Chapter 58
Chapter 58
ke mata daɗi akan Zinneerah. dan bata da burin daya wuce taga yarinyar ta tagayyara ta wulaƙanta a duniya, saboda kawai tazo matsayin ƴar kishiyarta. (Ƴan uwana mata dan ALLAH mu canja, mu daina saka yara a kishinmu. sannan kishinma mu dinga sassautama zukatanmu. Nasan kishi dolene domin kamar jininmune. To amma suma mazan idan suka fahimci kana musu kishi na hauka duk da sonsu ne yake jawo hakan saisu maidaka wawa mahaukaci. ka kuma fita a cikin ransu ma baki ɗaya su koma ganin baƙinka maimakon hasken da kake dashi a garesu. Babu amfani kai burin lalacewar ɗan wani ko shigarsa wani bala'in rayuwa. Dan kaima ba tsira naka zaiyiba wlhy. dan ba'a taɓa shuka dawa a girbi shinkafa. Sai ka ƙyautata zato da addu'a ga ɗan wani kaima ALLAH zaiji ƙanka ya ƙyautata rayuwar naka ƴaƴan insha ALLAH. ALLAH yasa mufi ƙarfin zukatanmu😭🙏🏻). Yanzunma wani ƙauye can nesa dasu sosai akai mata kwatancen wani malami shine taje. A yanzu haka dai ya mata alƙawarin dawowar Baba nanda kwanaki bakwai, idan har bai dawo ɗinba zai biyata kuɗin daya karɓa a wajenta. Hakkane ya sata tahowa gida cike da ƙwarin Gwiwa ko ranar dake dukanta da azabar tafi bataji. Shiru ta iske gidan babu kowa. ta zube ƙarƙashin bishiyar tsakar gidan nasu tana maida numfashi da ƙyar. Ta kusa mintuna biyar a haka kafin ta miƙe zuwa randunansu dan tasha ruwa. Wayam ta samu tabbacin dai Tinene data barma sallahon ɗebo musu ruwan bata ɗebo ɗinba kenan. A take ranta ya ɓaci taja ƙafafunta da ƙyar ta koma ta zauna dan har juwa takeji saboda yunwa. Ko karyawa bataiba ta fita, ɗan hatsin da baba ya bari a rumbu duk sun cinye ta salwantar da wani kuma wajen bin malamanta na tsiya. Hakan yasa abincima sau uku a gidan wataran gagararsu yakeyi. sai idan Yaya Gajeje taji tausayinsu ta ɗakko ta kawo musu. Koda yake mafi yawancin lokacima itace ke zama da yunwar, dan Tinene sai dai ta ganta da kayan ciye-ciye ta shigo. bata isa tambayarta kuma ina ta samosuba saita hayayyaƙo mata da rashin kunya. Wani lokacinma bata tambayar tata amsa take itama taci saboda wahala. Sa'a kuwa yanzu takan jera kwana huɗu biyar bata kwana a gidanba. Tuni ta koma gidan Baba Rabilu abinta, dan ɗansa ya maidata makaranta tana zuwa. da Inna ta nuna bata yarda bane yasa Sa'a tattara inata-inata ta kona can gidan. Sai randa ta bushi iska take zuwa ta kwana anan tunda yanzu babu talla Malamai sun cinye jarin Inna Asaben. Miƙewa Inna tai tana tsinar Tinene a cikin ranta, dan yunwa da wahalar tafiya tasa koma magana mai ƙarfi bata iyayi. Ɗakinta ta shige ta faɗa saman gado da fatan ALLAH ya kawo wani a cikinsu Sa'a ɗin ya taimaketa da ko kunu ne taɗan kurɓama cikinta ko taji dama-damar tashi ta bizne aykin malam. ALLAH kuwa ya taimaketa babu jimawa ta farajin motsi a tsakar gidan da ƙarar taunar chewing gum. ko ba'a faɗaba tasan dai Tinene ce. Dan itace mai ɗabi'ar cin cingam ɗin a koda yaushe. Idan tai mata magana tace mata ƙoshi ya sakata ci danta rage nauyin cikinta. Dole Innar keyin shiru dan Tinene kam ta fara fin ƙarfinta. Gashi kuma wani lokacin tana ɗan samun mai daɗi a wajenta taci. Bankaɗa labilen da akaine ya sakata ɗago idonta ta kalli ƙofar. Tinene dake tsaye a bakin ƙofa tana cakal-cakal da cingam a baki cikin rashin ladabi tace, “Oh oh, wai se yanzu kike dawowa gida Innarmu? Ke dai baki gajiya da mikama maluma kuɗi suna cinyewa mu baki anhwana mana da ko taro ba a ciki. Naga dai Baban da ƙahwarsa yabar gidan ba saceshi akaiba halan”. Kasa cemata uffan Inna tai, sai kanta data girgiza kawai. Hakan datai ya bana Tinene haushi, harta saki labulen da niyyar barin wajen Inna ta ƙwala mata kira cikin ƙarfin hali. “Tinene wai nikan yaushene zaki natsune? Ni yanzu duk bama wanga ba. Dan ALLAH idan da goma hannunki ko murtala kije nan gidan dije ki sayo mani kunu koba suga nasha”. Baki Tinene ta zunɓura gaba. kanar zatai magana sai kuma taja tsaki fuuu ta fice tana ƙunƙuni. “K kuɗinki na wajen bokaye da malamai ni kuma kin sakama nawa ido mu ramtsesu tare. Bayan duk kece kika jehwamu a wagga rayuwa ta yunwa da talauci wajen neman baƙin asirinki mtsoww”. Da wanan mitar taje ta sayo kunun na goma ta kawo mata dukda ba wani na kirki bane. Da rawar jiki kuwa Inna ta amsa tahau sha duk da zafin da yake da shi. Ta saki gyatsa tana ajiye kofin duk da bata ƙoshi bane yanda take buƙata. Daga haka ta zame ta koma kwance tana zufa. Tinene ta taɓe baki da nufar hanyar ficewa gidan tanama Innar tasu baƙar magana. (Hhhh yanzu aka fara wasan Hajja Asabe😂😂😜). ________________________★★ Washe gari lahadi ma duk suna a gidan, sai dai banga Khalipha da Yah Adnan da suka tafi jigawa. Dan jiya bai samu damar zuwanba saboda wani uziri. Bayan sallar la'asar duk suna zaune a falo suna ɗan hira iyasu ƴammatan sai ga Safiyya da ita kaɗaice bata gidan. Momie ta aiketa can wajen yayarta kai saƙo. A yanda ta shigo falon kamar wadda aka koro ya sakasu duk suka zuba mata ido. “Ke lafiyarki kuwa?”. Hajiya iya data kasa haƙuri ta faɗa tana duban Safiyyan. “Humm Granny inafa lafiya, wlhy wani abun al'ajabi da ruɗani nai gamo dashi a yanzun nan hanyata ta dawowa daga gidan Umma”. Duka falon maida hankalinsu sukai a kanta, kowa nason jin dami tai gamon?. Wayarta ta lalubo a jakka tai ƴan danne-danne sannan ta miƙama Hajiya iya. “Granny dan ALLAH kikalli yaron nan dawa yay miki kama?”. Cikin rashin damuwa Hajiya Iya ta amshi wayar. Yanda tai kasare tana kallon wayar ya saka su Meenal duk suka zuba mata ido suma. Itama da alamun makamancin irin ruɗanin da Safiyyar ta shigo da shi tace, “Keko Safiyya a ina kikaga wannan yaron haka?”. “Wlhy Granny a Napep. Mun taho da driver motar ta mutu a hanya. Shinefa nace masa bara na tare napep na ƙaraso gida. Mun daɗe tsaye yanason taremin ba'a samuba sai da ƙyar ya tsaida wanda ke ɗauke da maman yaron nan. Hajiya iya daketa faman jinjina kanta tace, “Amma wannan kamanni da mamaki a cikinsa. Koda yake hakan kan faru koda baka haɗa komai da mutumba. Amma ita matar a ina take?”. “Wlhy ban tambayetaba Granny, amma da alama wani waje zatajema. Bama tasan na ɗauki hoton yaronba dan cikin dabara nayi”. Wani irin nannauyan numfashi hajiya iya ta sauƙe. Sai kuma ta miƙama Abidah wayar ganin duk sun zaƙu su gani. A haka samarin gidan dake shigowa a tare sukazo suka samesu. Ganin yanda aketa ƴar bayayya da waya ya sakasu tambayar ko lafiya?. Safiyya ce tai musu bayani. Amsar wayar suma sukai duk suka gani. Duk wanda ya kalli hoton sai ga mamaki ya bayyana a fuskarsa da ruɗani. Duk wannan al'amari dake faruwa Zinneerah nacan ɗaki tana shirya kayanta data kwaso a ɗakin Yah Adnan cikin wadrobe ɗin Hajiya iya. Hakan yasa batasan hidimar da akeyiba. Dan so take ta gama shiryasu a daren yau tunda gobe idan ALLAH ya kaimu monday akwai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182