Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 173

Chapter 173

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

da ita zaman asibiti. Kwanakinta shidda a asibitin a wata safiya ta wayi gari da naƙuda. Sai dai fa tamkar cikin little jini ya ɓalle mata ga haihuwar shiru. Hankalin AK da kowama ya tashi, hakan yasa Dr Mahmud ya bada shawarar kawai ai mata cs kafin ta jigata ƙarfinta ya ƙare. Babu wani jayayya AK ya amince. Zuciyarsa fal tausayin halin da take ciki. Yayinda yake rayawa a ransa ko wannan tashin hankali da ta shiga a wancan karon na haihuwar little ya isa hana su Farah zaman lafiya da jin daɗi. Shikam sai yanzuma yake ganin matsalar da sukaita fuskanta na rashin jin daɗin rayuwar aurensu kullum faɗa da fitina shi da Farah ko wannan halin da suka zama sanadin jefa yarinyarnan ya isa su rasa farin cikin rayuwar aurensu ai. Dan Dr Mahmud ya tabbatar masa da haka tasha irin wannan wahalar a wancan karon ma. Alhmdllh an yi mata cs aka ciro ƴaƴa biyu mace da namiji. Zokaga murna wajen kowa. Shikam AK duk da yana murna da samuwar tasu hankalinsa nakan matarsa. sai da yaji tabbacin kasancewarta cikin ƙoshin lafiya sannan hankalinsa ya ɗan kwanta harya amshi jariransa ƙyawawa masu lafiya yana mai jerama UBANGIJI godiya daya bashi ƙyautarsu ta silar da ALLAH ya halatta masa bayan ya cire tsammani daga hakan. Inna daketa samun sauƙi tana zaune dan yanzu takan ɗan motsa jikin aka sanar mata da haihuwar Zinneerah. Hawaye kawai su Sa'a sukaga tanayi amma batace komaiba. Hakan yasa suka gagara fahintar na minene? Na daɗine kona nadama? Kona baƙin cikin har yanzu?. Oho masu karfin ajin ma basusan tanai ba. Dan cikin ƙanƙanin lokaci Shirawa suka cika asibitin domin taya Yayansu murna da samun wannan ƙaruwa. Waɗanda basa kusa kam irinsu Khalipha da Adilah tuni hotunan babes ya isa ga wayoyunsu. Addu'a dai kam sun shata kamar yanda Zinneerah ma keshan tata na fatan samun lafiya. dan kowa bai gantaba itakam har AK ɗin sai da daddare. Shima ya samu tanata barci. Ya ƙureta da ido cike da tausayi da ƙauna dan dukta rame sosai fiyema da lokacin da cikin na jikinta. Sumbatar goshinta yayi da hannunta yana mai jera mata addu'ar samun lafiya. Sauran ƴan uwa kuwa da abokan arziƙi basu sami ganintaba sai washe gari, zuwa sannan ta farka Alhmdllhi. Kuma tana gane kowa da amsama kowa gaisuwarsa. Lokacin da taga ƴan jinjirayenta da farin cikin dake shinfiɗe a fuskar AK murmushi ta dinga zubawa itama. a ranta tana musu addu'a. A fili kuwa sai ta dinga nuna alkunya su Hajiya iya na mata dariya. Sai dai har cikin ransu hakan da tai ya musu daɗi, dan yaran yanzu daba kawaici garemu akan ƴaƴaba koda na farine balle na biyu. Sai dai kuma wata sabuwa. wannan karonma tamkar haihuwar little ruwan nono ya zamarwa yaran damuwa. Dan da sun sha cikinsu duk sai yake kumbura suyita kuka. Ga namijin da son abinci tamkar ubansa. Hankalin AK ya tashi matuƙa da hakan. Amma da Dr Mahmud ya sanar masa haka dama sukasha fama akan little sai yaɗan sami nutsuwa. Yanzuma magunguna suka haɗa mata. Amma sai Mahma tace wanann al'amari kamar bana asibiti ba. Yanada nasaba da jinnu sai an dage sosai ma Zinneerah ɗin. Kowa yasha mamaki, amma sanin wacece ita a wannan fanin yasa duk suka amince. Itace da kanta ta fara harhaɗama Zinneerah magungunan gargajiya ta fara amfani dasu, tace insha ALLAH komai zai daidaita. Kwananta takwas a asibitin aka sallameta, Alhmdllhi zuwa yau kuma yara sunsha nono kuma babu wani matsala data biyo baya. Hakan ya saka kowa farin ciki dajin daɗi. AK yaga amfanin wannan sani na Mahma da yaketa ƙorafi akansa tunda gashi ta bama matarsa magani an kuma dace. A randa aka sallamesun ranar Mammah ta iso Nigeria, zokaga murna wajenta datai tozali da ƴan jikokinta. Su Adilah ma an iso daga Lagos suda tawagar Mommy. hakama Gwaggo Maryama. Inna ma da aka sallamota nan AK yace a kawo ta huta sosai kafin a maidata Danya. Kai tsaye gidan hajiya iya aka wuce da Zinneerah, za'ai suna acan sannan su koma gidansu su cigaba da jego kuma. Yara sunci sunayen Hajiya Iya da Baffah. *_Ameenatu & Kabeer_* za'ake kiransu (Amaan & Anam). AK ya zata Mammah zatai fushi, sai yaji batace komaiba. Yaji daɗin hakan, dan koba komai ya yarda ta dawo hankalinta yanzu kam. (An zinni sai muce ALLAH ya raya keda yayanmu angon jego). AK dai bason bidi'a yakeba. Dan haka aka shirya ƙwarya-ƙwaryar liyafa anan harabar gidan akaci akasha kowa ya godema ALLAH. Ƴan Danya, ƴan ɗanmusa ƴan bauchi sun cika gida dam domin taya murna. Hakama mai jego da jarirai sunsha ƙyau harsun gaji masha ALLAH. Kowa ka gani sai son barka. Amare ma da yawansu suna maƙale da cikkuna kanana sai fatan suma ALLAH ya saukesu lafiya. Kwana biyu da suna AK ya takura dole su Zinneerah suka tattaro suka dawo gidansu, aranar kuma ƴan danya da ƴan ɗanmusa suka koma. Suma ƴan bauchi washe gari suka kama gabansu sai kuna wata ta taso. Zinneerah tayi farin cikin kasancewar gidan cike da jama'a. Dan kuwa Ga mahma ga Mammah da suka koma sashen Farah suka zauna. Ga kuma Mama Ai, ga Yaya Gajeje da Inna. karima ma maƙalewa tai taƙi bin ƴan suna. Sai Tinene da Atine ne suka koma da amaryar baba. Ganin al'amura komai ya daidaita jikinta yayi sauƙi kamar ba yankata akaiba Alhmdllh yasata ƙudirin tunkarar AK da batun dawowar Farah gida. Dan itako tama fi son ta dawo hakanan tunda dai tasan zuwa yanzu ta horu. Dan su Meenal suna bata labari da sukaje da Granny kwanaki duba Farah ɗin abin gwanin ban tausayi. Duk sun fita hayyacinsu ita da Zakiyyan dan horo mai tsanani maimartaba yasa aketa musu batare da sanin kowa ba. Idan ka gansu bazaka taɓa ɗauka su din bane ƴan gayu ƴan ƙwalisa masuji da naira a bankuna. Suna zaune a falonta na farko ita da Yaya Gajeje da Karima, Yaya Gajeje tana shirya ƴan biyu da akaima wankan safe. Zinneerah ma tayi nata dan tana cikin kwalliyarta tamkar ba jego takeba. Har Karima na tsokanarta da tacigaba da kashe ɗauri baban ƴan biyu ya lallaɓo a samo gambo kafin arba'i. “Ya ilahi, dan ALLAH Yaya Karima barmin baki, ina ni ina wani gambo ana zaune ƙalau”. Dariya suka sanya mata, suna cikin dariyarne Mama A'i ta shigo riƙe da hannun Little dake kuka wai ya faɗi. Dubansu duk suka maida garesu, Karima na kamo hannun little ɗin da faɗin, “Yaya akaine Abdul?”. “Faɗuwa yayi, ya shigo da gudu yaci karo da kujera”. Mama A'i ta bama Karima amsa. Baki Zinneerah ta taɓe tana miƙama Yaya Gajeje pampas da za'a sakama Anam. Tace, “Maganinsa kenan, shidai a rayuwarsa yayi gudu, bansan daɗin mi yakeji ba sai kace wani ɗan ƙwallo”. Yaya gajeje ta katseta da faɗin, “Ai tsautsayi dai baya wuce ranarsa, sannu kaji Abdul ka daina gudu wannan gidan naku dake cike da kayan santsinnan, ni kaina babba idan ina tafiya wlhy a hankali nakeyi dan ji nake kamar zan faɗi”. Dariya Karima da A'i sukayi, Zinneerah taɗan murmusa da zancen Yaya Gajejen tana maida hankalinta ga little. “To gudun mi kakeyi?”. Baki ya tura gaba yana makalewa bayan Karima.

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182