Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

“Dama anan ta kwana? Ko zuwa tai yanzu da sahe?”. “Anan ta kwana mana. tare da ita muka taho nan saboda gidan nasu kasan akwai mutane bazai yuwu zama gareta ba ai ko?”. “Hakane Mama”. Ya faɗa yana cigaba da lalleƙa ko'ina na sashen nata. Har takaisa ga fita nasu sasssan. Har sashen ƙaninsa Safiyanu ya tambayi matar tace bataga Zinneerah ba itakam. Bama tasan anan ta kwanaba, dan sanda su Gwaggo Laritu suka dawo gidan tayi barci kasancewar tanada tsohon ciki dama. Wani tunani ne yazoma Awwal a rai, dan idan bai mantaba dazai fita salla a buɗe yaba ƙofar zaure. Ya dawo sashen Gwaggo yana faɗin, “Lallai Mama akwai matsala. ALLAH yasa yarinyar-nan ba guduwa tai ba, dan wlhy a buɗe naga ƙofar soro yau, kuma na tabbatar bazaki kwanta baki rihe ba”. “Hazbunallah! Wlhy na rihe wannan yaron, ni kuma takaici da damuwar da suka haɗu sukaimin yawa ya sani shigewa na barta anan zaune akan idan ta gaji da zaman zata shigo ɗaki ta kwanta. Aiko zama bai ganniba bara muga ko tana gidan nasu”. “A'a mama yi zamanki ni bara inje”. “Kai dai barsa naje. Ai ba fasa zancen za'aiba cikin hikina za'a dubata. Dan dama dole naje gidan saboda aiki tunda yau ne ɗaurin auren Karima ”. Badan hakan ya masaba ya haƙura. Dan har ransa yana son Zinneerah da tausayinta matsayinsa na ɗan-uwanta. Koda Inna taje gidan bata shigaba. Dan dama batazo danta shiga ɗinba. Tayi alƙawarin har agama wannan bikin bazata leƙa gidanba. Sunbar Inna da ƴaƴanta kamar yanda tafi buƙata. Yaro ta samu ta aika ya kira mata Sa'a anan maƙauftansu da yace sun kwana ita da su Karima.. Babu jimawa kuwa sai gata ta fito tana mutstsukar ido alamar yanzu ta tashi. Ko gaisuwarta Gwaggo Laritu bata tsaya amsawaba tace, “Sa'a shiga gidan nan naku cikin hikima ki dubamin Zinneerah ”. “Gwaggo Zinni kuma? Ba'a gidanki ta kwanaba dama?”. “Nidai ba surutu na tambayeki ba, jeki fara dubawa”. Kai Sa'a ta kaɗa tana nufar cikin gidan da ƴar hayaniyar waɗanda suka tashi ta fara kaurewa. Babu wanda ta tambaya ta shiga neman Zinneerah a gidan. Sai dai babu mai ko alamarta. A rikice ta dawo ta sanarma Gwaggo Laritu. Itama sai ta sake ruɗewa...... ★★★★ A ɓangaren Zinneerah kuwa barci tasha sosai a ƙofar wannan shago har fitowar rana. Sai da mai shagon ya fitone ya tadata domin buɗewa. Tashi tai kawai ta matsa gefe batare data tanka masa ba. Shima ɗin bai tanka ba dan kallon mahaukaciya kawai yake mata duk da babu alamar datti a jikinta. Saɓanin kwanciyar yanzu kam zama tai tana kallon motsin mutane dana wucewar motoci. Babu abinda take fahimta dan ƙwalwarta ba aiki take irin na mutane ba. Ga yunwa mai tsanani na cinta. Dan haka ta ƙurama mutane dake a runfar mai-shayi dake acan tsallaken titi idanu sunasha suna kwasar hira da dariya da gaddamar siyasa. A hirar tasunema takejin sunan garin da take a yanzu mai suna Tsanyawa. Mai shagon ne ya lura hankalinta na ga masu shan shayi, haka kawai yaji tausayinta, dan haka ya fito zuwa tsallaken ya siyo mata shayin da biredi harda indomie. Wajenta ya dawo yana murmushi, “Baiwar ALLAH kina son kici ko?”. Ya faɗa yana kallonta. Batace komaiba tai ƙasa da kanta kawai tana wasa da yatsun hannunta. Murmushi ya sakeyi shima ya ajiye mata filet ɗin indomie ɗin da kofin shayin da aka ɗora biredi a sama. “Gashi to kici”. Kanta ta rausaya masa kawai taja filet ɗin nanma batai magana ba. Batai ko tunani wanke hannu ba balle yin sallar asuba. Tasa hannu ta hau cin abincin a nutse kamar yanda nutsuwa ta kasance jinin jikinta dama can. Citai ta ƙoshi tai gyatsa. Batare da wanke hannunba ma a yanzu ta zame ta sake kwanciya sai barci. Sosai tausayinta ya sake cika zuciyar mai-shagon nan. Yazo ya kwashe kayan data gama cin abincin batare da yayi magana ba. Yanzu ma barci sosai Zinneerah tasha a wajen, dan bata farkaba sai gabanin la'asar. Zama tai tana kallon mutanen garin daketa faman kaiwa da komawa, dan wajen ya sake cika fiye da ɗazu da safe. Ga titin motoci nata kai kawo suma. Mai-shagon nan ne dai ya fito salar la'asar ya ganta zaune ta tashi. Cike da tausayinta yace, “Baiwar ALLAH kin tashi ashe?”. Bata tanka masaba yanzu ma. Tadai ɗago kai tai masa kallo guda ta maida kanta ƙasa. Yanzuma kamar ɗazun murmushi yayi, ya nufi inda masu abinci suke ya siya mata yazo ya bata. Kamar ɗazu bata tankaba bakuma ta wanke hannu ba tahau ci, tare da ɗaukar ledan ruwan ta fasa tasha ta ƙoshi tana lumshe idanu. Tamkar ɗazun sai ta sake zamewa a wajen ta kwanta sai barci. Mai shagon ya dawo sallar la'asar ya ganta ta koma barci, mamaki ya kamashi sosai ganin barci bai mata wahala. Yama fahimci yunwarce ke tadata kenan. Barcin kuma shine salon nata lalurar. Har lokacin tashinsa yayi kusan ƙarfe takwas na dare bata tashiba. Ya sai abinci ya ajiye mata bayan ya rufe shagon ya wuce gida. Zinneerah bata farka ba sai kusan sha biyun dare. Yanda ta tashi tana riƙe ciki da matse fuska zai baka tabbacin yunwace. Idonta na sauka akan roba rufe da leda tai saurin jawowa kuwa. Ganin abinci jikinta har rawa yake ta hau ci. Sai da ta cinye tas tasha ruwa sannan ta miƙe tamkar an tsikareta. Jakkar kayanta ta ɗauka ta fara tafiya tamkar daren jiya dan jitai gaba ɗaya nanma ta tsanesa. Burinta kawai ta ƙara gaba tai nesa da garin na Tsanyawa. Tafiya take cikin gushewar hankali da tunani tamkar daren jiya. Gashi abin tashin hankalin yau a kan titi ne. Sauƙinma darene babu yawan mitoci sai jefi-jefi. Haka dai ta cigaba da nausa kanta cikin kariyar UBANGIJI a wannan dare ma..... ★★★ Hankalin kowa ya tashi na rashin ganin Zinneerah ɗin, dan Gwaggo Laritu kasa haƙurin ɓoye rashin ganin nata tai sai da ta fasa. A take aka shiga nemanta lungu da saƙo na garin, sai dai ganin har wani daren ya sake rufawa kowa ya fahimci dai da gaske Zinneerah ta sake guduwa kamar yanda Inna ke faɗi cike da gadarar tabbatarwa tana dariya kuma. Kuma duk da tashin hankalin rashin ganin Zinneerah ɗin a haka aka ɗaura auren Babawo da Karima. Aka kuma kaita gidan mijinta a wanann daren. Dan zasu fara zama anan Danya kafin su wuce Kaduna kamar yanda ya faɗa. Washe gari an sake tashi da neman Zinneerah a ƙauyikan kusa da su har zuwa kusada ko za'aji labarin tahau mota zuwa wani waje. Babu wani labari makamancin an ganta da suka jiyo. Haka suka dawo gida cike da damuwa da tashin hankalin wannan al'amari. Ran Inna ya ɓaci dan ba haka tasoba. Sotai ace kowa ya dinga zagi da faɗin Zinneerah guwa ta sakeyi wajen karuwancinta. Amma sai taga saɓanin hakan kowama sai tausayinta yakeyi da damuwa da halin da zata shiga bayan wanda ta tashi a ciki. Sa'a kuwa kuka taci na tashin hankali ita da Yaya Gajeje, har takai Sa'ar da kwanciya zazzaɓi mai zafi. Duk da Atine ba damuwa tai da Zinneerah ba ita kanta saita wuni sukuku da ita, dan jini ya wuce wasa

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182