Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 139

Chapter 139

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

akan kishinsa har zargi na zuwa miki a harshe da tunani to lallai ki tabbata zaki koma 0 a ziciyarsa. Matan yanzu da yawa ba kishin mazansune kaɗai matsalarsu ba, harda zargi. Idan miji ya fita zuciyarki na miki kaikawo yanacan tare da wasu matan, idan ya shigo gida ya ɗauki waya bazakiyi masa zaton alkairi ba sai kice yana cheating da wasu matan. Idan yana huɗɗa da mata a ikinsa ko kasuwanci zuciyarki taita kitsa miki karuwansa ne, idan mai yawan sakewa ne da mutane ki zargesa da yawan son mata. To dama kin taɓa ganin namijin daya rayu babu mace a ransa? Komin tsanani da tsantsenin ki baki isa hana namiji ɗabi'ar son mata ba dan haka ALLAH ya haliccesu, ba kamar ke bace da akai miki iyaka dakinyi aure shikenan. Daga lokacin da kishi ya sakaki yawan zargin miji koda hankalinsa baya kan matan ma to zai fara nutsuwa wajen fuskantarsu, daga ƙarshe kodai ya ƙaro auren da kike tsoro, ko ya fara bin matan a waje su halakashi kema ya halakaki, waya janyo?. Ki nutsu ki zama jaruma ta kowanne fanni, nasan yaƙine ba ƙaramiba amma inhar kinsa kanki zaki iya, koda kina kishin mijinki ki dinga dannewa kinayin mai aji wanda shi kansa zaisa yaji shakkarki akan wata macen, da kuma shiga damuwar anya ma kina sonsa? Ya dingaji ƙaimi wajen kafa soyayyarsa a gareki dan yaga wannan kishin naki amma hakan ya gagaresa, sai kiga yafi lalacewa a wajenki fiye da wadda yake hange a wajen. Duk da nasan maza kala-kala ne kuma kowanne da irin nashi salon, ki nutsu ki karanci nakin, ki daina kuma tilastama kanki sai kin samesa ɗari bisa ɗari yanda kike buƙata. wannan bamai yuwuwa bane a gareki, dan kema baki cika hundred percent ɗin ba a garesa. Mijinki na sonki Farah, yana kuma miki kawaici darajar mahaigiyarsa da na zuminci, amma kinata ƙara sakaci da damarki, wadda idan har kikai wasa anzo gaɓar da zaki iya rasashi ma baki ɗaya wlhy, dan Abdul-Mutallab yana tarakine kawai, ina jimiki tsoron randa zai kai ƙarshe a al'amuranki, duk yanda kike tunanin Hindatu na tsaya miki bazai sauraretaba itama, sai kuma kin fita kwana a ciki dan ita uwa ce babu yanda zai mata. Aurensa bashi ke nufin ƙarshen rayuwarki yazo ba, yanzune ma ya dace ki zage damtse wajen dawo da kimarki da martabarki a wajensa, inba hakaba kuka yanzu kika fara dan zaibi ta hanyar ƙara auren nasa ya rama dukkan ƙuntatawar da kike masa ke da Hindatu, hakama danginsa zasuyi amfani da ita wajen ganin sun rusaku ke da ita ɗin tunda kin shiga makarantarta babu gaira babu dalili, itama ɗin da take hura hanci sun mata laifi banga ta inda sukai matanba balle ke da kikai taka haye akan abinda bakisan yaya yake ba. Ƙiri-ƙiri tana amfani dake akan wani shashanci nata mara tushe balle makama. Sai ki shiga hankalinki idan zaki shiga, dan daga ita har Zakiyyar ba hanyar da zata ɓille dake suke ɗauraki ba”. Tana kaiwa nan ta miƙe ta barta da sharɓar kuka tana nazarin maganar Mahma ɗin dalla-dalla. Dan tabbas sanda bata zama haka ba dukkan kulawa da tattalin rayuwa Yah Abdul-Mutallab yana batasu, danshi mutum ne mai kawaici, idan kuma ya ɓalle bayajin bari. Yasha nusar da ita illar kai ƙararsa da takeyi ga Mammah da Aunty Zakiyya amma ta kasa fahimta, dan a ganinta Mammah da Aunty Zakiyyar ne kawai zasu iya saita mata bauɗaɗɗen halinsa na tsiya koda yanaso ko bayaso. Ashe ba haka bane, sake kangarar masa da zuciya kawai sukeyi da kusantashi da dangin nasa da suka tsana. Itakam ta shiga uku, wlhy bazata iya zama da wata ɗiya mace a matsayin kishiya ba koda kuwa ƴar waye. A lokacin da Mahma da Farah ke wannan maganar Zakiyya da Mammah nacan sun kulle kansu a garden suna maganar da suka gagara samun sararin yi tun ɗazun. “Mammah inajin tsoro wlhy, anya mutanen nan basu fahimci wani abu daga garemuba suketa ambaton zancen dashen ciki? Gashi munyi sakaci wannan harmutsin na neman kaimu ga tonon silili, lokaci yayi da Farah zata koma Morocco da zama harta haihu amma hakan ya gagara. Kigafa yanda abokinsa yayi jiya da akace tanada ciki”. “Hakane Zakiyya, nima kaina da abin nan na kwana a raina jiya, babban tashin hankalina kuma yaƙin da mukeyi ɗinma baiyi amfaniba, tunda gashi dai Kabeer na neman cin galaba a kaina tunda sun aura masa wadda suke so ɗin, amma na ɗau alwashin sai Abdul-Mutallab ya saketa wlhy. Babban tashin hankalina a yanzu zancen yaron nan da Abdul-Mutallab ya haifa da yarinyarnan. Nasanshi sarai akan faɗar gaskiya, da ace ya aikata wani abu a gareta har aka samu cikin ko zamu kashesa sai ya faɗi yanda akayi, amma ki dubafa yace shima baisan yarinyarba sai a gidansu, kuma ma idan mukai aiki da hankalinmu muma ta ina zai santa? ita da akace a wani ƙauyen ƙayau take da ko kwalta basu da. Wlhy na rasa ina tunanina zai shiga, yarinyar dai dana san anyima aikin farko a gabanmu tai ɓari balle muce ko ƙarya tai mana taje ta haihu a wani waje. Kuma bama ita bace wannan dan waccan babbace ma ai, wannan kuwa yarinyace ƙarama fa sweet 17”. Gumi aunty Zakiyya ta share wani bahagon tunani nason mata kutse a ƙwaƙwalwa, ta haɗiye yawu da ƙyar tana gyara tsaiwa, “Mammah inason ganin ita wannan yarinyar dan kinsan ni bamma santaba”. “To Zakiyya miye amfanin ganinta tunda tunda ba wani abu muka haɗa da itaba. Ko akwai wani abu da kike tunani wanda ni ban sanshiba?”. “A'a wlhy Mammah ”. Tai saurin faɗa tana girgiza kanta da ƙara share gumi. “To kin gani. ai ganin nata baida amfani dan jira nake yazo gidan ma yanzun nan ya rubuta mata takardar saki ta kama gabanta. A yau kuma nakeson mubar ƙasarnan da Farah kafin ita kanta Addah da farga da halin da muke ciki, dole kuma mu sake neman wanda zai mana bincike sosai akan yarinyarnan, dan na kula wancan da yay mana shirme kawai ya tafka yaci kuɗi shegen, dan binciken nasa akan auren Abdul-Mutallab da yarinyar kawai ya tsaya. Ni kuma ta inda yarinyarnan ta samu ciki nakeson sani, dan ta wannan hanyar ne kawai zamu fahimci inda matsalar ta faro mukumayi maganinta kafin su Kabeer su kaimi ƙasa. Duk da yaron na tsananin kama da Abdul-Mutallab ban yarda da gwajin da akace an musu ba, gani nake kawai haɗin bakine dasu Kabeer dan a tabbatar da ɗan nasane a kaini ƙasa wajen aura masa yarinyar da maidosa zama cikinsu”. Nanma kai kawai Zakiyya ta gyaɗama Mammah dan tunaninta ya fara ƙarfi akan abinda zuciyarta keta mata kai kawo.... AK dake tsaye a ƙofar garden ɗin tun fara maganarsu ya dinga jan ƙafafunsa da sukai masa nauyi da baya-baya zuciyarsa na wani irin harbawa, idan har lissafinsa da abinda yaji zasu iya zama a muhalli dai-dai kamar akwai lauje cikin naɗi a maganar Mammah da aunty Zakiyya. Dan tun fara maganarsu akan kunnuwansa suka shiga kaf. Kasancewar a can wajen gate ya ajiye motarsa ya shigo shi kaɗai. Hango a yanda su Mammah suka nufi garden ɗin lokacin da yake shigo gidan ya sashi tunanin ko

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182