Chapter 66
Chapter 66
ƙarfin hali tai mata barka da yamma. Batare da sauraren amsartaba ta gitta zata wuce saita dakatar da ita. Juyowa Zinneerah tai gareta fuskarta ɗauke daɗan murmushi. A ɗage sosai Farah dake ƙarema Zinneerah kallon sama da ƙasa tace, “Kema anan gidan kike?”. Kai Zinneerah ta ɗan jinjina mata kawai batare datace kimaiba. “Uhyim! Amma ban sankiba ni”. Kallonta Zinneerah tai cikin ido kamar zatai magana sai kuma tai shiru fara'ar fuskarta na raguwa. Dan tsaf ta fahimci dizgata matar Yayan nasu da taji suna kira da Aunty Farah ke neman yi. Itama Farah ɗin da har yanzu ke mata kallon wulaƙanci da isa duk da kuwa babu wani abin kushewa tattare da Zinneerah ɗin, dan duk da take ƙyaƙyƙyawa babbar yarinya babu abinda zata nunama Zinneerah, itama idan dirin jikinne ALLAH ya bata, musamman ma yanzu da take a kan ganiyarta na kammaluwar sirrikan budurci, sannan jikinta a mulmule yake dan ba siririya bace bakamar Farah ɗin. Ga fatarta kalar ɗaukar hankali gamai kallo. ta buɗe baki zatai magana Hajiya iya ta katseta dan dama ta saka musu idone taga mi Farah ɗin zatayi. “Tunda ba zuwa cikinmu kikeba ta yaya zakisan kowa. Ke Zinneerah wuce kici abinci”. Sum-sum Zinneerah ta wuce dining tana ƙoƙarin maida duk wani ɓacin ran Aunty Farah ɗin daya fara yunƙuro mata. Dan a rayuwa ta tsani wulaƙanci da raini da disgi a rayuwarta. Zata iya jure komai banda waɗannan abubuwan. Sosai su Jamal sukaji daɗin abinda Hajiya tayi, itako Farah a fusace ta miƙe tabar falon zuwa ɗakin mijinta. Yi hajiya iya tai kamarma bata ganiba. Ta kuma haɗe fuska dan karma wani a cikin yaran yace wani abu. Daga hakama hirar ta watse. Dan barin falon itama Hajiya iya tayi. Kusan 6 Zinneerah da tuni suka fice suna can harabar gidan anata hira ta shigo sashen hajiya iya saboda matsa mata da mararta tayi. Bedroom ta nufa inda ta iske hajiya iya na waya. Sai da ta kammala ta dubeta tana ajiye wayar data gama ɗin. “Fitinar Moddibo dabance wlhy. Inno dubamin ko su Rahi sun wuce?”. “Lah Granny ai sun tafi, bakuyi sallama bane?”. “Munyi sallama. Na zata basukai ga tafiyar banebam wannan fitinatunne yay kirana yanzu, wai ashe azumi yakeyi amma bai faɗaba tun ɗazu ba sai yanzu. Kuma wai abinci yakeson a haɗa masa. Gashi su Rahi ba tuwo sukaiba yau”. Cikin ƙarfin hali Zinneerah tace, “Granny yaya za'ai yanzu to?”. “Nima ban saniba to Zinneerah, sai dai ko ke zaki shiga kitchen ɗin ki haɗa masa tunda waccan malalaciyar matar tasa na tabbata ƙila ko shayi bata iya dafawaba balle wani tuwo”. Idanu Zinneerah taɗan waro waje da faɗin, “Kai Granny nikuma? Ta ina zai iya cin jagwalgwalona”. “Ci kuwa zaiyi harda santi Inno na. Kinga tashima kije kar ya dawo ya samu ba'ayiba ya fara baƙar zuciya danshi baya wasa da cikinsa. Tuwon zaki masa da ɗan wani abun mai sauƙi tunda azumi yakeyi”. Zata ƙara magana Hajiya Iya ta girgiza mata kanta. “Kinga babu abinda zai faru, lafiya lau zakiyi insha ALLAH kinji ƴar albarka. nina ai dana idar da sallar magrib zanzo nama tayaki muyi tare”. Jin abinda Hajiya Iyan ta faɗa ya sata miƙewa tana fadin to ta fice zuwa kitchen da kwarin gwiwarta. Sai da ta fara karanto addu'ar nasara kafin ta ɗauraye tukunya tasa ruwan tuwo dai-dai misali, dan itama dai tana ganin tuwon zataɗanci ko zataji sassaucin ciwon marar nan da taketa dannewa dan karta tadama hajiya Iya hankali. Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala tuwon semo.. data bama nutsuwa sosai gudun yimasa kuskure, sai da ta kammala kwashewa zuciyarta keta ƙara ƙarfafata akan miyar da taketa tunanin masa tunda ta fara tuwon. Ɗanyen kifi ta cira ta gyara tasashi a wuta da kayan ƙamshi da albasa dan rage masa ƙarni. Kafin ta koma ta ɗiba kayan miya zallar attarigu da tattasai sai albasa da tumatur guda biyu kacal ta wankesu suma tasa a blender da ɗan ruwa bamai yawaba can tai musu markaɗe ɗaya da yay kamar jajjage amma yaɗara jajjagen laushi kaɗan. Kifin ta sauke ta tsamesa a ruwan ta buɗesa ta cire ƙayarsa duka ta farfasashi, ta ƙara ɗora tukunya tasa manja a wuta ta zuba wannan fasashshen kifin da albasa da magi ƙwara ɗaya ta rage wutar can ƙasa. Sallamar hajiya iyace ta sakata juyawa tana kallonta. Ta ƙaraso cikin kitchen ɗin tana magana cike da tsokana. “Wai wai, anya kuwa yau kunnen moddibo bazai kai ƙasaba Inno. Irin wannan ƙamshi haka da aka cika mana gida”. Dariya Zinneerah tai tana faɗin. “Kai Granny bammafa fara miyanba”. “Amma kuma ga ƙamshi ya cika ko ina” Hajiya iya ta faɗa tana buɗe tukunyar data saka kifin nan dake fidda ƙamshi mai daɗi a cikin manja. “Masha ALLAH miyar mi zakiyi?”. “Granny ɗanyen kalkashin nan dana gani da zanyi”. “Eh lallai kinyi tunani mai ƙyau, dama ɗazun Rahi tazo dashi wai ko zamuyi amfani dashi a gidanta suke ɗan shukashi”. “Aiko gashi yayi ƙyan fita Granny. shiyyasama ya birgeni. Kuma ta taimaka ta tsinkesa tun daga can yankawa kawai zanyi yanzu nasa a wuta”. “To bara na tayaki yankawa saiki haɗa miyar”. Babu musu ta bama Hajiya iyan, tunda dama tanason ɗan haɗa masa ko fruit salad ne haka da ɗan coconut juice idan zata iya. Ganin kifin ya mata yanda takeso ta zuba kayan miyarta a ciki da daddawa ta ƙara rufewa. Inda suke ajiye kayan fruit taje ta ɗauka komai dai-dai misali ta ajiye gefe, ta ɗauka kwakwa ta fasata itama ta ajiye gefe. Komawa tai ga miyarta taga kayan miyan yaɗan soyu, saita zuba ruwa ɗan kaɗan da kayan ƙamshi da magi amma ba star ba dan yana hana miya yauƙi. Da duk abinda take buƙata na saka miya ƙamshi ta saka ta maida ta rufe a binta da sake maida wutar can ƙasa. Dai-dai Granny ta gama yanka mata ɗanyen kalkashin. Amsa tai tana mata sannu da godiya. Granny ta bita da kallo tana murmushi. Madaidaiciyar tukunya ta samu ta saka kalkashin nan dan babu zancen wankesa shi. Tasa ruwa kaɗan da kanwa ta barsa a buɗe wutar naci daidai misali. Fita Granny tai dan an kira sallar isha'i, ita kuma tahau gyaran fruit salad ɗinta dan ɗan kaɗan zatayi ba yanda aikin zai mata yawaba. Saiko gashi ta gama a ƙanƙanin lokaci, tasa flavor na gwaba dana strawberry ta motsa. Kaɗan ta ɗan-ɗana, jin zaƙin ya mata dai-dai ta ɗaukesa tasa a fridge ta dawo wajen miyarta da dudduba. Komai yayi, kalkashinma ya dahu, kashe gas ɗin tayi ta koma wajen gyara kwakwar da zatayi juice itama, tabar kalkashinta dayay kauri sosai yana hucewa. Hakama miyar kayan miyanta tayi kauri yanda ko an haɗata da kalkashin bazata tsinkashiba. Sai da ta kammala haɗa coconut juice ɗinta ta saka a fridge shima sannan ta tattara kayan data ɓata ta wanke tsaf sannan tazo ta juye kalkashin cikin soyayyun kayan miyarnan ta motsa da kyau suka haɗe. Ɗanɗanawa tai taji komai dai-dai yanda take fata duk da dai akwai fargaba tare da ita har yanzun. “Inno an gama ko?”. Hajiya iya data sake dawowa ta faɗa tana shigiwa. “Eh Granny duk an kammala, amma dan ALLAH ki ɗanɗana wlhy inajin tsoro”. “Haba ɗiyar albarka nasanma komai yayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182