Chapter 178
Chapter 178
silar samun lafiyarta ai. Babu bakin magana ga Inna Asabe danya musu murus, sai kukan zuci da haɗiyar zuciya kawai. Randa suka cika kwanaki huɗu babu daɗi babu ƙari sai ga Moos'ab yazo kwasarsu. Zinneerah bataso hakaba dan catake zaiyi haƙuri sukai 1week ɗin data roƙa. Amma hakanma sun gode dan batai zaton zai bari ba. Aiko data dawo tasha mitar shi an barsa shi kaɗai a gida kamar mara gata. Dariya ta dinga masa da bashi haƙuri. daga ƙarshe tabi hanyar data dace wajen lallashin abinta. Gaba ɗaya gidan yanzu sai take jinsa wani iri da duk suka tafi, sauƙinma ta taho da ɗiyar Yaya gajeje zata ɗan mata hutu mai suna Saliha. Yarinya ce ƙyaƙyƙyawa kuma nutsatstsiya, shekaranta goma kwata-kwata. Tarbiyan yarinyar yasa ta shiga ran AK yace makaranta zai nema mata dan tazo kenan bazata komaba. Sosai Zinneerah taji daɗin hakan kuwa taita masa godiya. Bayan sati uku da dawowarsu daga Danya da ƙyar ya barta taje Minna wajen Gwaggo Maryama. Aiko taji daɗin wannan zuwa harda ƴar ƙwallarta. Kwanansu biyu acan suka dawo, Hajiya iya ta sake jajubarta suka tafi bauchi. AK nata fushi batabi takansaba tace yawan arba'in Zinneerah keyi dana aure daya hanata yi. Yama zai yi da tsohuwarnan inba yay gum da bakinsaba. Dan yana tankawa zatama iya ƙwaƙulo wasu dangin a wani garin tace Zinneerah taje. Satinsu ɗaya a can suka dawo. Shima kuma sai ya fara musu shirin zuwa Morocco daga can zasu wuce London su ɗan huta tunda little sun sami hutu. Fatansa kuma ya tarkato su Mammah su dawo a maida aurenta da baffah tunda yaga sun sakko an daina faɗan masoya saita waya idan sun kira juna da nufin gaisuwa. Mahma kuwa gida zai saya mata tai zamanta kusa dasu. *_MOROCCO_* Wannan shine karon farko na zuwan Zinneerah dangin kakarsu AK, tako sami tarba ta mutunci ga mutanen har taita mamaki, yaranta kowa yana nuna musu so da ƙauna abin birgewa. Yaran Mahma kuwa kamar sun santa dama can, dan janta suka dingayi a jiki ita dasu little. Magana kuwa sai da turanci, waɗanda basaji sai larabci sai dai ake musu tafinta da Zinneerah dan ita dai ba iyawa taiba sai abinda ba'a rasaba na islamiyya, wanda bai wuce gaisuwa ba da kalmomi. Satinsu ɗaya cif suka wuce london cike da kewarsu, inda acanma suka sami tarba ga Mahma da Mammah. Kwanansu biyu da isowa Adilah da Huzaifa suka iso suma. Ai fa sai gida ya kacame da farin ciki bakin Mammah tamkar zai yage dan farin ciki. dan itama Adilah fama take da ciki harya fito abinsa. Sunsha hutu da soyayyarsu a london kafin su tattaro kuma su dawo gida dansu little sun koma school. Satinsu biyu da dawowa aka maida auren Mammah da Baffah. Zo kaga farin ciki wajen yaran gidan, dan koba komai AK ya cancanci su girmama mahaifiyarsa su kuma sota dan shima yana girmama nasu. Ba'a wani tsaya ja'inja ba Mammah ta tarkato kayanta ta dawo Nigeria gidan masoyinta bisa rakkiyar dangin mahaifinsu. Aiko sai ga baffah da mammah an ƙara shimfiɗa sabuwar soyayya, ita da abokan zamanta kuwa sai dai sambarka. Dan tana ƙoƙarin danne kishinta kamar yanda suma suke danne nasu kodan yara da nasihar da hajiya iya ke musu kullum babu gajiyawa. Dan babu abinda zatace da UBANGIJI sai godiya na sake haɗe mata kan family ɗinta da yayi, bayan gwagarmaya da jarabawar data sha a shekarun baya wajen ganin ta haɗesu waje guda hakan bai samuba sai da iyaka tazo. Mahma kuma AK ya saya mata gida anan kusa dasu, da yake mutumce maison jama'a saita tarkato ƴaƴan dangi daga kaita dansu tayata zama. ★★★ Daga haka rayuwa ta cigaba da turawa Zinneerah na cigaba dama AK naci akan dawowar Farah. Duk da yana ɓata mata rai haka take sake dawowa ta ƙara masa maganar. Sai gashi a wasa-wasa dai sai da Farah da Zakiyya suka cika shekaru biyu cif da maimartaba ya basu. Zuwa lokacin ƴan biyu babu inda basa zuwa da kafafunsu, yara sunyi ɓul dasu masha ALLAH ga wayo dan sun hau karatun little. Naci Zinneerah ta cigaba da masa akan dawowar Farah ɗin yana basar da ita har sai da ta ƙara wata uku akan shekara biyun mai martaba sannan yace mata zaije. Amma babu rana. Wannan maganar tasata tunkarar hajiya iya da batun da Baffah a karo na farko. Albarka suka dinga saka mata. Uncle Ahmad yace insha ALLAH da kansa zaije ya ɗakko Farah ɗin. ★__________★ Aiko kamar yanda Uncle Ahmad yay alƙawari bayan sati guda da wannan zance batare da sanin AK ba sai gashi tare da Farah. Lokacin suna a barandar gidan su duka da yammaci iskar la'asar na kaɗasu. Boss na zaune yana harkar business ɗinsa a lap-top duk da ma su Anam na hanashi, dan sai hawa masa jiki suke suna ƙirniya. Zinneerah na gefensa tana koyama Little homework. Duban Zinneerah yay yana nuna mata Anam data haye masa dokin wuya. “Mami kizo ki ɗauke kakarnan taki kona jehota ƙasa ta isheni ALLAH, ta hanani aiki”. Dariya Zinneerah tai saboda yanda yay maganar a marairaice tana kallon uban da ƴar. Tace, “Idan ka jeho Granny ƙasa aiko ka koma Morocco da ƙafa dan takwararta ba ɗaga maka ƙafa zatai ba”. Murmushi yay yana sauke Anam ɗin da faɗin, “Madam rikici ba, ai saita saukemin Nigeria a kaina wlhy. Inaga dai bara na haƙura da aikin nan kawai dan ba barina zasuyi ba, shi baffah ma neman rikitamin system ɗin yake”. Little daketa tunzura baki gaba ya gaji da homework ɗin yace, “Daddy na ɗakko ball muyi?”. “Kokuma kakan ball ɗin ba”. Zinneerah ta faɗa tana nuna masa littafin gabansa. sake tunzura bakin yay yana kallon AK kamar zai kuka. Yanda yay ɗin ya bama AK dariya. Shima sai ya duba zinneerah yana marairaicewa kamar yanda little yayi. “Mami a tausaya mana a barmu mu huta. Itafa bokon nan iyakarta duniya, kuma mu ba dangin mango park ba”. Ta buɗe baki zata bashi amsa motar Uncle Ahmad dake tare da Khalipha da Farah ta shigo gidan. Shi AK da farko ma ya zata ko Suhail ne babban ɗan Uncle Ahmad ɗin dan nan ɗin gidan zuwansa ne sosai tunda ya baro Turkey. Dan haka yayma Zinneerah nuni da hijjab ɗinta dake gefe dama ajiye. Sai da yaga Khalipha ya fito da Uncle Ahmad ɗin ya sashi miƙewa tsaye babu shiri. Yana ƙoƙarin nufarsu Farah ta fito a motar. Ta rame sosai ta canja tamkar ba itaba. A take fara'ar fuskar AK ta ɓace ɓat. Sai dai babu damar magana saboda Uncle Ahmad. Sannu da zuwa Zinneerah taketa musu fuskarta ɗauke da murmushi. Uncle Ahmad ya ɗauka little yana faɗin, “Uhm babana zoka samin albarka”. Shima Khalipha sai ya ɗauka Amaan yace, “Nima taho samin tawa albarkar babana tunda abin hakane”. Dariya aka sanya musamman da Anam taje jikin AK itama ta maƙale. Shi dai ko murmushi baiyiba. Ita dai Zinneerah nufar Farah dake kallonsu tamkar tana hawayema tayi tana mata sannu da zuwa cikin fara'a. Yanda ta amsa mata kamar a kunyace sai ta bata mamaki, ta kama hannunta sukabi bayan su AK ɗin da har sun shige ciki. Sashen AK suka nufa, sai da ta raka Farah sannan ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182