Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 70

Chapter 70

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

ta sauke da saurin yin gaba har ƙafafunta na neman harɗewa. Ya ɗan bita da kallo ƙasa-ƙasa harta shige bedroom ɗin hajiya iya. Janye idanunsa yay da zummar nufar nasa ɗakin shima yaci karo da gimbiya Farah mai zamani hakimce cikin kujera tacika tayi fam. yanda tai mugun tsatstsaresa da idanu ya bashi tabbacin tunda suka shigo tana a falon kenan.. Sanin halinta yasa bai tanka mataba ya ɗauke kansa yay gaba. Sai da yay kusan mintuna biyar da shigowa sannan ta biyosa. Tana shigowa yana shiga bayi. Duk da tsahon lokacin daya ɗauka bai fitoba a tsaye ya sake isketa ta kuma cika fam fiye da farko. Hidimar shiryawarsa ya shigayi yanzunma bai kulataba. Sai da ya gama tsaf cikin kayan barci ruwan sararin samaniya sannan. Kamar zai shareta dan takaici sai kuma ya ɗan dubeta ya ɗauke idanunsa. Inda take ya matsa sosai tare da dafe bangon da hannayensa biyu ya sakata a tsakkiya yana zuba mata fararen idanunsa da alamun barci ya bayyana a cikinsu. A take dukkan fushinta ya fara rauni dan waɗanan idanun nasa suna ladabtar da ita idan tai laifi. Suna kuma tabbatar mata da ɗunbin soyayyarta a cikinsu idan yaso lallashi. Suna kuma mata kwarjini da girmama kimarsa a gareta a duk sanda shi ɗin yazam mai laifi a gareta. A karan farko ya saki murmushi ganin yanda ta lumshe nata hawaye na silalowa. Fuskarsa yakai gab da tata suna musayar shaƙa da zuƙar ƙamshin juna. Kafin ya cire hannunsa guda dake dafe da bango ya saƙalo ƙugunta ya sake mannata da jikinsa sosai yana wani sakar mata numfashinsa da ƙarfi akan fuskarta. A take ta saki nannauyar ajiyar zuya da saka duka hannayenta ta zagayoshi ta ƙanƙame itama. Murmushin ya sake saki, batare daya ce komaiba ya ɗauketa cak ya nufi gadon da ita. Yana sauketa bargo yaja ya lulluɓa musu, zatai magana ya rufe mata bakin da nashi. Daga haka ɗakin yay tsit kamar ba ita ta gama cin alwashin karta masa shika shikan rashin mutunci cassa'in da tara ba. ______________________________★ *_DANYA_* Duk yanda Inna tasoji daga Karima hakan ya gagara. Dan ciwo ta kwanta kashirɓan tun randa ta dawo. Abin kamar wasa sai ga ƙaramar magana na neman zama babba. Tuni Inna ta manta da wani zancen kiranyen dataima Baba saboda ruɗanin halin da Karima ke ciki. A rana ta uku duk yanda taso ɓoyewa hakan ya gagara. Dan dole ta nufi gidansu Babawo ta sanarma innarsa. Sunyi mamaki matuƙa. Dan shi dai baice dasu Karima tana Danya ba, kuma koda safe sai da sukai waya da shi. Dole Innar Babawo ta ɗakko gyale ta biyo Inna gidanta. Itama hankalinta ya tashi ganin yanda jikin Karimar yay kaca-kaca da sayin duka ga ciki tsoho haihuwa ko yau ko gobe. A ruɗe tace ma Inna ta shirya karimar suje asibitin kusada. Bara taje ta nemo ƙanin Babawo ɗin tunda yanada mashin. Daga haka ta fice ita kuma Inna daketa tsinar Babawo ɗin ta shiga kimtsa Karima......... _____________________★ Hajiya iya batasan su Zinneerah sun dawo gidanba sai da asuba ta ganta kwance a bayanta. Hannu tasa ta shafa mata fuska tare da gyara mata bargo. Itama cike da ƙarfin hali ta nufi bayi yin alwala dan ƙafarta ciwo take mata tun da daddare dama. Da ƙyarma ta iya kai kanta bayin. hakama da tayo alwalar da gyar ta fito. Duk yanda taso gabatar da salla a tsaye hakan ya gagara sai a zaune tayita. Bayan ta idar kuwa ko azkar yau batayiba ta zame ta kwanta a wajan. Itama Zinneerah farkawa tai, sai dai koda taga Hajiya Iya kwance a ƙasa bata kawo komai a rantaba ta shige bayi kimtsa jikinta. Ganin harta fito Hajiya Iya na kwance a wajen sai abin ya ɗan bata mamaki amma batai magana ba ta hau shiryawa dan wanka tayo. Batajin ciwon komai yau sai rashin ƙwarin jiki. Ta shirya cikin siket da riga na baƙin Material mai adon firanni golden. Ganin Hajiya Iya taɗan motsa ya sata zuwa gabanta ta tsugunna tana gaisheta. Hajiya Iya ta buɗe idanu da ƙyar tana duban Zinneerah ɗin. Murmushin ƙarfin hali tayi da miƙa mata hannu ta kamo nata. “Inno na yaya jikin?”. Kasa amsawa Zinneerah tayi saboda jin zafi jikin na Hajiya Iya. aɗan rikice ta sake damƙe hannun cikin nata tana faɗin, “Granny baki da lafiya ne?”. Kamshinsa ne ya katse Hajiya iya dake ƙoƙarin bama Zinneerah amsa. Zinneerah ma sai ta ɗan dubi ƙofar dai-dai ya shigo idanunsa suka shige cikin nata. Saurin janye natan tayi tana maida kai ƙasa dan wani irin matsananciyar kunyarsa taji saboda tunowa da faɗa masa a jiki datai jiya da dare. Ga sirrinta daya gamaji a bakin hajiya iya kafin su wuce da kuma tabbacin ya sakejin wani wajen Dr Mahmud. Shima nasa idanun ya janye yana duban Hajiya iya dake kallonsa a kwance. A take ya gano babu lafiya dan yasan hajiya iya sosai a rayuwarsa. Duk da kuwa zaman da yay a wajenta na shekaru tara ne kacal, sai hutun da yake zuwa mata kuma bayan ya koma London karatunsa. Ta inda Zinneerah ke tsugunne ya ƙaraso ya ɗan ranƙwafo kansu yana kai hannu goshin Hajiya Iyan. “Granny lafiya kuwa?”. “Wlhy ƙafafun nan ne ke neman takuramin kwana biyun nan Moddibo ”. Idon Zinneerah na cikowa da ƙwalla tace, “Amma Granny shine baki faɗaba? Wlhy jikinki zafi dan ALLAH ki tashi muje asibiti”. Yanda ta ƙare maganar hawaye na silalowa ga rawar murya ya sakashi ɗan dubanta, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ɗayan hannun Hajiya iya ya kama shima ya tadata zaune sosai dan tanada jiki itama masha ALLAH. Gaban Hajiya Iyan yay wani ɗan tsuggunne idanunsa na sauya launi zuwa damuwa. Dole Zinneerah ta miƙe saboda kusancin da suka samu yayi yawa. Cikin wayancewa tace, “Bara na haɗo miki kunu kiɗansha sai kisha maganinki”. Murmushi Hajiya Iya tai tana binta da kallo harta fice, kafin kuma ta sake maido idonta kan Yah Adnan dake mata tambaya muryarsa a ƙasa. Al'amarin kamar almara sai ga jikin hajiya iya na neman rikicewa a wannan yini, dole Dr Mahmud da Khalipha suka rufu a kanta duk da shi bai kammala nasa karatunba ma. Amma kwazon da yake nunawa yasa ko ƙasar yazo yakanje Shira hospital yay wasu ƴan ayyuka dai-dai saninsa. Tashin hankalin ruɗewar jikin ya saka Yah Adnan cewa zai wuce da Hajiya Iyan london a yau. Amma sai Baffah da ake saran zai dawo ƙasar yau ya taushesa akan yay haƙuri yana zuwa shima. Badan yasoba dole yabi umarnin mahaifinsa da yake zuwa yamma jikin Alhmdllh ya ɗan ɗaga mata. Duk wanda ya kalli Zinneerah yau yasan tasha kuka. tayi wuni firgai-firgai da ita na damuwa. tabi ta nane a ɗakin wajen Hajiya iya ita dasu Jamal. Ko yayansu ya shigo su su Jamal tsoro na sakasu fita da shakkarsa. Itako duk da tanajin shakkar tasa da kwarjin da yake mata saita fiske abinta taƙi fita. Dama tun lokacin da jikin ya rikice tai kiran Maman Sadiq ta sanar mata. Itama hankalinta ya tashi matuƙa dan haka tace zuwa yamma zata shigo tare da yara su dubata dan yanzu duk sun wuce makaranta Little ne kawai a gidan. Aiko kamar yanda Mman Sadiq tai alƙawari bayan

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182