Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

Mama dake cigaba da kallonta ta riƙo hannunta cikin nata tana gyara zama da fuskantarta sosai. Hakanne ya saka Zinneerah maida kanta ƙasa idanunta na cika da ƙwalla. Itama Mama idanun nata cike suke da ƙwallan, cikin rawar murya tace, “Kiyi haƙuri Zinneerah, kiyi haƙuri kiyi haƙuri. Na fara da baki haƙuri ne saboda dalilai masu yawa. Nasan har ranki kina kallona ne matsayin uwa gareki mara adalci. wadda ta wofantar da ke ta manta da rayuwarki. Wlhy Zinneerah ba hakan baneba. Ni mahaifiyarki ban taɓa mantawa dakeba koda na daƙiƙa guda. A kowane sakanni kina maƙale a raina da zuciyata. Hawayena basu taɓa jinkirin fitowa ba a duk sanda na tunaki. Duk wanda ke tare dani yasan hakan Zinneerah. Nisantarki da nai itace babbar jarawar da har yanzu na kasa cimmawa wajen cinyeta, sai dai Alhmdllh, tunda yau gani gaki a yanda ban taɓa tsammataba ko tunani. Inason ki daure ki cire komai a ranki ki saki jiki dani ko hakan zai ragemin raɗaɗin ciwon gyanbon dake maƙale a zuciyata kinji”. Hannu Zinneerah tasa ta share hawayen dake sakko mata daga idanu zuwa kumatu, cikin rawar harshe tace, “Amma miyasa baki taɓa zuwa gareniba mama”. Murmushi Mama tayi itama tana sharar nata hawayen. “Zinneerah bana cikin hayyacinane, koda na baro ƙauyen Danya a yanayin ciwon hauka na barosa, sai dai Alhmdllh ALLAH ya taƙaitamin wahala maimakon na nufi wani waje saina nufi gida. Bayan isowata gida ƴan uwana sunje har Danya danjin miya faru dani amma mahaifinki yaƙi saurarensu, yama nuna bai sansuba baisan daga ina suka fitoba. Asabe kuma taci musu zarafi da musu korar kare. Duk da sunji zafin abinda akai musu sun buƙaci tahowa dake dan a gida na barki ni. amma mahaifinki ya hanasu, yama ɗora musu da cin zarafin dayafi na farko. Wannan shine dalilin yin fishinsu, amma basu haƙura akan wataran zasu amsoki ba. Ansha fama wajen nemamin magani sosai, har takai mai gidannan dake a matsayin yayana yaje Ɗanmusa yaga halin da nake a ciki, shine ya fahimci sihiri ne tattare dani. Shine yasa aka kawoni nan kano wajen wani mutumi mai bada magungunan musulinci. Ya kashe kuɗi bana wasaba wajen ganin hankalina ya dawo tare dani, bayan wani tsahon lokaci aka dace na samu lafiya. Daga nanne ya nema aurena. Duk da banso hakanba aka tirsasani harna amince. Sosai kina maƙale a raina tunda na dawo hayyacina Zinneerah, sai dai bansan miyasaba ko sha'awar nufar hanyar Danya banayi, kai hasalima duk sanda nai yunƙurin son naje sai ciwona ya motsa min. Ƴan uwana kam bansan daliliba kowa ya bar zancen amsoki ko zuwama inda kike. Hakan na damuna a cikin rai, amma inajin kunyar yima wani magana ace na zaƙe da yawa, amma kiyi haƙuri Zinneerah ki yahe mani kinji”. Kuka sosai Zinneerah keyi fiye da farko. tausayi da ƙaunar mahaifiyarta na sake shigarta cikin jiki da ɓargo. sun daɗe a haka kafin Mama ta koma lallashinta da tambayarta abubuwa game da rayuwarta da Inna Asabe. Wani takan bata amsa, wani kuma takanyi murmushi ne kawai, hakan yasa Mama sake fahimtar ɗiyar tata tasha wahalar rayuwa kamar yanda tasani Asabe zama tayi fiye da haka. Dan ko ita ba daɗin zama taji da itaba a tsahon shekarun da sukayi tare na zaman kishi. Yanda Mama bataima Zinneerah zancen ciki ba itama Zinneerah batace komai game da cikinba. Ganin dare yayi Maman tace ta taso taje ta kwanta haka nan. Yau kam Mama da Zinneerah sunyi barci ne a gado ɗaya, hakan ba ƙaramin farin ciki da jin daɗi ya saka Zinneerah ba, har takaita da shagala dogon tunani akan abinda ke a cikinta itama. Mace ne ko namiji bata saniba. Wanene mahaifinsa yaya aka samar dashi bata saniba, wace amsa zata bashi taba mutane da mahaifiyarta game dashi bata saniba. Ta shafa cikin tana sakin wani murmushi mai ciwo da saka ƙunar zuciya, daga haka barci yay awon gaba da ita mai cike da mafarkin Khalipha. *WASHE GARI* A yau kam Zinneerah ta sake tabbatarwa ashe itama mutum ce mai daraja kamar kowa, dan yanda ƴan uwanta da Mamanta suka kasance da ita ya jefa zuciyarta cikin matsanancin farin ciki. Kowa burinsa yaga dariyarta a gidan, ko yaya tai ɗan shiru sai ance mata mike damunta?. Abinci kam saita zaɓa wanda ranta keso ake bata taci. Dawowar maigidan kuma aka sake ninka tattalin da ake mata, dan shima da aka kaita ta gaidashi bayan yaci abinci ya huta janta yay tayi da hira cikin kulawa, tun tana ɗan noƙewa bata iya amsawa harta saki jiki dashi ta fara amsa masa. Ta jima a wajensa tare da sauran ƙannenta kafin ta dawo sashen Maman Sadiq suka cigaba da shirmensu ita da ƙanen nata. Haka rayuwa ta cigaba da yima Zinneerah daɗi a gidan mijin mamanta kuma kawunta, a hankali tana sakin jiki da kowa da komai nagidan. Har zuwa yau kuma da zata cika kwanaki uku babu wanda yay mata tambaya akan cikin jikinta balle jin ba'asin sanin inda ubansa yake. Itakuma bataima kowa maganaba dan addu'arta bai wucema ace kowa yaƙi tambayar tataba tunda batasan wace amsa zata basunba. Yau ma duk suna zaune tsakar gida gab da magriba, tunda yaran suka dawo daga islamiyya anan suka yada zango inda suka sameta tana gurzama Maman Halima kuɓewa da zatai miyar tuwon dare. Anan suka shiririce bata labari tana musu dariya da biye musu kamar yanda ta saba. Ƴammata ne biyu suka shigo gidan da sallama a bakinsu ciki-ciki. Sai ƙananu biyu dake biye dasu da ledoji a hannu. Idanu Zinneerah ta zuba musu kawai dan bata sansuba, hakama sauran yaran kallonsu kawai suke babu wanda yay magana. Sai Aliyu ne cikin tsalle yake faɗin, “Gasu Zainab gasu Luba”. Ko kallon inda Aliyun yake basuyiba suka nufi ƙofar ɗakin uwarsu, dai-dai Maman Sadiq na fitowa ne uwar tasu ta shigo itama da ɗayar yarinyar da zasuyi sa'anni da Zinneerah. Cike da fara'a a fuskar Maman Sadiq ta shiga faɗin, “A'a ƴan bikine tafe. Sannunku da zuwa”. A ɗan yatsine Saude da suke kira Maman Sakina ta amsa idanunta akan Zinneerah ko ƙyaftawa batayi. Ganin kallon ƙurillar da take matane ya saka Zinneerah faɗin, “Sannu da zuwa ina yini”. “Lafiya” tace kawai tana nufar ƙofar ɗakin nata itama. (Ashe tsugunne bata ƙareba kenan) Zinneerah ta ayyana a ranta zuciyarta fal tunanin waɗannan kuma daga ina?. Bata da mai bata amsa, dan haka ta miƙe dan ganin lokacin sallama yayi gashi wasu masallatan har an fara kira. Alwala tace su Sadiq suje suyi su tafi massallaci, ita kuma suka shige sashen Maman Halima ita dasu ƴan biyu domin gabatar da tasu sallar. Daga haka bata sake jin ɗuriyar Saude da ƴaƴanta ba a gidan, bakuma ta tambayaba har suka gama hira ta miƙe ita dasu Abdul suka nufi sashen mahaifiarsu dansu kwanta. Washe gari da safe bayan sallar asuba gari yay ɗan sha suka tafi gaida mutanen gidan kamar yanda Maman ta horesu. Sashen Alhaji suka fara zuwa wanda yaran gidan ke kira da Abba. Yana zaune a falonsa madaidaici da redio a hannunsa da alama kunnawa zaiyi, shigowar tasu ya sakashi ajewa yana dubansu da kulawa. Aliyu yaje jikinsa ya zauna, suko duk suka durƙusa a ƙasa suna gaidashi. Da fara'a yake amsa

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182