Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

har kusan sau uku. Hankalinta bai tashiba sai da suka iso taga kowa na miƙawa direba ɗari da hamsin kuɗin mota. Cike da tashin hankali da fargaba ta miƙa masa naira tamanin ɗin da suka rage mata. Wani banzan kallo yay mata sheƙeƙe yana nuna kuɗin. “Naga kina miƙamin murtala huɗu (80n), bakiga abinda kowa ke badawa bane?”. Cikin rawar murya da cikowar ƙwalla a idanunta tace, “Wlhy su kaɗaine suka ragemani, dama ɗari biyar ce na taho da ita da ga katsina, to sai naba mai ƴar ƙurƙura......” “K! dakata. Wannan damuwarkice ba tawaba. Inda kinsan baki da kuɗin mota da baki bari nayi jigilar ɗakkoki ba ai. Dan haka ni kuɗina kawai na sani ba wai yanda kika taho daga katsina ba”. Sharr hawaye suka shiga sakko mata. Ta durƙusa a ƙasa zata fara roƙonsa, hayayyaƙo mata yayi da masifa. A take hankalin mutane ya fara dawowa kansu. Ita dai duƙe take tana kuka da roƙonsa. A mutanen da suka taru wajen duk basu bata goyon bayaba. Acewarsu miyyasa bata faɗa masaba kafin ta shigo. Idan data faɗa in yaso saiya taimaketa. Suma ɗin haƙuri take ta basu ita dai, dan harga ALLAH batasan adadin kuɗin motar ba. Hakama direba da zugar mutane ke sake harzuƙawa yana mata tujara. Tun tana roƙonsu a duƙe harta koma gurfane abin tausayi. A haka wani saurayi da tausayinta ya kamashi ya ciri naira ɗari ya bama mai motar. Daga haka suka sama mata lafiya. Har ƙasa ta duka taima saurayin godiya. Yace karta damu, tadai daina shiga mota babu kuɗi. Gara ma idan bata da shi ɗin ta dinga faɗa kafin ta shiga zaifi sauƙi. Godiya nanma tai masa ta miƙe riƙe da naira talatin ɗin daya sake rage mata tunada an biya mata ɗari. A kusada ɗinma ba sanin ina zata gano hanyar garinsu tai ba. Dan tunda tasan kanta bata taɓa zuwa cikin Kusada ba. Iyakarta ƙananun ƙauyukan dake gefen ƙauyensu kawai. Tana son tambaya tanajin tsoro, ga wani azababben ciwon ciki da takeji yana taso mata kaɗan-kaɗan. Duk yanda taso cigaba da tafiya sai ya gagara. Da ƙyar taja ƙafafunta zuwa wata runfa ta zauna. Da alama runfar mai yin faci ne. Kasancewar magriba tayi harya tashi. Zama tai ta duƙunƙune kanta cikin kafafu jikinta na rawa. Ga wata irin zufa na keto mata ta ko ina saboda azabar ciwon ciki. Tun tana zaune har sai da takai kwance a wajen tana juye-juye. Bata damu da cinnakun daketa galla mata cizo ba a jiki, dan ciwon da cikin nata ke mata ya danne komai. Tsahon lokacin data ɗauka a yanayin ciwone yasa har dare ya rufa bata saniba. Sai jin garin tai ya rage hayaniyar jama'a. Ba ciwon cikin bane kaɗai matsalarta harda Yunwa da ƙishi. Dan rabonta da abincin kirki tun jiya a gidan Hajiya. Abincin da aka bata a gidan da aka kaita ƙinci tayi sosai, dan tana tsoron taci su yanke mata kanta kamar yanda zuciyarta ke bata danshi suka kaita gidan. Tashi tayi zaune a hankali tana ɗan waige-waige. Titin babu haske. hakama jama'a duk sun nufi gidajensu sai ɗai-ɗaiku. Duk yawan motoci da mashinan ɗazun yanzu babusu. Sai wasu da basu wuce uku ba. Mashinanma bazasu gaza haka ba. Sai fitilar mai shayi da take hangowa can a wajen da motocin ke tsayawa (Tasha). Komawa tai ta kwanta. Dan haka kawai taji wani shegen tsoro ya turniƙeta. Ta rufe idanunta gam tana karanto abinda ta sani na addu'a. Cikin amincin ALLAH kuwa sai ga barci ya kwasheta. Da alama hakan nada nasaba da gajiyar dake tare da ita ta wahalar tafiya da gudun da taci kafin samun Napep.. ★★★★★ Tun kiran sallar farko na asubahi ta farka da wani irin ciwon ciki. Murkususu ta dingayi tana kuka. Ta jima tana shan azaba kafin ya lafa mata. Zuwa lokacin anata ƙoƙarin shiga sallar asuba. Tashi tai a jikkace, dan yunwa takeji sosai. Ta taka a hankali zuwa inda massallacin tashar nan yake. Butocin da akai alwala ta dinga taɓawa harta sami mai ruwa. Ɗakkowa tai ta dawo wajen rumfarnan. Ta zagaya bayanta tai fitsari da yin alwala. Sauran ruwan kuma ta shanye. Sai a yanzune ta tuna ko sallar La'asar ɗin jiya batayiba. Rabonta da salla tun ta azhar da bayan idarwarta ta gudo. A take ta fara maka sallolin nan batare da tabi tsarin daya dace na mai ramuwaba. Sai da ta gama jerosu har asubahi. Zuwa lokacin mutane nata fitowa, hakama masu mashina da motoci. Da farko zaman kallonsu tayi. Daga baya kuma saita mike bisa shawarar zuciyarta. Ƙarasawa tai wajen mai shayin nan daketa ƙoƙarin ɗora tukunyar garwar shayinsa yana raira waƙar shata. bayan ta masa sallama ya amsa ta gaishesa da girmamawa dan babbane ba laifi. “Baba dan ALLAH tambaya nake?”. Ɗago kansa yay ya kalleta a karon farko. “ALLAH yasa na sani ɗiyata”. Ya faɗa da kafeta da kallon ƙurilla. Kanta a ƙasa tana ɗan juya yatsun hannunta cikin juna tace, “Baba dan ALLAH inane hanyar Danya?”. “Danya! Danya!?. To indai Danya dana sanice ta kusa da Gozarki hanyarta na nan gabas da mu”. Jin sunan Gozarki ya sata kallonsa cike da jin daɗi. Ta kaɗa kanta fuskarta na sauyawa alamar farin ciki tace, “Eh itace baba”. Yace, “To zaki zauna ki jira masu mashina dake shiga kenan. Idan kuma bazaki iya jiraba ki samu mai mashin anan ki biyasa talatin ya kaiki ainahin Gozarki ɗin anan zaki samu ƴan mashinan Danya”. Taji daɗin shawararsa. Hakan yasata masa godiya. Duk da talatin din ta rage mata a jiki, kuma yunwa takeji gara tabi shawararsa. Babu wani jimawa kuwa ta samu mai mashin. Kamar yanda mai shayi ya faɗa talatin mai-mashin din yace zata bashi. Sai da ta bashima sannan ta hau. Cikin mintuna ƙalilan suka iso Gozarki. Amma sai da ya kaita har hanyar ƙauyensu Danya. A take farin cikinta ya ƙara bayyana. Harta zauna da nufin jiran masu mashin dan babu wanda ya fito saboda akwai sauran safiya, sai kuma ta mike. Ba komai ta tunaba sai nasihar saurayin jiya daya cika mata naira ɗari. Bata da ko sile. Mizaisata zaman jiran mashin? Gara ta taka da ƙafa, duk da kuwa tasan akwai nisa. Amma ɗokin gata a kusa da gida sai ya gusar mata da komai har yunwar da takeji da rashin daɗin jiki. Tafiya ta fara a doguwar hanyar jan birjin da batasan iyakar lokacin ƙarewarsa ba. Ga ɗan sanyin safiya na busawa kaɗan-kaɗan. Tayi tafiya mai nisa ciwon cikin nan da batasan dalilinsaba a kwana biyun nan ya ƙara turniketa. Ƙarƙashin bishiyar dalbejiya ta samu ta zauna. Taci murƙususnta da kuka na wani lokaci kafin ta tashi ta cigaba da tafiya. Zuwa lokacin ƴan mashinan garinsu nata fitowa ɗai-ɗai da fasinjoji akai. Kafin ta gama ankara rana ta ƙwalle. Ga yunwa na cigaba da ragaɗar hanjin cikinta. Haka ta cigaba da jurewa tana jan ƙafafu tamkar mai tsohon ciki. A lokacin da dukkan wani ƙarfinta ke gab da ƙarewa ne ta hango rufin ginin makarantarsu dake da matuƙar tsaho fiye da duk gine-ginen gidajen garin. Ta saki murmushin yaƙe idanunta dake ganin duhu-duhu na lumshewa. Sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi da sauri-sauri. A hankali hajijiya ta fara juya mata hanyar, saiko gata ƙasa yaraf

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182