Chapter 106
Chapter 106
mahaifiyarsu Hajiya iya. Sama-sama suka gaisa ya shiga ciki watsa ruwa. Koda ya fito massallaci suka fice da matasan ƴaƴansa. Sai da aka idar da sallar isha'i sannan suka sake shigowa gidan. Sai lokacin matan gidan suka sami damar zuwa masa sannu da zuwa da ALLAH ya sanya alkairin ɗaura aure da sukaji a bakin ƴaƴansu. Hakama Mommy ta shigo har falonsa inda aka shirya musu abinci tare, cikin farin ciki sukaci abinci shi da ƴar uwarsa. Sai da suka kammala suka sami zaman yin hira sosai, inda a cikin hirar ne Baffah yay kiran Khalipha ya sakashi ya haɗasu da Hajiya iya. Tsaf ya kwashe mata komai ya sanar mata game da ɗaurin aure. Duk da yasan zatai farin ciki dama dajin haka sai yaji murnar data nuna ma ta zarta wadda yay zato, dan albarka dai ya shata har babu adadin ƙididdiga. Suna tsaka da wayarne AK da Huzaifa suka shigo ɗakin. Kai tsaye wajen Mommy data ware masa hannu ya nufa. Ya zauna kusa da ita tare da ɗan hugging ɗinta ta gefe yana murmushi har haƙoransa na bayyana. Dan har ransa yana ƙaunar ƙanwar mahaifin nata saboda itama tana ƙaunarsa. “Ina cewa zanje na gaisheki tunda wancan zuwan ban samu shigaba sai kuma gaki?”. Murmushi Mommy tayi dakai hannu ta shafa kan AK mai maganar. Tace, “Ja'iri anya na yarda dakai kuwa? Yanda ka ƙwace mana Inna ka kai London bamma tsammaci zuwanka nan kusaba. Nazata sai bikin su Saffiya, ashe ma kai zaka fara angwancewa kafin su. To ALLAH ya sanya alkairi ya bada zaman lafiya na har abada”. Kansa ya duƙar yana murmushi, akan laɓɓansa ya amsa da amin. Cikin tsokana Huzaifa yace, “Aini Mommy soma nake naga wace mai sa'a ce ta shiga tsakkiyar lailah Majnoon ɗin nan haka? Dan naga alamar itama da ƙarfinta take dan tun ɗazun murmushi yaƙi barin fuskar ɗan naki”. Dariya Mommy da Baffah suka sanya, AK kuma ya zubama Huzaifa harara da masa daƙƙuwa. Cikin dariya Mommy tace, “To ai kaga ya nuna maka shi ba matsoraci bane, cikakken jarumine tunda gashi har yaje ta biyu, kai kota ɗayanma ka kasa”. “Faɗa masa dai Mommy. Dan wlhy ban taɓa ganin matsoracin irin wannan yaron ba, maybe sai ya tsufa mu taimaka masa da wata yafendo a dangi”. Filo Huzaifa ya ɗauka ya jefama AK mai maganar, saurin cafewa AK ɗin yay yana masa gwalo. Su Baffah dai nata musu dariya. Dan kowa yasan dama inhar Huzaifa da AK suka haɗu duk rashin son maganarsa sai ya takura masa yayi harma suyi faɗa. Suna tsaka da wannan nishaɗin Moos'ab da Haneef suka shigo ɗauke da little daketa faman zuba musu surutun da ba fahinta sukeba sosai suna dariya. Kusan a tare suka ɗago suna sauke idanunsu akan little. Yayinda Mommy ta sauke wata sassanyar ajiyar zuciya tana kallon yaron ko ƙyaftawa babu da tsarkake sunan ALLAH buwayi gagara misali daya sanya wannan kamar mai ƙarfi tsakaninsa da AK, Huzaifa kuwa hannu ya miƙa masa alamar yazo. Amma sai ya maƙalƙane Haneef yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Haneef ne dake ɗauke dashi ya ajiyesa a tsakkiyar falon yana faɗin, “Bara muga wajenwa zai je”. Tsit falon yay sunason suga yaya za'a kwashe? Dan yanda little ɗin ke musu kallon ɗaya bayan ɗaya dolene ya baka dariya. Kamar wanda aka raɗamawa sai ya nufi inda Baffah yake, duk zatonsu wajen Baffah ya nufa, dan haka Baffah dake murmushi ya sake gyara zamansa. Yana zuwa gab da shi sai ya zagayeshi ya miƙa hannu zai tsinki appale ɗin dake a jikin flower ɗin kusa da baffan kamarma baiga kowa a falonba. Hannu baffa ya kai ya dungure ƙeyar little ɗin yana faɗin, “Like father like son” fuskarsa ɗauke da murmushi. A take duk suka kwashe da dariya, banda AK da yay ƙasa dakai kawai yana murmushi, dan shima dai yanda Little ɗin ya wanu basar da kowa ya bashi mamaki, dan sak halayyarsa na basarwa da mutane ke yawan faɗa masa ya iya. Hannu Baffah yasa ya ɗaukesa ya ɗaura a cinya yana faɗin, “Ja'iri, saika mana yanga dan kaga muna son ɗaukarka?”. Kamar little yasan mi baffan ke nufi ya wani ƙyalƙyale da dariyar data basu mamaki, dan sanda suka shigo duk da surutu yakema su Haneef dan zuwa yanzu ya saba dasu fuskarsa a turɓune take. Suma dai duk dariyar sukayi kafin Baffah ya mikama Mommy shi. Zuciyarta cike da rauni ta amshesa tana murmushi, har cikin ranta jitayi so da ƙaunar yaron na shigarta. musamman yanda yake kamanni sosai da AK kamar yayi kaki ya aje. Fita su Moos'ab sukayi dan son zuwa su huta. hakanne ya bama su Baffah damar tattaunawa akan zancen little dake lafe jikin Mommy. AK dai baice komaiba. Sai su uku suke maganarsu da juya al'amarin. Ganin sunata jefama AK tambaya a ɗan fakaice Huzaifa yace, “Niko dai zuciyata nason min wani hasashe, amma dai kubari zan sake bincike kafin kuji minene”. Baffah dake kallonsa yace, “Son faɗa mana mana karka barmu a tunani”. “A'a Baffah, banson inyi gaggawa ne, amma dai kuyi haƙuri na ƙara nazari akai”. Haƙura sukai suka barshi akan yayi nazarin. AK da dai dama ba saka baki yake a zancenba sosai ya miƙe yana faɗin, “Bara naje na kwanta wlhy na gani Mommy”. “Ai ya isa kam agaji Babana. jeka huta kaji”. “Thanks you Mommy ”. AK ya faɗa yana murmushi da nufar ƙofa. Kamar an tsikari Little dake wasa jikin Huzaifa sai cayay “Abbah zanje”. Danshi kowa Abba ne a wajensa indai namijine babba. Cak AK ya tsaya tare da juyowa yana kallonsa. shiko da gudu ya sauka a jikin Huzaifa ya nufesa. Babu musu ya kama hannunsa suka fice. Da kallo duk suka bisu cike da sha'awa, a ransu sunajin tausayin yaron da baijiba bai ganiba, amma yaya zasuyi da ƙaddara kowa da irin tasa. ALLAH ya rubuta cewar ta hanyar daya samar da yaron yaso azurtashi da shi, ya kuma fisu sanin dalilin yin hakan, fatansu kawai ALLAH ya rayashi ya albarkaci rayuwarsa data ƙannensa masu zuwa. Huzaifa ne ya sake sauke numfashi, hakan yasa su Baffah dawo da kallonsu gareshi, cikin jinjina kai yace, “Ku daina zargin AK ya samar da yaron nan ta hanyar banza. Akwai wani voice recording dana taɓaji a wayar Adilah batare da itama tasan wayar ta naɗa ba, sai dai bai isa zama hujjaba sai nayi bincike”. Da sauri Mommy tace, “Voice recording kuma akanmi?”. “Kuyi haƙuri na bincika ɗin zaku sani, kudai ku tayani da addu'a ku kuma bani lokaci”. Cikin jinjina kai Baffah yace, “Mun baka ɗan albarka. ALLAH yayi jagora muji alkairi”. Da amin Huzaifa ya amsa yana miƙewa. dan shima so yake yaje ya kwanta ya huta. ________________________★ *_LONDON_* Ganin yanda Hajiya iya ke murna ya saka Khalipha samun waje ya zauna danta gama ta gumtsa masa. Tana kuwa ajiye wayar ta ɗaga hannu sama tana ambaton Alhmdllh. Katseta yayi da faɗin, “Niko Granny taƙaita addu'ar nan ki faɗamin minene?”. Hannu ta sauke tana masa daƙuwa. Sai kuma ta ƙara washe baki da gyara zama. “Burina ne ya cika Abdul-Mutallab ƙarami, ALLAH ya tabbatar da tarkon dana ɗana. Na kuma daɗe ina mafarki da addu'a. Bazan ɓoye makaba yau dama saboda Moddibo nasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182