Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 110

Chapter 110

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

Dan haka baima son zama ya yini a gidan sam. A hankali ya kwantar da little dake barcinsa. Duk da ya ɓata jikinsa sosai a can bai tadashiba, sai dai shi ya cire nasa kayan ya nufi bayi a gurguje saboda lokacin sallar magrib yayi. Wankan ma a gaggauce ya yisa ya fito, jallabiya kawai ya zura ya ɗan saka turare ya fito yana addu'ar ALLAH yasa kar little ya farka harya dawo. Bayan an idar da salla bai zaunaba ya nufo gida saboda tunanin barin little da yayi shi kaɗai. Koda ya leƙo yaga barcinsa yake har yanzu sai ya koma massallacin. Sai da akai sallar isha'i suka taho shi da ƴan uwansa da Baffah gwanin sha'awa. A gajiye yake matuƙa, dan haka ya wuce sashen hajiya iya kai tsaye yana cema Mas'ood yasa cikinsu Safiyya wani ya kawo masa tea da abinci kaɗan saboda little karya farka ya nema. Da to Mas'ood ya amsa masa cikin girmamawa. Harya nufi hanyar sashen hajiya iya baffah dake ƙoƙarin shigewa nasa sashe shima ya juyi ya dubi AK ɗin. “Karfa suga mun musu ƙarfa-ƙarfa akan yaron nan, daga zuwa ya gaida Bilkisu”. Juyiwa AK yay zuciyarsa na harbawa, harga ALLAH baya fatan abinda zaisa Baffah yace ya sake rabuwa da little ɗin a yanzu, danshi yanzu haka yana shiryama zuciyarsa tafiya da yaron nema london. Amma yanzu sai ya ɗan murmusa, murya a sanyaye yace, “Baffah zai koma ai sonake saina tashi tafiya”. “Sai da safe”. Baffah ya faɗa yana shigewarsa. Shima cigaba yay da tafiya zuciyarsa na masa rauni akan iya sake rabuwa da gudan jinin nasa gaskiya. Washe gari da safe bayan idar da sallar asuba koda suka dawo sake kwanciya yayi, dan cikin dare Little ya farka da kuka, sai da yay masa wanka ya bashi abinci suka sami salama. Shiyyasa yau ya tashi kansa na masa ciwo. To ɗan barcin daya samu ya sake komawane kuma yana tsaka ya ringajin hayaniya na tashi sama-sama a cikin sashen nasu. Duk yanda yaso daurewa karya tashi hakan ya gagara. Dole ya miƙe da ƙyar yana jan tsaki. Mamaki ya kamashi ganin babu little a ɗakin, tashi yay ya zira doguwar riga bayan ya shiga toilet ya fito, yasa Slippers ya fita. Ganin babu little a ɗan corridor ɗin wajen nanma ya fita da sauri, abinda ya gani ya sakashi tsayawa cak. Ashe a falon hajiya iya ake hayaniyar shiyyasa yake jinta sosai. Ba kuma kowa keyiba sai Mammahn sa, Farah na gefenta tana kuka kamar zata shiɗe. Yabi Baffah dake ɗauke da little da kallo, daga shi har Mommy suna zaune kawai sun zubama Mammah idanu tana ta zabga musu azabar masifa akan abinda shi yama kasa fahimta kai tsaye. A matan gidan Momie ce kawai, dan ita kaɗai Baffah ya bama damar zuwa lokacin da Saifudden yazo ya sanar masa da zuwan Farah da Mammah duk da sau ɗaya ya taɓa ganinta kuma suna yara sannan, amma tsananin kamarta da Yayansu yasa yaji a ransa lallai itace Mammah, hakama yaran babu ko ɗaya a waje sai Huzaifa kawai. Ji AK yayi tamkar ya fasa kuka dan takaici, dan har cikin ransa yaji haushin wannan zuwa da sukai. A hankali ya fara takowa zuwa tsakkiyar falon cikin izzar da fushi ya haddasa masa, fuskarnan tai kicin-kicin kamar zata fashe dan ɓacin rai. Wani shegen tsawa data saka little fashewa da kuka yana ƙanƙame Baffah ya dakama Farah dake ƙoƙarin fara magana dan daga ita har Mammah basuga zuwansa wajenba. Ba Farah ba har Mammah sai da tai ɓam da bakinta ta juyo tana tana kallonsa ranta a matuƙar ɓace. Yi yay kamar baiga Mammah ba ya fara saukema Farah duk fushin nasa. “Da izinin ubanwa kikazo Nigeria? Wai Farah kin maidani ɗan iskane da duk abinda ranki ya raya miki kikeyinsa komi?. Ki maida hankalinki fa.......” A fusace Mammah ta katsesa da cewar, “Ubanka yace tazo, taƙi ta maida hankalin nata kuma, yanzu nan Abdul-Mutallab ko kunyar ALLAH bakaji a gabana kake cimata mutunci?”. “Mammah!” ya faɗa ransa a ɓace, danya fahimci idan har ba nuna mata ɓacin ran nasa yayiba itama to zata cigaba da bauɗar masa da Farah da banzar aƙidarta. Cikin rufewar ido yace, “Please Mammah ba maganar wasa nakeba, wane kalar rashin mutuncine sai dai ta ɗauka ƙafa daga wata ƙasa ta taho bada izinina ba, kodan taga wancan karon na mata shirune? To wlhy ni bazan ɗauka wannan iskancin ba, na bata nanda awanni goma ta koma inda ta fito, inba hakaba wlhy saina tabbatar mata da ainahina na Abdul-Mutallab Kabeer Abdul-Mutallab Shira”. Daga haka ya juya ya koma ɗakinsa. Wani ɗan murmushi Baffah yayi na manya ganin yanda Mammah tabi AK da kallo baki buɗe kamar sokuwa. Ƙara rungumesa little yayi da sumbatar goshinsa, shiko yaro ya ƙara lafe masa a jiki saboda tsorata da bala'in daddynsa. Juyowa Mammah tayi tana kallon Baffah cike da tashin hankali. Idanu ya ɗan waro mata alamar minene? murmushi ɗauke a fuskarsa har yanzu. Ƙara ƙufula tai da salon nasa, dan babu abinda ta gani sai Kabeer ɗinta masoyinta na da, muryarta har rawa take wajen faɗin, “Kabeer haka ka maidamin yaro?”. “Dama haka kika haifi abinki”. Baffah ya bata amsa kansa tsaye yana sake sumbatar goshin little. Sai kuma ya kalleta yana ƴar dariya, “Hindatu ko iya haka muka tsaya kin sami amsarki akan Adnan, dan kinji dai abinda yace, sunansa Abdul-Mutallab Kabeer Abdul-Mutallab Shira. Ba Abdul-Mutallab Hindatu Umar Kaita ba. Ballantana yanzu muka fara wasan ni da ke wlhy, dan sai na tabbatar miki ke kaɗai kikazo gidan nan badasu ba”. “Kabeer Shira!”. Ta faɗa a tsawace. Shima Baffah a fusacen yace, “Yes! I am. Hindatu Kaita!”. Ganin yanda Baffah da Mammah sukai ɗin ya tayarma Mommy da Momie hankali, shi kansa Huzaifa ƙarjinsa sai bugawa yake dan tamkar AK yake bayason hayaniya, barshi dai da shegen surutu shima yafiyi ga wanda ya sani sosai. Farah kuwa ai sake tsurewa tayi dan bata taɓa tunanin haka Baffah yakeba. Kallon mutum mai sauƙin kan tsiya take masa. “Dan ALLAH kuyi haƙuri ni banga abin tashin hankali ananba Yaya”. Mommy ta faɗa hankalinta tashe tana dawowa kusa da Baffah. A fusace Mammah ta miƙe tare da kama hannun Farah da duk jikinta ke ɓari. Ta duba Baffah da manyan idanunta da har ƙwalla suke tarawa dan bala'i. “Banzo Nigeria da niyar yin fitina da kai ba Kabeer, amma tunda har kace ka shirya muje zuwa. Ina mai tabbatar maka bazan bar ƙasar nanba sai da yarona, sai kuma nasan uwar data haifa wannan ɗan da shi. In ko har aure ka ɗaura masa da ita aka samar da shi sai ya saketa, na haɗa da yaron kuma na wuce, dan yazama nawa shima”. Wata ƴar dariya ce ta suɓucema Baffah babu zato, ya shafa kan Little yanayin kayarsa hankali kwance. Kafin ya ɗago yana nuna mata little. “Wannan shine tunani mafi gurɓata da kika taɓayi a rayuwarki Hindatu, kinsanfa ance abin cikin ƙwan yafi ƙwan daɗi. Dan haka ki sani wannan da kike gani zuciyata ne da duk ma wanda yake rayuwa a gidan nan. Kinsan kuwa raba zuciya da gangar jiki abune mai wahala ga ɓarawo. Amma tunda kema kin shirya wasan muzuba, ɗan halak ka

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182