Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 98

Chapter 98

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

Adnan akan kamanninsa da Little”. Murmushi Baffa yayi mai faɗi, ya gyara zamansa yana faɗin, “Nasani Hauwa'u, muma kuma ba hakan bane a ranmu wlhy, sai dai ki sani tun randa kukazo da yaron nan gidannan babu wanda zuciyarsa ta huta akan kamaninsa da Adnan a gidan nan. Jin gaskiyar samuwarsa tasa muke kwaɗayin yin gwajin ko hakan zai sama mana kwanciyar hankali, dan nayi alƙawarin saina ƙwatoma Zinneerah haƙƙinta awajen koma wanene. Yanzuma bayan anyi gwajin insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zamuje can asalin ƙauyen nasune. Dan haka banason zuciyarki ta ƙara miki wani hasashe daban bayan ƙyaƙyƙyawa”. Sosai raunin mmn sadiq ya bayyana, tace, “Shikenan yaya, ALLAH ya saka da alkairi yabar zuminci. Bara nama Yaya magana to dan yana gida sai mu kawosa kawai”. “Hakan shine dai-dai, mu haɗu a shira hospital daku”. Daga haka Baffah ya yanke wayar. Wanka kawai AK ya samu yayi bayan Safiyya sunje sun gyara masa ɗakinsa da falon ɓangaren hajiya iya, abincima bai iya ciba sai tea yasa Ni'ima ta haɗa masa. daga haka ya fito ya sami Baffah dake zaman jiransa yana waya rai ɓace. Shiru yay yana nazarin wayar ta Baffah, inda kai tsaye ya gane da Mammah suke waya, runtse idanunsa yayi da ƙarfi jin yanda Baffah ke dasama Mammah baƙaƙen maganganu, wanda ya tabbatar itace ta fara masa, shiko yake maida mata murtani. Juyawa yay a hankali zai fita ya jiyo kalaman Baffah da suka sakashi dakatawa a kausashe. “Komi zakice kice Hindatu, wlhy da banma kawo hakan a rainaba game da Adnan. Amma wlhy kinji na rantse a wannan gaɓar zan tabbatar miki da cewa ni Kabeer Abdul-Mutallab Shira nine mahaifin Adnan, ba kuma tsoronkine yasa na barmiki shiba daga shi har ƴar uwarsa. Dan haka muzuba mu gani ni dake ɗan hakal ka fasa”. Daga haka Baffah ya yanke wayar yama kasheta gaba ɗaya dan baya buƙatar ta sake kiransa..............✍ *_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 39* ..........Da sauri AK ya ƙarasa ficewa ransa na masa ƙuna da wannan halayya na Mammah, bashi da burin daya wuce ganin iyayensa sun sasanta kansu sun koma rayuwar aurensu, sai dai ya gwada ƙoƙarin yin haka yafi sau a ƙirga abin ya gagara. Kuma Mammah ce ke bada matsala a koda yaushe. Tunma Baffah na nuna masa zai amince shi, har takai yanzu idan yay masa maganar Mammah saiya ja masa warning. A mota ɗaya suka tafi ran kowa babu daɗi, dan haka motar ta ɗauki shiru sai driver daketa aikin tuƙi har suka isa Shira Hospital. Tuni AK ya tanadi likitocin da zasu aikin harsu uku domin samun gamsuwa akan abinda zai fito, dan haka suna isowa suma su Mmn Sadiq suka iso ɗauke da Little. Yanako ganin AK ya maƙale masa, duk da ɓacin ran da AK ke ciki sai da yay murmushi yana mai rungume little a jikinsa. Ganin yaronma da yayi sai yakeji a ransa ALLAH ma yasa ya kasance nashi ɗin, dan har cikin ransa wata irin ƙauna yake masa mai ƙarfi da saka zuciya nutsuwa. Cikin mutunta juna suka gaisa, inda mamaki ya cika Dr Mahmud saboda ganin Abba. Shima Abba daya ganesa sai wani tunani yazo masa. Cikin kasa jure abinda ke ransa yake tambayarsa ko ina bawan ALLAHn nan daya sakama little sunansa?. Kai tsaye Dr Mahmud dake dariya ya nuna AK, “Baba ai gashima zaune, ina takwaran nasa kuwa? Nasan ya girma yanzun ko?”. Da sauri Abba ya kalli AK da Little ke a jikinsa zuciyarsa na bugawa. Cikin ɗan rawar murya yace ai ga yaron nan a hannunsa”. Ba Dr Mahmud ba, hatta AK sai da zuciyarsa ta harba. Yay saurin duban Abba da faɗin, “Uncle kana nufin kaine wanda ya bani damar zaɓama yaro suna shekara uku data shuɗe?”. “Tabbas nine kuwa. Kuma wannan shine yaron”. Sosai maganar Abba ta sakasu jin shock su duka. Baffah dake saurarensu ya nemi jin ƙarin bayani. Dr Mahmud ne yay masa bayanin komai har yanzu firgici da al'ajabin kamannin little da AK na bayyane a fuskarsa. Murmushi baffa yayi yana jinjina kansa. Sai dai komai baiceba yabarma zuciyarsa. Dan yama gama yarda AK na ɓoye masa wani abune game da yaron kenan, inba hakaba yaya akai hakan ta faru? Tunda a wannan zuwan basusan yazoba sai a shanun ƴan talla yaji. To lallai kam zaiyima tufƙar hanci, dan yama gama yanke hukunci saura zartarwa. Baffah ne ya dakatar da wannan hasashen su Dr Mahmud suka shiga aikinsu. Duk wani gwaje-gwajen daya dace akan ƙwayoyin haluttar little da AK akai musu. Abinka da masu abu, ba'a wani zauna wasaba suka shiga ganin sun tantance komai dan Baffah yace bazasubar asibitinba sai da result....... _________________________★ *DANYA* A lokacin da gwajin ƙwayoyin halitta ke gudana acan Shira Hospital tsakanin AK da Little anan danya kuma baƙuncin Baba su Inna suka samu da farar safiya babu zato babu tsammani. Duk suna zaune a tsakar gida ƴan barka na shigowa jefi-jefi da ƴan gulma. Karima na ɗaki kwance ita da ƴar jinjirarta tana kwasar kuka akan abinda ya barota da Kaduna, dan wahalar ciki tasa bata samu damar nazari akan komaiba sai yau da take jinta sakayau. Tinene na kwance a ƙofar ɗakinsu wai ƙirjinta da kanta na ciwo, tun safe data tashi da abinda ta wayi gari kenan. Sai Sa'a daketa kaikawon yin aiki ita da Yaya Gajeje. Inna kuma na zaune kusa da Tinene tana gyaran gyaɗa da Yaya Gajeje tazo da ita gidan domin yin miya. Sallamar mace da sukaji ya sakasu ɗan juyowa kusan su dukansu dan duk zatonsu ƴan barka ne ko cikin dangin Babawo dakan zo jefi-jefi, dan innarsa ma da tace zata dawo tun jiya har yau basuga ƙeyartaba. Sai dai ta aiko musu da kayan kunun da tace dana barka kuma kamar yanda uwar miji keyi a al'adar ƙauyen. Ƙyaƙyƙyawar mace mai tarin kamala da ƙwarjini ta sake maimaita sallamar datai musu ganin duk sun zubo mata idanu basu amsaba. Yaya Gajeje ce tai ƙarfin halin amsawa da cewa, “Maraba, bismillah shigo baiwar ALLAH duk da dai bamu wayekiba”. Murmushi matar tayi tana ɗan juyawa bayanta jin motsin takowar abokin tafiyar tata. Kafin ta samu damar bama Yaya Gajeje amsa Baba ya shigo shima da sallama a

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182