmdllh dan bakamar jiya da muka baro Bauchi da ita ba. Amma dai nima nafi yarda da maganar zuwa india ɗinma a duba wannan ƙafar tata da ƙyau”. “Karki damu Innata, insha ALLAHU harma nayi magana da Bashir zai fara shirye-shiyen tafiyar daga daren yau ɗin nan”. Sai da ta jero masa addu'a sosai, sannan ta nuna masa su maman Sadiq dake gaisheshi. Bayan ya gama amsa gaisuwar yaransa da suma ke cike da ɗakin mazansu da matansu. Dan dolene kazo duba Inno saboda muhimmancinta ga Hajiya Iya. Da kulawa ya amsa musu yana sauraren bayanin mahaifiyar tasa. bayan ta gama ya miƙe tsaye yana bama Alhaji hannu da faɗin, “Lallai yau ina cike da farin ciki gani ga ƙannena da ban saniba suma basu sanniba kuma. Idonku kenan a gabanmu?”. Cike dajin kunya da mamakin sauƙin kansa tamkar mahaifiyarsa suka shiga bashi amsa. shiko kasancewarsa mutum ɗan boko kansa tsaye yake masu magana har Alhajin dake mamaki da al'ajabin dama Alhaji Kabir Shiran haka yake da sauƙin kai ashe? Bazaka taɓa cewa shahararren ɗan kasuwar nan bane mai faɗa aji a cikin kano da wajenta a gabansu haka ba. Dan ya saki jiki dasu sosai babu wani alamun girman kai ko raini duk da ya gansu talakawa kuma yaune ya fara sanin nasu. Sai da suka fito zasu tafi ne dan itama ashe isowarsa take jira su tafi gida tare yakejin zancen cewar ta hana su maman sadiq bin alhaji gida. Murmushi yayi mai ƙayatarwa yana duban mahaifiyar tasa da jinjina rigimarta dason zuminci. “Innata ai ba'ayi hakaba. Nasan dai ƙannena bazasu rasa yara a gidaba. Dan haka kiyi haƙuri suje yau ɗaya su shiryo kamar zaifi”. “Uhm-uhm Babangida banyardaba. Salon suje suƙi dawowa tunda dama gudunmu sukeyi”. “A'a Inna baza'ayi hakaba insha ALLAH”. Mmn Sadiq ta faɗa da sauri. Sudai sauran jikokinta da suke asibitin dariya suketa kwasa a gefe sanin halin kakar tasu. Itafa indai akan zumincine bata da wasa. Shiyyasa su kansu suka tashi da wanan trianing ɗin nata kansu ke a haɗe bakajin wani fitina sai wadda ke a ɓoye dan ba'a rasataba musamman a tsakanin iyayensu mata. Da ƙyar dai Alhaji Kabir ya lallaɓa Hajiya Iya ta yarda akan su mmn sadiq su taho da shirinsu gobe idan ALLAH ya kaimu. Daga haka Alhaji Kabir ya buɗe mata motar da aka kawosa da kansa ta shiga, shima ƴaƴansu suka buɗe masa yana ma su Alhaji sallama da jaddada ma su mmn sadiq su taho da ƙatuwar jakka dan sai Iya tasha ziyararsu ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182