Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 41

Chapter 41

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

more zasu koma gidajensu. d sukai masa dajin daɗin wannan karamci da suka samu daga manyan mutane da ada basu taɓa tunanin ganiba ido da ido sai gashi sun kasance jininsune ma ashe. _______★★ Sai da suka ɗauki hanyar gida ne cikin mamakin daya kasa sakin Abba har yanzun yace, “Nifa kaina a ɗaure yake har yanzu Hauwa'u. Wai dama kunsan familyn Alhaji Kabir Abdul-Mutallab Shira sune ƴan uwanku ɗinnan da kika taɓa bani labari?”. Saurin kallonsa Mmn sadiq tai da mamaki itama tace, “Kabir Shira kuma yaya? Muko a ina zamu san Shira? Bashi baneba”. Ƙaramar dariya yayi saboda fahimtar itama dai da gaske batasan hakanba, ya kalli Maryama ta mirror “Maryama kema baki saniba kenan?”. “Wlhy Yaya ban saniba. Nadai san Gwaggo Aminan na anan cikin kano da iyalanta, kuma sunda arziƙi suma, sai dai bansan sune ake kira Shira ba koda wasa”. “Ikon ALLAH kenan. To aiko waɗanan dai sune Shira Family da ake faɗa a cikin kano da wajenta. Kuma kenan wanda yayma Abdull-Mutallab alkairi har yaci sunansa shima jininsu ne. Wata hikima sai UBANGIJI kenan”. “Gaskiya kam Yaya. Dan wannan UBANGIJI ne kawai mai kusanta abinda suka kasance makusanta batare da su kansu sun saniba. Amma wlhy ni harma na tsorata. Sai dai sun bani mamaki yanda sukasan darajar mutane”. “Ai babu wani abin tsoro Hauwa'u, sanin darajar mutane kam tarbiyyarsuce hakan daga mahaifiyarsu. ALLAH ya ƙara mana zuminci da sanin darajarsa”. Sun amsa da “Amin ya rabbi” dai-dai suna isowa gida. Bayan Alhaji yayi fakin a inda yake ajiye motarsa anan ƙofar gidan duk suka fito suka shiga dan ba'akai ga rufe gidanba da alama su ake jira. Ilai kuwa a tsakar gida suka iske Maman Halima zaune baiwar ALLAH. Ta tarbesu da sannu da zuwa tare da tambayar mai jikin?. Saida suka tsaya wajenta suma suka gaisa da sakejin lafiyar gidan sannan suka shige dan duk a gajiye suke. Yaran duk sunyi barci kamar yanda Maman Halima dama ta sanar musu. Sai Little ne kawai kecan wajenta shima bayan tafiyar tasu zazzaɓi ya rufesa ashe. Itama dai Zinneerah wuni tayi kwance sai yamma zazzaɓin ya saketa harta ɗan fita tsakar gida ta zauna dan Maman Sakina da yaranta basu yini a gidanba. Wanka kawai sukai suka nema makwanci tunda a ƙoshe suke. Washe gari tunda safe Alhaji ya samu kira daga Alhaji Kabir Shira daya amsa lambar hannun Buba. Da farkoma bai gane mai maganaba sai da yay masa bayani. Cikin ɗan rikicewa Abban ya shiga gaishesa dan zai iya girmarsa ma ko'a shekaru. Sai kuma yanda yaji muryarsa ya sake rikitashi. Daga can Alhaji Kabir ya sanarma Abba ALLAH yayma Inno rasuwa tun asubahin yau, yanzu haka ga gawarta zasu ɗauka zuwa can gidan, sai suyi ƙoƙari suzo ayi jana'izarta dasu. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Abba keta faman ambata dukkan gaɓɓansa na saki lokaci guda. Da ƙyar ya iya fitowa zuwa sashen Mmn Sadiq ɗin yace musu su shirya zasuje asibiti. Sosai hakan ya basu mamaki, sai dai ganin bai basu fuskar da zasu tambaya ba ya sakasu yin shiru gabansu na faɗuwa. Dan sunaji a jikinsu lallai babu lafiya. Yau ɗinma dai haka suka shirya suka tafi su biyu kawai ko little ba'aje da shiba sabboda baijin daɗi. Zinneerah dai gara ita da sauƙi jikinta ba kamar jiyaba. Kasancewar gidan Alhaji Kabir Abdul-Mutallab Shira ba ɓoyayye bane a birnin na kano kai tsaye Abba ya nufi can dasu bayan ya kira Buba kawai ya tambayi anguwar. Gidane katafare sosai, duk da kuwa gidajen anguwar ma babu ƙaramin gida. Kasancewar Buba ya fito gate ya saka suka samu damar shiga babu wani gargada dan mutane basu kai ga fara isowaba. Ruɗanin mutuwar da suka samu ya hanasu damuwa ko tsayawa duban yaya gidan yake, balle tsarinsa. Kukan Hajiya Iya ya matuƙar sake tada hankalin kowa dake a gidan matuƙa. Su Mmn Sadiq kam ai ba'a magana dan suna tsananin so da ƙaunar kakar tasu, musamman daya kasance ita suka tashi suke gani tamkar mahaifiya a garesu tunda sun rasa tasu tun basusan kansuba. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi, dan ba'a binne Inno ba sai da tawagar ƴan bauchi ta iso. Inno uwace kuma kaka da wannan family bazasu taɓa mantawa da alkairan data ginasu a kaiba. To yau dai gashi ta tafi ta barsu da kewa da kuma alkairin data bari baya garesu. Dama ita kaɗai ta rage musu cikin iyaye. To ya rage nasu subi bayan nata da addu'a batare da gazawa ko ƙosawaba. (Ya rabbi kasa mu kasance cikin bayinka masu barinma bayanmu tarin alkairi ba sharriba. ALLAH yasa ranar barinmu duniya ta zama ranar farin ciki a garemu😭🙏🏻, ALLAH ka gafartama iyayenmu da bayin ALLAHn da suka rigamu tafiya badan sunyi gaggawaba🙏🏻😭). A ranar dai dole su Maman Sadiq anan gidan suka kwana. Yanda manyan mutane keta shigowa gaisuwa sai kasha mamaki da tabbatar da lallai Inno nada matuƙar daraja ga Hajiya Iya. Dan dukkan ahalinta suna ɗaukartane kakarsune uwa ga Hajaiya Iya, hakan yasa dukan harkokinsu suka tsaya cak harna tsahon kwanaki uku da aka amshi gaisuwa. Sai a ranar cikon ta huɗu ne ƴan Bauchi da suka rage suka koma gida, hakama sauran dangi dake wasu garuruwa kowa ya kama gabansa. Suma su mmn sadiq shirin komawa gidan sukeyi yau dan harma sunyi waya da Abba akan zuwa anjima zaizo ya ɗaukesu insha ALLAH. Shima dai kwanakin nan uku kullum sai yazo gidan wajen amsar gaisuwa, hakama mijin Gwaggo Maryama yazo harda ƴaƴanta biyu maza duk da ƙananune, amma a ranar suka koma. Da ƙyar Hajiya Iya ta aminta da komawar tasu, sai dai ta musu dogon sharaɗi da gargaɗin wannan karon bazata yarda da sakaci da zuminciba. dan su kaɗaine jinin inno mafi kusanci da suka rage a yanzu. Dama Inno bata wani haihu da yawaba. Yaranta biyune kacal a duniya, mahaifiyarsu sai mahaifin Buba. Kuma duk ALLAH yay musu rasuwa, shima Buba shi kaɗaine namiji a wajen mahaifinsa sai ƙannensa mata biyu duk sunyi aure anan Bauchi. Suma kuma sai da Hajiya Iya taja musu dogon gargaɗin kafin su wuce da safe. Sai su kuma su Mmn Sadiq ɗin da suka kasance suma su biyu kawai. Sun mata alƙawarin kulawa insha ALLAH a wannan karon. Da wannan yasa ta amince su koma gida ɗin dan Gwaggo Maryama ma da anyi bakwai zata wuce duk da ba taro zasuyiba, amma tace zata sake dawowa nan gidan taima Hajiya Iya sallama. Sai kusan biyar na yamma Abba ya iso tare da su Sadiq da Mama batasan dasu zaizo ba. Amma hakan da yay ya sakata jin daɗi matuƙa kamar yanda Hajiya Iya ma ta nuna jin daɗinta sosai. Har ƙasa su Zinneerah suka kai suna gaisheta da mata gaisuwa. Cikin jin daɗi ta kamo hannun Zinneerah ta zaunar kusa da ita tare da Aliyu. Suma su Sadiq tace su matso gareta. “Ikon ALLAH, nan ai Inno ce kamar an tsaga kara an karya”. Hajiya Iya tai maganar tana nuna Zinneerah da kanta ke a ƙasa. Sauran dake ɗakin suma suka shiga faɗin albarkacin bakinsu akan tsananin kamanni da Zinneerah ɗin keyi da marigayiya Inno. Dan duk wanda yasan Inno yaga Zinneerah yasan jinintace. Gashima ita Zinneerah ɗin ba saninta tayiba. Hajiya

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182