Chapter 108
Chapter 108
sai gabannin asuba ya tashi yana kiran “Mama ruwa, mama ruwa”. A hankali AK ya buɗe idanunsa, ya miƙa hannu ta bayansa ya kunna fitila dake a bedside drawer dan da alama basu da wuta. Zaune ya tashi da ƙyau yana riƙo little dake neman yin kuka yana kiran ruwa. “Oh oh sweetheart i'm sorry ina zuwa”. Ya faɗa da ɗagashi gaba ɗayansa ya maida jikinsa. Kafin ya ɗakko ruwan daya ajiye gefensu dan shima yakan tashi shan ruwan dare shiyyasa baya kwanciya babu shi a kusa. Sosai little yasha ruwan. Yana gamawa ya lafe a jikinsa ya koma barci. Shiru yay yana kallon fuskar yaron mai tsananin kama da tashi, wani lallausan murmushi da ajiyar zuciya suka kufce masa a lokaci ɗaya. Kwantar dashi yay a hankali yaja bargo ya rufa masa shi kuma ya sauka dan yasan bazai iya sake komawa barcinba kuma. Harya fita sallar asuba ya dawo little nata barcinsa, shima sake kwanciyar yayi dan barcin yake buƙata. Kusan takwas na safe ya farka dole saboda tsalle-tsallen da little ya farka yana masa a jiki, dole ya buɗe idanunsa da sukai nauyi irin na wanda ya tashi a barci. Kamo hanunsa yay ya zaunar a jikinsa yana murmushi tare da kai hannu ya shafi fuskarsa. “Little Handsome ka hanani barci bayan kai kasha naka”. Cikin rashin damuwa little yace, “Abba tea”. Dariya AK ya ƙyarƙyale da shi yana miƙewa zaune dashi a jikinsa. “Wato kai yaren abinda kakeso kawai kake ganewa ko? Inga bakin shan tea ɗin?”. Babu musu little ya ko wage masa baki alamar gashi. Dariya nanma ya sakeyi da sumbatar goshin yaron wani farin ciki na saukar masa. Huzaifa dake tsaye a ƙofar ɗaki yana kallonsu yay murmushi tare da jin daɗin ganin ɗan uwansa na walwala maiban mamaki, dan ba abu ƙarami bane a rayuwa ke saka AK ƙyalƙyala dariya. Baiyi magabana ya juya abinsa. Shiko AK daba ganinsa yayiba little ya ɗauka zuwa toilet, da kansa yay masa wanka, ya naɗo abinsa a towel ya kawo ɗaki ya ajiye a kan gado. Wayar Haneef ya kira yana tambayarsa sunzoma little ɗin da kaya ne?. Daga can Haneef ya amsa masa da eh bara ya kawo. “Okay” ya amsa yana yanke wayar, game ya sakama little a waya ya nufi toilet ɗin shima yin wankan. Shigarsa babu jimawa sai ga Haneef, sai da yayi sallama sau kusan uku, jin ba'a amsaba ya leƙo da kansa. Little kawai ya hango yana kokawa da waya, dan haka ya shigo yana dariya. “My Darling good morning ” ya faɗa yana kaiwa tsugunne gaban gadon. Little dayay busy abinsa ya ɗan ɗago ya dubesa ya sake maida kansa. Yanda yayi ɗin sai ya bama Haneef dariya, ya fisge wayar yana faɗin, “Haba my man ni zakama jama aji danka samu phone?”. Ɓata fuska little yay zaiyi kuka Haneef ya maida masa wayar yana dariya. Daga haka ya miƙe ya ɗakko man Yayansu daya hanga a kan mirror yazo ya yayema little towel ɗin da yake a ciki ya hau shafa masa. Sunayi ana kokawa dan little baison ajiye wayar hannunsa. Har dai aka gama. Yana saka masa kaya AK ya fito. Gaidashi Haneef yayi. Ya amsa shikam yana binsu da kallo, dan yanda suke kokawa wajen saka kayan kawai zai tabbatar maka akwai shaƙuwa a tsakaninsu sosai. Haneef na gama shirya little ya ɗaukesa suka fice danya bama Yayansu damar shiryawa. A hankali AK ya sauke numfashi, zama yay a bakin gadon yana ɗan kai hannu ya murza goshinsa, hakan yayi dai-dai da shigowar kira a wayarsa. Kamar zai share sai kuma ya ɗauka wayar dake a kife, duk da ganin Mammah da yayi ɓaro-ɓaro a jikin screen ɗin bai kawo komai a ransa ba ya ɗaga. Sama-sama ta amsa masa sallanarsa, gaisuwa kuwama bata amsaba ta shiga masa magana cikin faɗa. “Yanzu Abdul-Mutallab danka maidani banza harka iya ɗaukar ƙafa ka tafi Nigeria bakako sanar minba!!?”. Idanunsa yaɗan lumshe da raunan muryarsa gareta kodan daraja ta uwa da ALLAH ya bata, cikin girgiza kai kamar yana a gabanta yace, “Am so sorry Mammah, nima tafiyar ta dolece wlhy, ki gafarceni”. “Dole kace ta dolece tunda ubanka ya gama gayamin magana jiya, aiko yayi da ƴar halak da bazata raga masaba. Dan insha ALLAH yau zan baro london nima zuwa Nigeria ɗin, sai naga munafurcin da kuke son biznewa”. Babu shiri AK ya miƙe yana faɗin “Mammah Nigeria kuma?”. “Ƙwarai da gaske, ko karnazo ne ubana?!”. Bakinsa ya cije dakai hannu ya dafe kansa, zaiyi magana ta yanke wayar ƙitt Rasa abinyi AK yayi a ɗakin, ya shiga kai kawo kamar mai ɗawafi. Sam baiso Mammah tazo Nigeria a wannan gaɓar, dan yanda Baffah ya ɗauki zafi wlhy ba raga mata zaiyiba. Shiko baya buƙatar ganin suna shiga irin wannan rikicin dan ƙara nisantasu yakeyi. Wayar Mahma ya kira da sauri dan yasan itace kawai zata iya takama Mammah birki. Harta tsinke ba'a ɗagaba, dan haka ya sake kira. Jin an ɗauka ya sauke ajiyar zuciya. Sai dai jin muryar Adilah na faɗin, “Sweet bro surprise”. Ya sakashi maida hannunsa a goshinsa yana murzawa. Ƙoƙarin dai-daita muryarsa yayi yace, “Uhmyim Darling badai kina london ba?”. Ɓata fuska tayi daga can kamar tana gabansa. Cikin shagwaɓa tace, “Uhm ai dama nasan yanzu ka daina sona ALLAH, yau kwana biyu ina nemanka a waya saboda dawowana amma bana samunka, na dawo ɗazun nan, saina tarar wai kana 9ja, yanzu haka ina shirin tafiya can gidanka wajen Granny ne, ina jiran Khalipha yace zaizo mutafi idan ya fito school”. “Oh parrot har yanzu dai baki canjaba. Ina Mahma ne?”. Baki ta tura duk da kuwa bata kasance ƙaramar yarinyaba, dan tama girmi Khalipha da kusan shekara biyu. Cikin shagwaɓa tace, “Haka dai kakeson parrot ɗin nan taka. mahma gata can suna rikici da Mammah akan wai zatazo Nigeria ita da Farah. Wai mike faruwane na isketa sai faɗa faɗa, ni wlhy namaji dama ban dawo ba. Shiyyasa zan tafiyata gidanka dan banason faɗan nan na Mammah taita zagin mana Baffahn mu”. Hankalin AK ne ya kuma tashi, atake raunin da yake ɓoyema ƴar uwarsa ya bayyana. Idanunsa suka sake kaɗawa sukai jajur. “Adilah akwai matsalane, amma yanzu sanin tushenta bashine abinyiba. Inason kije ki sace min passport ɗinta dana Farah ɗin duka”. “Tab, wlhy Bro hakan dakamar wuya, dan inaga abinda Mahma tai niyyar yi kenan Mammah ɗin ta gani, yanzu hakama gata can harta fito da kayan tafiya shine Mammah ta kulle ƙofan ta canja security”. “Thanks GOD”. Ya faɗa yana furzar da zazzafar iska. Hakan da yayine ya sake tayarda hankalin Adilah, dan ta tabbatar Yayanta na cikin damuwa, tambaya ta shiga masa amma bai iya bata amsa ko gudaba, sai ma yanke wayar yayi daga ƙarshe ya zame ya kwanta a gadon yana mai dafe kansa da yakejin ya fara sara masa da ƙarfi. A cikin gida kuwa little nacan yanata hidimarsa a tsakanin su Baffah hankali kwance. Dan tare yay karin kumallo da Baffah da Mommy abinsa. Hakan harya dinga basu mamakin yanda ya saki jiki dasu sosai. Sai da suka kusa gamawa AK ya shigo falon. Gaidasu yayi sanan ya kai zaune kusa da Mommy. Ta shafa kansa cikin kulawa take faɗin, “Kana lafiya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182