Chapter 120
Chapter 120
ne masu kaisun, karan farko da zaije tushen Zinneerah. Anan ɗinma dai ansan da zuwansu, dan sai da safe baba yake sanarma Inna, amaryarsa kuwa tasani kusan kwana biyu, da itama akai aikin abincin baƙin a gidan Gwaggo Laritu harda Yaya Gajeje ma. Ƙarfe ɗaya da wasu mintuna motocin su Khalipha suka shiga cikin garin Danya. Gidan maigari suka fara isa dan can su Haneef suka sani, daga can aka saka yaro musu rakkiya dan babu wanda yako fito a motama a cikin matan. Cike gidan yake da ƴan uwa domin amsar lefe, dawowar su Gwaggo Laritu gidan kenan su Mommy suka iso, an musu tarba ta mutuntawa da girmamawa, inna dai shigowar waɗan nan ƴan gayun matama neman birkitata yayi. dan duk iya jarabarta sai gata tai muƙus sai kallo da idanu. Gidan baba yasha gyara aƴan kwanakin nan, dan ɗakuna ya sake zubawa sabbi aka kuma siminte tsakar gidan tsaf, ga amaryar baba akwai tsafta dan tunda tazo gidan ya ƙara ɗaukar saiti. Musamman yau ma datai masa gyara na musamman ita da Sa'a. Dan jiya akai taron sunan Karima duk da dai baimayi wani armashiba. Sai uwar rigima da aka kwasa tsakanin dangin Babawo dana Inna. Saboda Babawo har yau baizoba yakumaƙi cewa komai, ita kuma idan an tambayeta sai tace bata masa komaiba. A ƙarƙashin bishiyar gidan aka shimfiɗa musu tabarmi dansu sha iska, aka kawo musu lemuka da ruwan leda da su baba suka tanada domin su kawai. Ba ƙaramin daɗi su Mommy sukaji ba a yanda aka tarbesu da girmamawa da mutunci. Bayan anyi gaisuwa da tanbayar iyalan juna aka shigo da akwatunan da suka saka ƴan uwa fara callara guɗe-guɗen da suka nema jefa Inna a hauka. Dan duk yanda taso ta daure ta kasa sai gata ta shiga zage-zage. Cikin mamaki da ɗaukarta mahaukaciya su Momie ke kallonta, yayinda su Gwaggo Laritu da sukasan hali basubi takantaba, sai maida hankali a murna da farin cikin Zinni tayi goshi da sukai, suna kuma yaddama Inna habaici akaikaice. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya sake haukacewa da makwafta da yara ƴan kallo, dole aka maida su Mommy ɗaki dan suma su samu suyi salla. Su dai yanda mutan garin keta arerewa akan wannan lefe nasu sai abin ya ƙayatar dasu ainun, Adilah harda yin video dan ita kam wani ƙayatar da ita suke da sakata nishaɗi, sai washe baki take ranta fes. A waje ma dai yanda mata ke gudun shigowa gidan da yara sai abin ya dinga saka su Khalipha dariya, da birgesu. Dan suma suna zaune ne a ƙofar gidan a ƙarƙashin bishiya ni'imtacciyar iska na kaɗasu. Haka suka kasance a ƙauyen danya suna kallon yanda ake kai kawo akan ganin lefe. Sai da sukai sallar la'asar sukai haramar baro garin cike da alkairi da tukuyci, duk da sunƙi amsa Baba yace indai basu rainaba su amsa dan ALLAH. Jin furucinsa yasa dole suka amsa suna mai yaba ƙoƙarinsa da dattako. Daga haka akai musu rakkiya suka shiga motoci suka ɗauka hanyar tafiya kano akan sai kuma ranar juma'a sunzo ɗaukar amaryarsu da zata iso zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu itama. Koda suka taho a hanya labarin yanda al'amarin ya faru suketayi, dan sun baro Inna ta birkicema jama'a kamar sabuwar kamu a hauka. Duk da dai Yaya Gajeje da Karima na ƙoƙarin tausarta. Gida su mmn halima suka wuce, suma suka wuce nasu gidan inda suka kaima hajiya iya labarin farin ciki. AK na zaune a dining yana cin abinci shi da little yana jinsu, sai dai uffan bai tofaba bayan sannu da zuwa da yay musu. Adilah ce tazo inda yake bakinta a washe ta sumbaci little da tunda tazo take maƙalle da yaron, cikin sabawa daya farayi da ita ta bashi nata kumatun shima yay mata kiss suna dariya. AK dake kallonsu yay ɗan murmushi kawai batare da yace komaiba. Zama tayi tana fara bashi labari, tare da nuna masa video ɗin da tayo a waya. Shi kansa abin ya burgesa da bashi dariya. amma sai baiyiba yaɗan murmusa kawai yana ajiye wayar da dubanta cike da kulawa. “Yaushe zakije ki gaida su Mammah?”. A take fara'ar fuskarta ya ɓace, ta shagwaɓe fuska idanunta na cika da ƙwalla. “Bro ka barni Please basai najeba, kuma bama kace tana katsina ba tunda mukazo da Mahma?”. “Kema ai katsinan zakije, gobe idan ALLAH ya kaimu zanje sai muje tare na baroki can ki biyo Mahma ranar biki”. Hawayen da suka cika mata ido suka gangaro, sai kawai ta miƙe tabar dining ɗin ta shige ɗakin Hajiya iya. Binta yay da kallo kawai yana dariya a ransa. Dama tsokanarta kawai yakeyi, shima yaso zuwan amma Mahma ta hana, tace ya bari ai zata ɗakko su Mammah suzo wajen bikin dan dole suma dangin mahaifiyarsa su kasance ai tunda aure abin farin cikine ga kowacce zuri'a. Yanzu kuma Mammah ɗin kanta a zafi yake zuwansa bazai haifar da ɗa mai ido ba. _________________________________ A washe garin da aka kai lefe hajiya iya ta samu Zinneerah a gidan Hajiya Falmata ita da Adilah. Yanda Zinneerah ta ƙara canjawa a cikin sati ɗaya ya saka hajiya iya jin daɗi matuƙa, hakama Adilah da sau ɗaya kawai suka taɓa ganin juna a london rungume tayi dan tunda ta ga yarinyar dama ta shiga mata rai, da Hajiya iya ta bata labarin komai kuma shima AK ya bata sai ta ƙarajin tausayi da ƙaunar Zinneerah, tare da ƙara taya ɗan uwanta murnar samun mata dai-dai da shi da zata kawo ma rayuwarsa farin ciki tunda Farah taƙi kwantar da hankalinta ta daina biyema Mammah ta riƙe mijinta kamar yanda ta fara a farkon aurensu. Daɗin yanda Zinneerah tai ƙyau mai ɗaukar hankali yasa hajiya iya harda ƙarama hajiya falmata kuɗi tana jera mata tagwayen godiya. Cike dajin daɗi itama hajiya falmata tace, “Ai hajiya namaso ace daga gidan nan sai gidan mijinta za'a kaita, amma hakanma babu laifi tare dani zata tafi can ƙauyen muɗan ƙarasa abubuwan da suka rage”. Hajiya iya taji daɗin wannan karamci na hajiya falmata, dan duk da yanda Zinneerah ta canja kogi bayaƙin ƙari. Da wannan damar hajiya iya ta zauna ta sakema Zinneerah nasiha, a yau kuma ta sanar mata an ɗaura mata aure amma bata sanar mata da waye ba. Share-share sai ga Zinni na kuka da hawaye tana kallon haijiya tamkar wata sokuwa. Cike da kulawa hajiya iya ta kamo hannunta cikin nata da sigar lallashi tace, “Nasan bamu ƙyauta mikiba Inno, amma insha ALLAH wannan shine gatan da zamuyi miki na har abada. Ki saka a ranki wannan itace taki nasarar cin jarabawar, insha ALLAH nasan bazakiyi kuka ba a wajen wanda muka baki, inamiki fatan alkairi da tarin farin ciki mai ɗorewa a rayuwarki da rayuwar aurenki”. Kasa magana Zinneerah tayi sai kuka, ta faɗa jikin hajiya iya tana abinta. Itace kuma aka ɗaurama aure bayan taci alwashin bazata taɓa aureba. Gaskiya da anyi shawara da ita da haka bata kasanceba, batason tai aure a gorantama little, batason tai aure a aibantata akan ta taɓa haihuwa a waje. Bata da burin daya wuce yin karatu mai zurfi a rayuwarta, sai dai kuma duk waɗanan burikan nata da farga basu kai daraja da kimar hajiya iya ba a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182