Chapter 16
Chapter 16
matuƙa. Ita Inna tsoronta ALLAH tsoronta a gano gaskiyar da sa hannunta Zinneerah ta tafi Katsina. Saukinta ma Hajji Lanti bata dawo garinba ai tun tafiyar da tai dasu Zinneerah ɗin. To amma tasan akaje gaban hakimi ai ca za'ai sai wajen ƴan doka (Police) da ga haka kuma sai wajen alƙali. Lallai tsugunne bata ƙare ba kenan, ba burinta kenanba, babban burinta kawai Zinneerah tabar mata garin baki ɗaya dan bata ƙaunar ganinta a cikinsu kamar yanda ta tsani mahaifiyarta sanda tana tare da su. Sanin halin inna yasa Gwaggo Laritu tafiya da Zinneerah gidanta, bayan ta saka Sa'a ta tattaro mata duk kayan Zinneerah dake a can gidansu dan dolene ta dawo zama a gidajen ɗaya daga cikinsu har ALLAH ya sauketa lafiya. Tunda suka shigo gidan sam hankalin Zinneerah baya a jikinta. A hankali wani irin tsanar garin Danya da komai nasa ke shiga jikinta. Koda Sa'a ta kawo mata kayanta tana zaune can rakuɓe kanta cikin ƙafafu, ba kuka takeba ba kuma tunani ba. baƙon al'amarin dake shiga cikin jikinta ne kawai ke ratsata. Ta ɗago ta kalli Sa'a data dafa ta, ganin yanda Sa'a ke hawaye ya sata sakin wani murmushi maiban mamaki, batare da tace komaiba ta maida kanta yanda yake. Hankalin Sa'a ne ya ƙara tashi, dan a duk sanda taga irin wannan murmushin a fuskar Zinneerah to takai ƙololuwa a shiga tashin hankalin rayuwa kenan. Dan duk lokacin da takurawa da matsawar Inna yaymata yawa bata kuka. Ko nuna tausayinta sukai kuma sai dai tai musu wannan murmushin bazata taɓa ta tanka ba. Zuciyar Gwaggo Laritu a kusa take ainun da baƙin cikin halin da suke ganin Zinneerahn ta jefa kanta. Da kuma haushin Inna dana Baba da ya koma tamkar mara amfani agaresu, yanzu haka a kaf ruguntsumin nan da akeyi yaƙi cewa ƙala. Wanan takaicin da sukai mata yawane ya sata shigewa ɗaki tabar Zinneerah waje zaune batare da tace taje ta kwanta ba. Sauƙinta ma itama su kaɗaine a gidan sai matan ƴaƴanta biyu, suma kuma an katangema kowa sashensa babu mai ganin wani. Abinka da ƙauye ahankali garin ya fara ɗaukar shiru. Har takai Zinneerah dake zaune a ƙofar ɗakin Gwaggo Laritu barci ɓarawo ya saceta har takai ga zamewa ƙasa ta kwanta akan sumintin wajen tai filo da jikkar kayanta da Sa'a ta kawo da yake ba wata babba bace, dan kayan nata basu wuce a ƙirga ba. Barci ne sosai mai nauyi yay gaba da ita, yayinda itama acan Gwaggo Laritu datai tunanin idan Zinneerah ta gaji da zaman wajen zata shigo ɗaki ta kwanta barcin yay gaba da ita dan gajiya. Tamkar wadda akace ta tashi Zinneerah ta miƙe zumbur, babu wani tunani ta ɗauki jikkar kayanta ta nufi hanyar ƙofar gidan nasu Gwaggo Laritu. A hankali ta zare sakatar murfin gidan ta fice kamar tana tsoron wani ya jita koya ganta. Kallon gabas da yamma kudu da arewa tayi, garin tsit babu alamar akwai wani rai mai numfashi, ga wata yayi nisa babu wani hasken kirki, ga sanyi kasancewar lokacinsane sai dai farko-farko dan baiyi ƙarfi ba. Ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya ta fara tafiya babu alamar tsoro ko fargabar jin garin shiru tattare da ita sam. A cikin daren nan Zinneerah ta nausa kanta cikin daji batare da alamun akwai hankali a jikintaba, dan yanda take matsoraciya ko fitsari ya kamata da dare sai ta tada Yaya Sa'a ta rakata. Amma yau sai gata a hanyar daji cikin tsakkiyar dare babu ko gezau.............✍ Hasbinallahu wani'imal wakil. Ya rabbu ka iya mana da abinda yafi ƙarfinmu, harma da wanda mukafi ƙarfinsa.😭🙏🏻 *_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇 0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 https://youtu.be/NgqdCTVKOF8 Channel name Abdul-rahmaan. He's a very young boy who's passionate about becoming one among the huffaz, he loves reciting the Holy Qur'an even at his younger age. He has memorized so many surahs within juz ammah. please help him grow his channel fisabilillah and also pray for him to be come a Hafiz in future in sha Allah. Jazakumullah khair ________________________ *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 7* ...........Tafiya take batare da tasan ina take dosaba. Gashi babu alamar gajiyawa tattare da ita, duk da mai kallo a kallo ɗaya zai iya fahimtar lallai tana tare da gajiyar, amma ita kasancewar bata cikin hayyacinta bata saniba. Babban burinta kawai tai nesa da garin Danya baki ɗayansa. Bata damu da yunwa da ƙishirwar dake damunta ba, balle ta tuna bayan ita akwai wata halitta a jikinta dake buƙata idan ita bata buƙata. Kusan dai-dai ketowar alfijir ta iso bakin titin da batasan kona wane gari bane. Batai kuma tunanin son ta sani ɗinba ta zube a ƙofar wani shago ta kwanta cike da gushewar hankali dana tunani. Wani irin nannauyan barcine ya ƙwasheta kuwa, kafin wani dogon lokaci ta fara sauke numfashi...... ★★★★ Tsabar gajiyar da suka kwasone a yinin yau ya saka Gwaggo Laritu barci mai nauyi sosai, har takai da sai da babban ɗanta ya leƙo sashen domin tada ita da asuba. Dan da kullum itace mai tashinsu, amma sai gashi yau sun rigata su. Rashin jin motsinta kuma ya tabbatar masa da makara tayi kenan. Tashi tai da ƙyar tana mamakin barcin da tai haka mai nauyi. ga ƙofartata buɗe alamar Zinneerah bata rufe musu ba. Kallon saman gado tayi inda ta bar mata ta kwanta dan ita dama bata iya kwanciya a gado sai ƙasa. Ganin babu kowa a gadon tai tunanin ko Zinneerah bayi ta shiga ita ta tashi ne. Bata damuba ta fito gabatar da alwala. Saboda tunanin Zinneerah na bayin ya sata zuwa can wajen dabbobinsu tayo fitsari tazo tai alwala kar makarar tai yawa. Hankalin Gwaggo Laritu bai sake tashi ba sai da taga harta idar da salla gari yay ɗan shaaaa babu motsin Zinneerah. Ajiye carbin da take ja tayi ta fito tsakar gidan. Ganin babu alamarta ya sata nufar ƙofar bayi tai gyaran murya. Shiru. ta sakeyi, nanma shiru. Sai kawai ta danna kai. Gabanta ya faɗi ganin babu alamar anyi amfani da bayin ma. A rikice ta fito, hakan yay dai-dai da dawowar Awwal babban ɗanta daga masallaci, shi Safiyanu yana Lagos neman kuɗi. “Mama lafiya kuwa? Mi kike nema?.” A rikice tace, “Zinneerah wannan yaron (bata faɗar sunansa saboda ɗan fari). Ban gantaba”. Da mamaki shima yace,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182