Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
Download Book

ƙyauran langa-langar ƙofar gidan nasu ta fito. “Uhyimm! Kaji farkar taka ta dawo kazo kenan? To billahillazi bari kaji yanzu bazan ɗauki wannan sheɗancinba. Kaji da ƙyau karna sake ganinka ƙohwar gidan nan. Idan son ganinta kake ta bika can mahaɗar taku man......” “K dalla malama saurara, tsohuwar banza da bakinta bai hiɗin alkairi sai sheri wa ɗiyan mutane. Na rantse da ALLAH kika ƙara hiɗin wani kalmar ɓatanci garemu yau sai kin kwana ofishin ƴan sanda. Ni nazo ne akan maganar jarabawa da zasu yi ta koma makaranta....” “Anƙi ta koma ɗin munahiki algungumi. Dama can niya nai na barta take zuwa. da ga yau da ga yanzu kuma na hwasa. Bata sake zuwa talla zataimani”. “Ashe kuwa zaki gurfana gaban mai-gari......” “Kaini gaban sarkin katsina ma ƙarewar mai-gari mana. Ke kuma munahika dan ubanki tashi ki shige ciki, ƴal bura'uban yarinya kulin bata iya komaiba sai janyoma mutane jidali da yaye-yaye a ƙwar gida. Zanyi maganin rawar kanki ne ai...” Yanda ta kaima Zinneerah duka ya sata miƙewa da gudu ta shige gidan. Shima Malam Badamasi bai sake tanka mataba ya bar ƙofar gidan rai ɓace. Inna kuwa masifa ta cigaba da zazzagawa har sai da Sa'a da Karima suka fito suka shiga da ita gida. Tana shiga ta hau dukan Zinneerah babu ji babu gani. Sai da tai mata lilis ta barta kwance tana numfashi da ƙyar. Zinneerah akwai taurin zuciyar tsiya da kafiya wani lokacin. Duk wahalar da take sha wajen Inna akan jima ba'aga kukanta ba idan ba ita taso ba. Idan kuwa kaga ta cika yawan kuka to lallai abin ya kai babba gareta sosai. Inna na tsaka da cigaba da jarabarta aka buga sallama. Sa'a ce ta amsa tare da nufar zauren gidan nasu dan taga wanene. (Sanƙira) mai shela idan abu ya faru a garinne tsaye yana baza babbar riga. Ta rissina tana gaidashi dan dattijo ne sosai, amma Baba zai iya girmarsa. “Tsohuwar taki na nan ko?”. “Eh baba tana nan”. “To maza sanar mata mai-gari na biɗar ganinta. inko bata zuwa cikin salama ƴan doka zasuzo su kaita da kansu. Tazo tare da ƴar uwarki zinneerah”. Sosai gaban Sa'a ya faɗi, amma ta daure cikin girmamawa ta amsa masa tare da juyawa cikin gidan. Inna ta dubi Sa'a cikin haushin Zinneerah da bai gama sakintaba tace, “Ke kuma minene kika shigo ma mutane haka? Halan shegen nanne bai tahi ba?”. Kan Sa'a a ƙasa tace, “A'a Inna. Baba Lado sanƙira ne fa, wai ana kiranki gidan mai-gari ke da Zinni....” “Ki koma ki hiɗi masa ba'a zuwa. Ba'a kamar ana zuwa ɗin...” “Inna wlhy cayay fa idan baki zuwa ƴan sanda zasuzo su tahi da ke”. Shiru Innar tayi ƙirjinta na bugawa. Ta tsani harkar ƴan sanda, dan tun sanda sukai faɗa da Lamunde aka adashi ta kaita kusada ofishin ƴan sanda akazo har gida aka kamata sai da tai kwana biyu a kusada hannunsu take shakkarsu. Ba ƙaramin wuya taciyo a kwana biyun datai wajensu ba. Amma a fili sai ta ƙyaɓe baki zata fara masifa kuma....... “Shin wai Asabe saƙon mai-gari bai iso gareki bane?”. Karaɗin Sanƙira daga ƙofar gida ya katse mata masifar datai nufin farawa. A tsorace Karima tace, “Innarmu dan ALLAH kije, tunda kinga harda ita akace kuje. Kinsanfa mai-garin nan ba mutuncine da shi ba wlhy yana iya kira maki ƴan dokar”. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ta kai dubanta ga Zinneerah dake kwance barci ya fara ɗaukarta. Tsawa ta daka mata wadda ta sakata tashi a firgice babu shiri. Ran Inna fal masifa ta tasa Zinneerah gaba Sanƙira na biye dasu suka tafi gidan mai-gari. Acan suka iske malam badamasi. Tun daga nesa Inna ta dinga antaya masa uwar harara kai kace idonta zasu zubo ƙasa ne. Shiko baima san tanaiba. Dan hankalinsa dana mai-garin da fadawa duk yana kan Zinneerah ne dake ɗingishi. “Ranka ya daɗe ka ga abinda nake hidi maka ko! Da alama bayan barowata gidan bugunta tai”. Ran mai-gari a ɓace ya wurgawa Inna mugun kallo. “Ke dai Asabe baki gamawa da duniya lahiya inhar baki canja halinki. Ace mutum shi dai baisan komaiba sai mugunta, ke shikenan zicciyarki tamkar ta kahiran hwarkon ƙarni! Kai ALLAH ya wadaran halinki wlhy Asabe. shi dai malam Sule bai sa'ar mace irinki ba. Ya auri ta arziƙin kin koreta a gidan kina kuma gallazama abunda ta haihwa. Wlhy ina mai tabbatar maki wata rana sai kinyi nadama, dan wanga ɗiya sai ta zame miki ɗan hakkin faka raina, RAINA KAMA kuma mara mutuncin mata”. Kan Inna a ƙasa tanata faman kumurya da kumatu babu damar magana, sai da mai-gari ya ƙare mata zagi tas da gorin asalinta kafin ya ɗora da gargaɗi. “To naji kince baki sake barin yarinyar nan taje makaranta. Kece kika sata ne?”. Kan Inna a ƙasa har yanzu tace, “ALLAH shi sawwaƙa ranka ya daɗe. Niko miya ja mani kai ɗiyana boko. Ubana bai saniba bani kai ɗiyana su tabaɗe. Can abokan cin mushenta ne suka kaita......” “E, ai shi abokin cin mushen nata da kike magana shine kika asirce ya koma kan ɗiyanki, kinga ashe kema abikiyar cin mushen tashi ce ko?”. Malam badamasi ya faɗa a harzuƙe cikin katse Inna. Babu wanda ya dakatar da shi, dan kowa yasan Babawo take nufi, tunda shine yay tsaye tsayin daka har Zinneerah ta shiga makaranta saboda tana so. Amma yaran gidansu daga firamari basa cigaba. Sa'a ce ma taɗan fara sakandire ɗin itama zango ɗaya tayi ta gudo saboda wani malami ya daketa Inna taje tai masa tijara tace Sa'ar bata sake zuwa. Daga nan kuma bata sake zuwan ba. Mai-gari ya cigaba da faɗin, “To bara na gaya miki a gaban kowa ki riƙe a ranki yarinyarnan zata cigaba da karatunta har sai ta gama. Ni nan mai-gari zan ɗauki nauyin ɗawainiyar karatun natama daga yau, tunda ance dama yaron daya kaita ya janye dama daga yi saboda sherin da kikayo ta ƙarƙashin ƙasa. Wlhy kinji na rantse, dai-dai da rana ɗaya yarinyarnan kika hanata zuwa makaranta sai kin kwana a kusada ofishin ƴan sanda. Kowa dake nan ya shaida”. A take duk suka amsa masa da cewar sun shaida. Banda Inna dakeji tamkar zata haɗiye zuciyarta ta mace. Zinneerah kam a ranta wani irin daɗi ne ya lulluɓeta. Sai da mai-gari ya ƙarama Inna dogon gargaɗi sannan ya sallameta banda Zinneerah. Bayan wucewar Inna Mai-gari ya shiga yima Zinneerah tambayoyi tana bashi amsa kanta a ƙasa. Sosai tausayinta ya sake mamayesu, suka shiga mata nasiha akan muhimmancin haƙuri da ribar da mai yinsa kanci a duniya ko a lahira. Sannan ya damƙa amanarta hannun malam Badamasi. Tare da tabbatar masa duk abinda za'a buƙata na ɓangaren makaranta na Zinneerah yazo gunsa ya amsa. Daga haka aka sallamesu bayan mai garin ya bata ƙyauta jikka biyu da rabi (500). Godiya tai musu sosai cike da girmamawa itama, tare da addu'oin fatan alkairi sannan suka taso ita da malam badamasi daya rakota har gida yana ƙara mata nasiha. Koda Zinneerah ta dawo gida tayi tunanin inna zata hukuntata akan abinda ya faru a gidan mai-gari. Amma sai taji shiru batace da ita ƙala ba. sai dai tana ɗaure mata fuska fiye da yanda ta saba. Sannan

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182