Chapter 175
Chapter 175
suke yaba kamshin a jikinta da gidanta. Hakan yasa tasa Hajiya Falmata ta haɗa musu na musamman akai musu packaging nashi. Sai gata harda ƙwalla da zasu wuce. Bama ita ba hatta su Yaya Gajeje sunji babu daɗi. Inna ma da take ɗan magana yanzu kuma takan ɗan motsa jikinta tafiyace dai batayi sai da ta nuna alhinin tafiyar tasu, dan kullum sai sun shiga sun gaidata sau uku a rana babu fashi. Duk yanda Zinneerah ke share hawaye AK na kallonta ta mirror. Yay ɗan murmushi yana cizar lip ɗinsa dan yau kam yasan ango yake tunda Mahma ta ɗaure mata ƙugu sai da tai arba'in duk da ba haihuwa tayi da kanta ba. Baisan Mahma ta masa wayo bane tanata gyare masa Zinneerah ɗin a ɓoye. Ga gyaran Hajiya Falmata datake ɗorata a layi, hakama Hajiya Iya kullum cikin faɗa mata dabaru takeyi. Ita kanta tasan idan taje hannun boss din nata sai ta yabama aya zaƙinta. Shiyyasa yau duk take a tsure. Kasancewar da little ya tafi suna wucewa mai ƙunshin da zatai mata tana isowa. Ƙunshi akai mata na gani na faɗa na jan lalle da baƙi, Yaya Karima ta yarfa mata kitso kananu da ya fiddo mata ƙyawunta sosai musamman yanzu data yi wani bulɓul da ita tamkar ba itace tasha fama da rama lokacin cikin ƴan biyu ba. Kasancewar basu zauna wasaba kamar wasa kafin la'asar suka kammala komai tai fes da ita. Dama tunda ta fara zaman jegon nan take dilke jikinta da kayan gyaran fata na musamman da Hajiya Falmata ta haɗa mata ga kuma na Mahma. A gurguje ta shiga gyaran sashe. AK duk da bawani ƙura yayi ba. Sai da ta tsaftace komai yay mata yanda takeso ta baje kalolin ƙamshinta masu rikitashi. Sanda ta dawo sashenta ma su Mama A'i sun gyare ko ina sai ƙamshi yake. Waya tai zamanyi da AK ɗin taji kosun taho. amma yace mata yana dai shirin tahowar. Taji daɗin haka dan ta samu damar shiga kitchen kenan ta haɗa abinci da kanta. Dan tunda ta fara zaman jegon nan kullum cikin ƙorafi yake akan abinci, idan kaji baiyi maganaba Mahma ce tai girki da kanta saboda shi. Lafiyayyen abinci ta shirya masa da tasan zai gamsar dashi. Tare da haɗaɗen shayin barnawa daga Hajiya Falmata da kalolin kayan sha na zoɓo da kunun aya. Suna kammalawa dan da taimakon Mama A'i tayi ta bar mata idawa bayan ta ɗiba na AK takai sashensa. Wanka takeson shiga Amaan ya wani saka kuka shi a dole yunwa yakeji. Ɗaukarsa tai tana dungurinsa da kiransa acici like Daddynsa. Tana gama bashi a tsaitsaye itama Anam ta saka tata rigimar. Kanta ta dafe da amsarta Yaya Gajeje na dariya. “Wai yaran nan mi kuke son maidani ne halan? Ku gama naku shima yazo ya isheni da tasa rigimar”. “Ai daidai kenan”. Cewar Yaya Gajeje tana dariya. Murmushin jin kunya Zinneerah tayi da ajiye Anam din ta shige cikin dan watsa ruwa...........✍ *_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _______________________ *Page 68* ..........Sai da Zinneerah ta fara gabatar da sallar magrib bayan fitowarta wanka sannan ta zauna ta tsara kwalliya ƴar gaske, tare da baje lungu da saƙo na jikinta da ƙamshin mayun turarurrukan ta sabbin haɗi daga Hajiya Falmata. Ta ɗakko less da yaji ɗinki mai ƙyau da tsari ta saka tare da kashe kan ɗauri. Awarwaraye da sarƙa ta zuba kai kace wani biki zata. Ta sake ɗorawa da wasu turarurrukan sannan tai zaman sallar isha'i. ALLAH ya sota ƴan biyu suna goye a bayan Yaya Gajeje da Mama A'i. Sauri-sauri ta kammala ganin har isha'i su AK basu shigoba. Koda ta fito su Yaya Gajeje wani ihun dariya suka ɗauka da yaba wannan wanka nata. Kunya tasata jan mayafi ya rufe fuskarta. Mama A'i da yake itama a ce, babu yawan magana sai lalata tace, “A'a wannan gayun bai kamata ki kaisa turaka ke kaɗai ba. Bara na ɗakkoma su Alhaji ƙarami kaya a canja musu suma dasu za'a”. “Wannan zance nakan hanaya Mma A'i”. Yaya Karima ta faɗa tana dariya. Zinneerah ta tura baki kaɗan tana faɗin, “Gaskiya nai dai a'a, salon su batamin gayu”. “Iyee, lallai Zinni binni ta buɗe miki ido da baki, a gabana babu kunya”. Cewar Yaya gajeje tana riƙe haɓa. Dariya Zinneerah ta shiga kwasa. Ta faɗa ɗaki tanayi da faɗin, “Yi haƙuri Yaya gajeje na tuba”. Suma dai dariyar suke tayata harta ɗakko kayan da za'a canjama ƴan biyu. Su Mama A'i suka shiryasu tsaf sannan Zinneerah ta kwashesu. Dan Yaya Gajeje korata tai wai ta tafi can yazo ya sameta zaifi jin dadi. Su Yaya Gajeje tsoffin masoyane da sukasan takan maza da muhimmancin irin wannan ranar. Aiko shawararsu Zinneerah ta bi. Dan dama itama akwai nata shirin a ƙasa. AK bai shigo gidan ba sai wajen tara da rabi na dare. A gajiye yake matuƙa. Dan haka kai tsaye ya nufi sashem Zinneerah ɗauke da little dayay barci. A falon farko ya samesu dan sunfi zama nan, kai shi baima taɓa samunsu a falon ciki ba dan daga shi sai Zinneerah ɗin ke shigarsa da bedroom dinta na ciki, saiko little. Mama A'i ta mike tana amsar little ɗin da masa sannu da zuwa. Suma su Yaya Gajeje sannun suke masa. Cike da mutuntawa yake amsa su yana baza idon ganin ta inda Zinneerah zata ɓullo da twins nashi. Ganin dai babu alamarta ya sashi leƙa Inna sannan ya fice. Gulmarsa su Yaya Karima suka shigayi suna dariya. Dan yanda yaketa kalle-kalle sunsan matarsa yake son gani, gashi su kuma sun yi gum bama su nuna sun fahimcesaba. Shiko harya ɗan shaƙa dan ya zata abinda ya faru tsakaninsu ɗazun da safe ne ya sata fushi. Sai da ya shigo sashensa ya shaki wani mayataccen ƙamshi daya nema karar masa da man kai lokaci ɗaya sannan ya sauke ajiyar zuciya. Taku yake tamkar mara laka a jiki yana bin falon data sakama hasken wuta kaɗan da kallo. Bukatar fara wanka ta sashi nufar bedroom ɗinsa ransa fal waswasin ina ta shiga. A bedroom ɗinma ƙamshin da yafi na falo ɗaga masa hankali ya shaƙa. Kasancewar wutar ɗakin a kashe dindim ta sashi fara lalauben makunnar fitilar. Ɗan zabura baya yayi lokacin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182