Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 174

Chapter 174

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

“Daddyna yace nakiraki zaije anguwa”. “Naji to, kace ina zuwa”. Sai da little ɗin ya fita ta duba Mama A'i. “Mama an gama haɗa abinda ya rage ɗinne?”. “Eh an gama maman Abdul, harma na miki karanbani na shirya a tray ”. “Kai aiko ngd aiba karanbani bane”. Zinneerah ta faɗa tana mikewa. Fita tayi domin kai masa kayan breakfast ɗinsa. A falo ta samesa zaune yaci gayu cikin ɗanyar shadda ash, yana zaune a dogon kujera little a kusa dashi yana duba masa ƙafarsa da yaji ciwo. Koda tai sallama bai ɗagoba har ta karaso inda suke ɗauke da tray ɗin. “Barka da hutawa”. “Barka” ya amsa mata yana ɗan dagowa ya dubeta. Duk yanda yaso maida idonsa ga ƙafar little ɗin kuma sai ya kasa. tai ɗan murmushi da ɗauke kanta ganin kallon da yake mata. “A ajiye nan ko dining?”. Lumshe idanun yayi ya ɗan buɗe a kanta, cikin kasalar data samesa yanzu yace, “Ajiye anan kawai”. Saman centre table ta ɗaura tray ɗin da duban ƙafar little dake cikin hannunsa. “Shi kuma wannan miya samu ƙafar tasa?”. Iska AK ya ɗan furzar. “Yace faɗuwa yayi ga waje harya fashe, taimakemu da man zafi ma a ɗaki”. Bedroom ɗin nasa ta nufa tana faɗin, “Maganin mai gudu kenan idan yana tafiya”. Murmushi kawai AK dake binta da kallo yayi, dan a kwankin nan data haihu duk ramar nan ta ciki da tayi nan ɓacewa take, sai wani irin buɗewama takeyi alamar lafiya ta samu. Miƙewa yay yabi bayanta yanama Little gargaɗin ya jirasa ya dawo. Zinneerah na ƙoƙarin fitowa sukaci karo, baya ta koma tana faɗin, “Ouch Yayanmu zaka fasamin kai”. “Kokuma ni zaki fasamin ba”. Ya faɗa yana matsota. Kallonsa take da mamaki, ganin dai da gaske kanta yayo tai saurin faɗin, “Yayanmu wani abu ya farune?”. “Faffaruwa ma madam” Yay maganar yana kamo hannunta da jawota jikinsa. Hancinsa ya cusa cikin wuyanta yana magana raɗa-raɗa. “Ko tausayinama baƙyaji kin barni da kwana da little ke kinacan kina morewarki ko?”. Dariya zancen nasa ya bata, amma sai batayiba tai murmushi da ƙoƙarin ƙwace kanta. “Yayanmu ai amfanin mata biyu kenan, ni ina fama da wannan fiɗan inani ina ɗaukarka. Kawai aunty Farah ta dawo kaga ni sai nayi arba'in”. Gani tai ya saketa baki ɗaya yana tsuke fusaka. Ya watsa mata harara yana jan guntun tsaki, batare da ƙara cewa komaiba ya juya ya fita a ɗakin. Bayansa tabi da kallo tana murmushi, a fili tace, ‘Uhm ka gama mazuranka ne dan nasan kana son kayarka’. Iskeshi tai yana zuba abincin da kansa. Batai maganaba ta matsar da little kusa da shi ta zauna, “Ina waje. ciwon Alhaji?”. Ta faɗa tana kamo ƙafar little. Nuna mata yayi, ta buɗe man zafin ta shafa masa yana wani shii da baki da yarfar da hannu. “Daddy kace tayi a hankali zafi”. “Oh ALLAH, ALLAH yaron nan saika kashe auren da babu soyayya, yanzu shafa maganinne da zafi?”. Zancen nata ya bama AK dariya amma sai ya gimtse bai yiba. Yadai kamo hannun little ɗin yana bata amsa a daƙile. “Dama can babu soyayyar ne ai”. Tasan da biyu ya faɗa, dan haka taja bakinta tai shiru. Sai dai ta cigaba da kallonsu yanacin abincin yana bama yaronsa har suka kammala. Bai wani jima da gamawarba ya mike yana kallon agogo. “Saifudden zai kawo muku cefane. Dan bazan dawo ba sai dare”. Mikewa itama Zinneerah tayi da faɗin, “ALLAH ya saka da alkairi ya kara buɗi, miza'a dafa maka da daren”. Kallonta yay cikin ido sonta da buƙatarta na ɗawainiya da shi, yaja numfashi da duban inda little yake. Ganin hankalinsama ba'a kansu yakeba sai ya sake kallonta. “Abinda nakeso a dafamin kam ai ba bani za'aiba. Sai dai nayi manage da tuwo”. Murmushi tayi tana maida kanta gefe dan tasan ina ya dosa, ta hau tattara kwanikan, “Uhm ni Yayanmu ALLAH fitina kake ƙarowa kullum, na kawo mafita kuma kaji haushina”. “Ke dai kika sani” ya faɗa yana nufar ƙofa. Murmushi kawai tayi ta cigaba da abinda take. Sai da ta kammala ta tisa ƙeyar little da baima lura da fitar Daddyn nasaba ta rufo sashen. A sashenta ta samesa zaune suna gaisawa dasu Yaya Gajeje ƴan biyu duka na'a jikinsa yana kallonsu zuciyarsa fes da farin ciki. Inda yake little ya nufa ita kuma ta nema waje ta zauna. Ya ɗan jima a falon suna maganar jikin Inna daya fara lekawa tana barci dasu Yaya Gajeje kafin ya basu yaran da musu sallama ya fice, bayan ya jefeta da wani kallon duk randa na kamaki. Murmushi mai sanyi kawai tai masa da rakashi da addu'a. Shima daga nan sashen Farah ya shiga inda ya samu su Mammah na karyawa. Sun gaisa nanma yaɗan zauna suka taɓa hira sannan yay musu sallama yabar little anan ya fice. ★★★ Daga ranar Zinneerah bata sake masa zancen Farah ba har ALLAH yasa sukai arba'in. A randa tai arba'in ɗin kuma su Mammah ke shirin tafiya katsina duba su Farah daga can su wuce london. Gaba ɗaya Zinneerah sai ta shiga damuwa. Dan zamansu a gidan ba ƙaramar shaƙuwace ta shiga tsakaninsu ba. Ganin shine zai kaisu katsinar ta sake daurewar masa zancen dawowar Farah sai ya balbaleta da faɗa, duk da tasan bayason wargi bata taɓa ganin fushinsa irin yau ba. Ita kuma yanda yake mata ihu akai yasata fara kuka. Suna haka Mammah ta shigo falon. Saurin share hawaye Zinneerah tayi tana ƙaƙaro murmushi da yima Mammah ɗin dake binsu da kallo sannu. Daga haka ta zame ta gudu ta barsu, dan tasan tunda Mammah din ta shigo nan da kanta magana zatayi da shi. Da kallo tabi Zinneerah harta fice kafin ta maida ga AK dake ta wani bata fuska. “Abdul-Mutallab mi kaima yarinyarnan?”. Guntun tsaki yaja yana murza goshinsa. “Mizan mata kuwa Mammah, itace da neman fitina kawai”. Shiru Mammah tai tana kallonsa cike da nazari, sai kuma taɗan girgiza kanta da cewa, “Fitina kamar ya? Ai kowa Yasan Zinneerah bata da kwaramniya, dan nidai a zamanmu gidan nan banga wani abun ashsha daga garetaba sai dai ajizanci irin na ɗan adama kawai. Amma yarinya mai kawaici da kunya ga haƙuri. Sai dai idan kai ne da laifin tunda sarai na san halinka bawai baƙona bane. Miya haɗaku?”.. “Nifa Mammah babu abinda nai mata. Kawai ta isheni da zancen Farah ne”. Kallonsa kawai Mammah keyi dan maganar yanayintane da faɗa sosai. Ta sauke numfashi da gyara zamanta. “Abdul-Mutallab nasan Farah mai laifine tabbas, amma karka manta harda gudunmawarmu, kuma maganarta da yarinyarnan take maka tasan kantane. Dan wannan haline irin na mutanen ƙwarai da sake tabbatar maka ita mai tarbiyyace da hangen nesa. Ni bazance dole ka dawo da Farah gidankaba, amma zan baka shawarar ka daina ƙuntata yarinyarnan akan abinda ba laifinta bane saima alkairi da takeson ɗoraka akai. Ita rayuwa komai ɗan haƙuri ne ai. idan akai haƙurin sai komai ya zama labari wataran”. Shi dai kansa na ƙasa baice mata komaiba harta gama zancen Farah da Zinneerah ta ɗakko abinda ya shafesu sannan ya tsoma baki. Duk da Zinneerah tasan su Mahma basu rasa komai na rayuwaba sai da ta shirya musu tsaraba domin girmamawa. Musamman turarurrukan khumrah dana wuta da a koda yaushe

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182