Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 34

Chapter 34

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

Abba yace, “Koma ki ɗakko zani kizo ki goyashi akwai sanyin safiya”. Cike da kunya ta juya ta koma. babu jimawa ta dawo da zanin goyon a hannu. Maman Sadiq ce ta amshesa ta saka mata a baya dan har yanzu ba wani iya goyon tayi da ƙyauba. Kusanma wannan shine karo na uku kacal da zata goyashi. Dan mafi yawancin lokuta su ƴan biyune ke goyashi ko Maman Halima ko ita Maman Sadiq ɗin. Har Sadiq da Abdull goyamusu akeyi, ƴaƴan maman sakina ma sukan faki ido suzo su ɗaukesa saboda kusan shine ɗan ƙaramin yaro yanzu a gidan, sai yazan abin sha'awa ga kowa banda maman sakina da ko sau ɗaya bata taɓa ɗaukarsaba ma ita. Da ƙyar Maman Sadiq ta samu goyon yayi dai-dai tanata ma Zinneerah ɗin faɗa. Ita dai batace komaiba sai dariya takema a ranta wai mama ta dage da masifa akan ɗan aljanu, sai randa sukazo suka ɗauke abinsu taga yanda kowa zaiyi a gidan ai. Bayan fitar Abba da Maman Sadiq Zinneerah ta hau gyaran ɓangaren nasu kamar yanda ta saba, Sadiq kuma suka shige suna shirin makaranta dan an koma hutu. ★★★★ Haka rainon Little Abdull ya cigaba da gudana kusan kaso biyu a hannun Maman Sadiq da maman Halima ne. Kaso ɗaya kuwa Zinneerah na rabawa dasu Sadiq. A haka sukai arba'in yaron yay ɓulɓul masha ALLAH, ga ƙyawunsa na sake fitowa. Yaro gaba ɗaya bai ɗakko kamannin Zinneerah ba ta fuska sai halittar yatsunsa na ƙafa da hannu da abinda ba'a rasaba. Amma daga basuba kamanninsa daban da nata. Takan zauna ta dinga kallonsa da shiga dogon nazarin ko zata iya gano da wanda yake kamar. Amma sam bata iya hasaso komai ga kamannin nasa. Sosai jikinta ya warke, idanma baka saniba bazaka taɓa ɗauka cs akai mataba. Musamman da yazam bayan dawowarsu gida maman Sadiq da Maman Halima kulawa da gyara na musamman suke mata wanda ita bawani gane inda suka dosa take ba. Abinda kawai ta sani tanajin daɗin jikinta sosai balle yanzu barci take sosai tamkar kasa. Ga lafiyayyen abinci da take samu kuma ga kwanciyar hankali. Sam bata wani tunawa da Inna. Garama Babanta da Yaya Sa'a da Yaya Gajeje. Takanyi kuka a duk sanda sukazo mata ranta koda a boyene. Sai ko Khalipha da har yanzu yake maƙale a zuciyarta. Gashi yanzu Naziru ko gidan yazo baya mata maganarsa ma. Itako kunya ta hanata sake tambayarsa ko yanzu yana samunsa. Bayan tayi arba'in da kusan wata ɗaya Maman Sadiq taga zaman nata baida wani amfani. sai dai taci ta ɗanyi aikin gida ta kwanta barci. Samun Abba tai da shawara akan Zinneerah ɗin ta shiga wata islamiyya dake anan kusa da su ta ƴanmata, inda su Sakina ke zuwa da yamma. To sunayi da safe kuma zuwa ƙarfe ɗaya ga yaran da basa zuwa boko. “Eh shawaranki mai ƙyau ce Hauwa'u, nima kuma maganar fara karatunta dama yana raina. Na bartane kawai Abdul-Mutallaf ɗin ya ƙara ƙwari sannan. To amma tunda dai naga bama itace ke rainonsa ba gara ta fara islamiyyar kawai itama bokon sai a nema mata inda zai dace da ita dan nasan da wuya ace acan tayi karatunma”. Cikin gamsuwa da bayaninsa Maman Sadiq tace, “ALLAH ya saka da alkairi yaya, sai dai duk da bamu taɓa maganar karatu da itaba sai naga kamar taɗanyi acan, dan naga wasu lokutan idan su Abdull na Assignment haka takan saka musu baki harma tayi gyara a wani wajen”. “A'a ikon ALLAH, to kinga kiramin ita dai muji ta bakinta, kinga ai sai mu sami madafar kamawa ko”. Miƙewa tai tana amasa masa da to. Babu jimawa kuwa sai gasu sun dawo tare da Zinneerah. Bayan ta gaida Abba sai yake tambayarta ajinta nawa a makaranta?. Duk da a bazata tambayar tazo mata sai gashi ta saki murmushin da ya basu mamaki. Kanta tsaye cike da zumuɗi tace, “Abba nayi jsce ma ai”. “Ikon ALLAH, to to Alhmdllh. Ashe ɗiyar tawama ƴar boko ce bamu da labari. Amma gaskiya naji daɗin hakan sosai, kuma na yaba ƙoƙarin babanki anan....” Cikin suɓutar baki tace, “Lah Abba ai bama shine ya sakaniba. Inagama Baba fa baisan ina zuwa makarantaba, dan shifa babu ruwansa dani a gidan. Ni saima nayi kwana hudu biyar ban gansaba wani lokacin”. Duk idanu suka zuba mata, a ransu kuma cike suke da zumudi da jin daɗin yanda ta fara sakin jiki da faɗa musu abinda ke ranta. Maman Sadiq ce tace, “To wani guri yake zuwa da har kike kwanaki baki gansaba?”. “A'a mama, yana nan a gidan, kawai dai bansan miyasaba shi bayason ganina ne wani lokacin, wani lokacin kuma daga sallar asuba idan ya fita bai dawowa sai munyi barci”. Babu wanda ya iya magana tsakanin Maman Sadiq da Alhaji. Maman Sadiq dai rayawa take a ranta yaushe al'amarin baban ya taɓarɓare haka kuma?. Dan tasanshi a da mutumne tsayayye akan iyalansa da gidansa. Dan ko talla wannan bai yarda yaronsa ya fita ba. Duk inda akai sallar isha'i kuwa yana gidansa, bazai sake fitaba sai asuba. Da an idar da salla zai dawo gida ya karya sai rana ta haska zai fita kasuwa wajen sana'ar sai da dankalinsa ɗanye da makani....... Tambayar da Alhaji ya jefama zinneerah ce ta katse tunanin Maman Sadiq ɗin ta maida hankalinta garesu. “Karki damu yarinyata, haka rayuwa take kullum cikin tsere-tsere da jarabawa. To amma wanene ya kaiki makarantar?”. Kunyar wanda zata ambata ɗin ya sakata jan lokaci kafin ta bashi amsa. “Abba Babawo ne ya kaini kafin ya koma yace Yaya Karima yake so”. Duk da a dunƙule tai maganar kasancewarsu manya masu hangen nesa sai duk suka gano inda ta dosa kai tsaye. “ALLAH ya saka masa da alkairi”. Abba ya faɗa dajin daɗi. Amin sukace ita da maman Sadiq. Daga haka Abba ya sallameta suka cigaba da tattaunawa shi da matarsa. “Hauwa'u kinga fa'idar shiru da mukai mata akan son sanin bayanta ko? Ina mai tabbatar miki inhar zamu cigaba da binta a haka harma abinda bamuyi zatoba sai munji daga gareta wataran. Kinsan shi yaro tamkar dabba yake, mai kula dashi da mai sake masa shi yake sakewa da shi shima. Dan haka ki sake nutsuwa wajen fahimtarta a hankaki komai da muke buƙata zai fito. Domin a fahimtar danai mata rashin samun sake a inda ta baro ya sakata kasancewa shiru-shiru kamar mara wayo. Amma ras take kuma tanada kwaramniya, sai a hankali zakiga ta hau bisa hanya da ƙyau”. Murmushi maman Sadiq tayi har haƙoranta na bayyana. “Maganarka haka yake Yaya. Dan yanda ma zakaji tana faman shagali dasu Sadiq idan na barsu su kaɗai ya isa tabbatarwa. Idan kaji bakinta cauy-cauy baka taɓa cewa itace ke zuba zance”. Dariya shima Abban ya sakeyi. “Ahaf kaɗanma kenan. Bayan takurar data taso a can harda cikin yaron nan ya sake dankwafe dukkannin kuzarinta da karsashi. Amma zata ware tsaf ta bama kowa mamaki. Naga alamar kuma tanason karatu ma sosai, dan jin daɗinsa ya sakata bamu labarin abinda bamu tambayetaba ma”. Haka suka cigaba da hirarsu cike da fahimta dajin daɗi. Yayinda Zinneerah kecan tana tsallen murna zata koma makaranta. Harda ɗaukar Little dake barcinsa ta hau masa rawa. Aiko ya farka ya birkuce mata kuma.

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182