Chapter 15
Chapter 15
barki bane, sannan tana aikoma yarinyar da wasu ayyuka, shiyyasa da munyi aiki akan yarinyar baya wani nisa yake warwarewa. To amma ke kin tabbatar akwai cikin kuma?”. Cikin wata lalatacciyar dariya Inna tace, “Ciki kau akwaishi malam kallamu, dan ƙuru-ƙuru ya bayyana kansa ga mutane”. “Tohwa babbar magana. Amma yanzu kunsan wanene yay cikin?”. “Inaaaa! Babu wanda ya sani, inada tabbacin acan inda nasa ƙawata ta kaita aikataune wani ya ɗura mata shi. Kasan yaran birnin nan akwai basira. Balle ƴar banzar yarinyar tanada ƙyau irin na uwarta. Yanzu haka jiran Hajji Lanti nake tazo naji miya hwaru. Amma itama bullum kakeji kamar an aiki bawa garinsu”. “Shikenan, yanzu dai ayau ɗinnan zanyi wani aiki. Kamar dai yanda na hwahinta ke dai bakiso yarinyar ta hiɗi ta sanadinki tabar gari ko?”. “Kwarai ko Malam Kallamu wannan shine hwatana. Dan nahi son kowa ya dinga kallonta da hita tai yawon tazubar ɗinta harta samo wannan cikin. Nihwa idan san samunane tabarma garin baki ɗaya yanda mutane zasu sake yarda komawa tai wajen farkan nata. Bazan ɓoye makaba zaman yarinyarnan a gidan na baƙantan rai, dan ji nake kamar har yanzu uwarta na tare damu, duk da na nisantata da garin tuni, to itama ɗiyar sonake na nisantata da Danya har abada, nahison na rayu gidan mijina dagani sai ɗiyana aradu”. Kai Malam Kallamu ya jin jina yana murmushi saboda shima mugunne na haƙiƙa, shiyyasa tasu tazo ɗaya da Inna. Kuma wai a haka shiɗin malamine, harda almajirai a ƙarƙashinsa yana basu ilimi🤦🏻. Ya sake haɗa mata abubuwa da yawa. Tare da tabbatar mata a daren yau zaiyi wani aiki akan Zinneerah. Ta ajiye masa kuɗi tana masa godiya ta taho akan sai gobe yazo ɗaurin aure zai tahoma da Karima wani haɗin neman sa'a a gidan Babawo. (Humm ALLAH ya shirya mana zukatanmu. Babu wani banza daya isa baki ƙyaƙyƙyawar rayuwa a duniya sai UBANGIJI. Domin shima idan kura na maganin zawo yayma kansa mana. Idanma asirin kikayi akan wani kikaga yacisa dama can ƙaddararsa kenan koda bakiyi komaiba tunda ALLAH yay alƙawarin shigarsa wannan halin saiya shiga ɗin. Abindama jahilai suka gaza ganewa shine. Da yawan jarabawa tsanice na kaiwa ga nasarorin rayuwa ga bawa. Dan da wahala kaga mutum yaci wahala a rayuwarsa daɗi da farin ciki basu biyo bayansaba. Bawai dole sai a duniyaba. dan UBANGIJI yay mana alƙawarin samun babban tagomashi a lahira da yafi na duniyar komai. Dan kaci wahala a rayuwarka ba dolene sai kayi arziƙiba a ƙarshe. Ba dolene saika zama mai ɗaukakaba a ƙarshe. ba dolene saika zama tauraron al'umma ba a ƙarshe. UBANGIJI zai iya sakanka makane ta hanyar da kaima bakai zatoba. Amma fa saika zama mai juriya da haƙuri wajen karɓar jarabawarka da ƙaddararka. ALLAH kai riƙo da hannayenmu a komanmu😭🙏🏻). ★★★★ Bayan farkawar Zinneerah a barci kusan ƙarfe huɗu suka baro Kusada zuwa danya. Kallo ɗaya zaka fahimci ransu a dagule yake su duka. Zinneerah kam bama a iya tantance halin tashin hankali da ruɗanin da take a ciki. Sam zuciyarta da ƙwaƙwalwar kanta basa aiki irin na kowanne mutum. Abubuwa da yawa ke zuwa mata a rai game da wannan ciki, har kashe kanta ta ayyana yi amma wani ɓangare na zuciyarta ya ƙwaɓe akan wannan ba mafita bace. Tunda mashinansu suka shigo garin idanu caa a kansu. A take ƙananun magana suka fara tashi akan wai ankai Zinneerah kusada ne an zubar da ciki. Su dai basu san sunayi bama. Wani matsanancin tsoro ne ya shiga zuciyar Zinneerah ganin sun iso gida. da ga ita sai Gwaggo Laritu suka iya shiga gidan. Su kawu juyawa nasu gidajen sukai abinsu dan basusan yanda zasu tunkari yayansu da wannan magana ba. Gashi likita yace abar Zinneerah ta huta na kwana biyu kamar yanda jikinta ke buƙata. Mata ne cike da gidan danƙam anata arerewa da guɗa. Dan masu kiɗan ƙwarya Inna ta kira suke wasa a gidan wai yau take nata yinin bikin. Da farko har suka shigo gidan sukama kusa kaiwa ɗakin kwanan su Zinneerah babu wanda ya kula da su. Suna gab da shigewarne Inna ta hango Zinneerah. A tsawace tace, “K! K! K! Dakata mani. Masu kiɗa ku saurara kaɗan ina zuwa”. Kamar wadda tai busa da sarewa a kunnuwan jama'a a take gidan yay tsit, hankalin kowa ya dawo kan Zinneerah da Yaya Gajeje yasata saurin nufosu itama. Kusan a tare suka iso gaban Zinneerah ɗin, inna ta kalla Gwaggo Laritu datai kamar batajiba tana neman shigewa ɗakin su Zinneerah ɗin. “Lallai ko ba'a faɗaba yanayin da kuka shigo mani gida kawai ya tabbatar da zancen ciki......” Da sauri Gajeje ta katseta da faɗin, “Haba Inna wacce irin maganace haka? Wannan ai zancene na cikin gida ko”. Harara Inna ta watsama Gajeje, ta kai hannu ta finciko hannun Zinneerah da kanta ke a ƙasa hawaye masu zafi na ziraro mata a saman kumatu. Hannu tasa ta yaye hijjab ɗin jikinta ta jefar. Ta kama rigarta zata cire Gwaggo Laritu ta riƙeta a fusace. “Wlhy! Wlhy wlhy kinji na rantse sau uku, inhar kika hiddama yarinyar nan riga yau saina nuna miki ni jinin gidan baduku ce Asabe. Wai kina tunanin ana tsoronkine ko me? Mi yarinyarnan ta tsare maki a gidan nan ne wai shin? Idan ma cikkinne da gaske a jikinta ai kece silarsa. Dan kece kika hana mata rayuwa zaman lahiya kamar yanda kika hana ubanta. Ya auro mahaifiyarta dan yaji sauƙi kika shiga kika hita sai da kikaga tabar gidan saboda son zuciyarki. Wama yasani yanzunma ko kece kika biya aka lalatama yarinya rayuwa, dan wlhy duk abinda akace kinyi Asabe nasan zaki iya mahiyinsa saboda son duniyarki”. Tofa babbar magana. Waɗan nan zantuka na Gwaggo Laritu a take ya hargitse gidan, kafin kace mi taron biki ya zama taron faɗa da bala'i. Tun anayi a cikin gida har aka koma ƙofar gida, abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai faɗa ya juye tsakanin dangin Baba dana Inna. Yayinda jama'ar gari suka rabu gida biyu, wasu na goyon bayan Inna wasu na goyen bayan dangin Baba da Zinneerah. Abu yay tsamari har magriba babu alamar zasu sarara, daga ƙarshe dai sai da zance ya kaisu ga gidan mai-gari daya aiko aka tattaresu zuwa can. Sosai zancen ciki a jikin Zinneerah ya tayarma mai-gari hankali. dan har ransa yakejin ƙaunar yarinyar da tausayinta. Tun a randa sukazo shari'arnan shi kaɗai yasan abinda ke ransa game da Zinneerah. Dan ya ɗaukama kansa alƙawarin zai tsaya mata tai karatu, kuma ɗansa dake karatu yanzu haka a Katsina shi yake burin zama mijinta. Sai kuma gashi yau wannan magana maiban tashin hankali ta ɓullo rana tsaka. A yau ma tambayar duniya anma Zinneerah akan wanene mai ciki tace ita bata taɓa aikata iskanciba, dan haka batasan ina ta samo ciki ba. Lallai wannan al'amari ya kai a kirasa MAKAUNIYAR ƘADDARA, ita da ciki ke jikinta batasan yanda samuwarsa ta wanzuba, su kuma dake tuhumarta ina zasu kama?. Ganin dare yana neman rufawa mai-gari yace suje gida gobe idan ALLAH ya kaimu zai nemesu, dan wannan magana babbar maganace dolene sai sunje ga hakimin kusada ko a samo bakin zaren a can. Wannan magana ta tadama Inna da Zinneerah hankali
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182